Alaka Tsakanin Sufanci Da Shi’anci!


Bismillahirrahmanirraheem…
Wai meyasa ‘yan dariku suka fi alaka da ‘yan shi’ah? Hakika A aqeedance shi’ah da darika akwai alaka tsakaaninsu.. Toh amma bari muyi dan wata tsokaci, saboda ‘yan’uwa wanda guguwar bid’ah ta debesu su fahimta… A kullum ‘yan dariku sunfi nuna zafinsu akan qiyayyah ga ahlussunnah saboda sunace ahlussunnah suna zagin waliyyansu, ainihin abinda ya janyo gaba mai tsanani kenan tsakanin ahlussunnah da ‘yan darikah. Sannan suna sake fakewa da cewa ahlussunnah suna zagin iyayen annabi, sannan kuma suna rage wa annabi daraja. Toh amma kuma abin mamaki yanda yasa muka gano ashe duk karya sukeyi, su duk babatunsu bawai don ahlussunnah suna rage wa annabi darajah bane, da kuma suna ce iyayen annabi suna wuta.. Shine shigowar mabiya addinin shi’ah.. an tuhume ahlussunnah da zagin waliyyai irinsu shehu tidjani, da su nyass!!!! Aka kashe wassu daga cikin mabiya sunnah saboda wannan abu,. Toh amma shigowar mabiya addinin shi’ah sai suka kafirta waliyyai na ainihi masu register a qur’ani da hadisi, irinsu abubakar da umar da uthman. Da dai sauransu. Suka kuma sake kafirta iyayen annabi(s.a.w)… Toh abin mamaki duk da haka suka samu karbuwa a gurin ‘yan darika. Saboda basu zagin waliyyan boge irinsu tidjani, da nyass… Kaga anan ya bayyana a hakikanin gaskiya ‘yan darika ba suna fada da ahlussunah ne saboda annabi da iyalansa ba. A’a suna fada ne dun ahlussunnah sun taba waliyyan bogi irinsu nyass da tidjani… Domin inda suna fada da ahlussunnah saboda iyayen annabi da sunyi fada da ‘yan addinin shi’ah, saboda ‘yan addinin shi’ah suna da rubutacciyah acikin littafinsu cewa iyayen annabi suna wuta.. Ku duba cikin littafin ‘Mulla muhammad baqir’ wanda akafi sani da allama majlisi.. Littafi mai suna ‘Biharul-anwaar’ wanda wannan littafi tana daga cikin manyan littafin mabiya addinin shi’ah… Kaman yanda in akayi maganar littafin musulmai za’a kawo sahih na bukhari da muslim.
Acikin wanna littafi sukace annabi yace:
“DA ZAN NEMA MUSU GAFARA
DA ABU DALIB ZAN NEMARWA,
SABO DA YAYI MIN ABIN DA
BASU YI MINI BA. TO AMMA
ABDULLAHI DA AMINA DA ABU
DALIB SUNA WANI KWAZAZZABO, DAGA
CIKIN.KWAZAZZABUN JAHANNAMA” Toh kunji fa… Ina ‘yan darika masu babatu cewa ahlussunnah suna zagin iyayen annabi? A wani littafin ahlussunnah ne kukaga ya zagi iyayen annabi? Wato a hakikanin gaskiya an ribaci jahilcin mabiya ne aka cusa musu irin wannan aqeedar. Domin da yawa zakaji mabiya suna ce ahlussunnah suna zagin iyayen annabi, amma inka tambayesu a’ina suka gani bazasu iya bada bayaani ba… Wannan zargine wanda bata da tushe… Saboda haka mukeso mabiya a zurfafa bincike domin kada ku kama gaaba da wasu gabar da kuma baku da dalilin yinta…. Sannan shin kunyarda da ‘yan shi’ah, duk da suna zagin sahabbai? Amma kunki ‘yan sunnah saboda suna zagin nyass da tijjani? Toh anan su tijjani da nyass sunfi sahabbai ne? Haba ‘yan darika ku kula kuyi nazari kada a cusaku cikin shirme da rudu… Allah yasa mudace, Allah ka nuna mana gaskiya ka bamu daman binta, ka nuna mana karya ka bamu daman kauce mata… Yaa Allah ka shiryar damu tafarki madaidaiciya. Wa’innan ‘yan’uwa namu ka shiryar dasu da mu baki daya… Wassalaam…

Advertisements

15 thoughts on “Alaka Tsakanin Sufanci Da Shi’anci!

 1. Mai gara za ta yi wa dutse…?

  A kullum sai dai kaska ta mutu da haushin kifi!

  Shin kuna tsammanin haushin kare zai razana mu ne?

  Saboda haka, WAHABIYAWA ku kara kaimi wajen bude wagegen bakinku ku yi ta kwararo haushin da ku ka saba yi!

  SUFANCI 4 LIFE!!!

