‘YAN MATAN FACEBOOK(Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe)


‘YAN MATAN FACEBOOK
Hausawa suna cewa ‘Yammata
adon gari, In ba ku ba gida, In kun
yi yawa….. .Annabi (S.A.W) ya na
cewa: “ Mata warin takalmin ‘ya’ya
Maza ne” Alqur’ani mai girma
kuma yace: “Su sutura ne gareku
(maza) kuma sutura ne gare su
(mata)”
Lalle Allah ya halitta Mata cikin son
kawa da kwalliya, kamar yadda
hakan ba haramun ba ne, matukar
ana cancada adon ne cikin iyakar
Musulunci.
Daga cikin abubuwan da suke ba
ni mamaki a wannan dandali akwai
yadda na ke ganin ‘yan mata ke
saka hotunansu tsirara don Mutane
su kalla suji dadi ba tare da sun
biya sadaki ba, abin ban mamakin
ma har da wasuu daga cikin matan
aure. Amma abin tambaya anan
shine: wai me ke jawo wannan hali
na rashin kunya da yakamata ne?.
Tsammani na, abubuwan da ke
jawo hakan:
• Wassu ba su san cewa hakan
Harmun ba ne.
• Wassu kuma tallen kai ne.
• Wassu kuma fitsara ce zalla!!
• Wassu kuma gaurin gwauranta
ne.
• Wassu kuma wasa da Nishadi ne.
• Wassu kuma ban sani ba!!
Allah madaukakin sarki a cikin
Littafinsa ya umarci Mata su rufe
jikkunansu da tufafi, ka da su
baiyyana adonsu sai ga
Mazajensu ko Muharramansu.
Kamar yadda Allah ya kira irin
wadannan shiga da sunnan fita irin
ta Jahilyyar farko. Me wannan hali
inji Allah Jahila ce!!!
In ka tambayi Maza, ko za ku iya
aurar irin wadannan matan? Sai ka
ji sun ce maka: Allah sauwaka!!
Dalilinsu wai bayan kowa ya san
komai nata!!!
Manzon Allah yace: “ Wanda ba ya
damuwa da wa zai shiga kan
Matarsa, ba zai shiga Aljanna ba”
Tirkashi!! Ina