 2. ameen mallam, Allah ka hada mu a kan kitab wa sunnah baki daya da dariku da shi’a ka ganar da su sunnan manzonka na tsira (s.a.w) mu kuma wayanda muka amsa sunnah ka hada kan mu kada mu sake rabuwa ha abada……

 3. BABU MAKIYYAN GIDAN MAXAN ALLAH S’W KAMAR YAN SHI’A SUWA SUKA KASHI JIKOKIN MAXAN ALLAH DUK MAI JADA HALA YANE MAN AKAN WANNAN NUM DON KARIN BAYANE 08037710391

 4. HABA DANSHIAH ADUWULLAHI MAI KIRAN KANSA AMINULLAH KO DA KAKE DAAWAR DARIKA, MUN SAN KAI DANSHIAH NE DAGA KALAMANKA. DA FARKO MUNA BIYARKA BASHIN KA FADI INDA KA CIRATO KAZAFIN DA KA JINGINA GA SHEHUL ISLAM. IN KUMA HAR DANTIJJANIYYAR NE KAI DA GASKE MU BABU ABIN DA ZAMU CE MAKA DON TA BAYYANA GA DUK MAI HANKALI CEWA WALIYYAI KUKE BAUTA KAMA YADDA YAKE RUBUCE CIKIN LITTAFANSU IRINSU YAQUTATUL FARIDA DA JAWAHIRUL MAANI DA KUMA WAKOKIN BAYA BAYANNAN INDA HAR SUN KAI NYASS GA CIKKAKIYAR ULUHIYYAH. WANNA WAKOKIN NA NAN A HANNUN MUTANE ASIRI YA TONU. ALLAH YA KIYASHE MU.

 5. Hhhh yaro man kaza! Ko dan izalah ya yarda da waliyai kuwa? Ko ya yarda da iyayen annabi ba kafirai bane domin dama makiyi annabi damuwarsa akoda yaushe shine yagwagwayi martabar ma’aki shiyasa harkoda yaushe yan izalah basujin kunyar maimaita wannan maganar domin su agunsu annabi mutumne kamar kowa wal iyazu billah mai wannan magana ko ya hardace hizbi dubu sittin(60,000) makomarsa tayi muni.
  Da wannan ne yasa yan izalah duk abinda yarabi ma’aiki zasu dasa kiyayyah dashi, fara da matan annabi, sahabban annabi, kai harma da diyar annabi FADIMA ba irin sharri da jafa’i da dan taimiyya baiyi ga sayyidina Aliyu ba, haka kuma sayidatuna Aisha, wai ko baku karanta littatafan ibn taimiyya bane?
  Yan izalah basu ki waliyai ba saidon suna jinin fadimatu
  DON MU BAMUGA MASU CIN MUTUMCIN ANNABI DA SAHABBANSA DA ‘YA YANSA DA MATAYENSA DA JIKOKINSA KAMARKU BA, KO SUNNAR MA KUN FAKE DA’ITANE DON KUJI DADIN KIRAN WASU YAN BIDIA amma alhamdulillah domin hadisine acikin bukhari annabi yanacewa duniya bazata tashi ba har sai sunnah an juyata ta koma bidi’ah ita kuma bidi’ah anbata sunan sunnah.
  DAGA KARSHE INA ROKON YAKAREMU DAGA BIN TAFARKEN KHAWARIJ KODA AMAFARKI.

  • Toh mu dai abun sani ga ahlisunnah shine dan bidi’a da dan shi’a sashen su mosoyan sashe. Kai dan darika har ka samu daman fadan wata magana bayan ababen dake cikin miyagun littafanku na shirka ga allah s.w.a da fifita waliyan ku akan annanbi da sahabban sa acikin littafanku kamar yaqutatul fareeda. Kamar jawahirul ma’any. Da al burda da ishriniya da sauran miyagun littafan ku cewa kunkayi wayennan shehunnan nan naku sune ALWASILA zuwa ga allha sai kun ka cire annabi kai koda baku cire annabi ba ku kafirrai ne kuma makaryita ne amma wannan fa sai idan kun yadda da abunda ke cikin al qur’ani gaskiya ne don allah na cewa cikin suratu ZUMAR aya ta uku sai allah ya ce; lallai wayenda suka riki wasu waliyai koma bayan allah. Sai suce mu ba bautar su muke yi sai don SU KASANTAR DAMU ZUWA GA ALLAH ABUN KUSANTARWA da sannu allah zai yi hukunci a tsakaninsu cikin abunda suke sabani acikin sa don allah baya shiryar da duk wanda yake MAKARYACI NE KUMA KARIFI. To dan bidiah da dan shi’a kaji sakon allah dauke da bayanai mai zafi maza ka juyo baya kuma ka mika wuya ka sallama kanka ga allah don mai yafiyane kuma mai jinkai

 6. Pingback: KUYI RIKO DA AQEEDAR SALAF KU KAUCE WA GURBATATTUN AQEEDU | welcome To Nibras's Blog | Get Updated Always!

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s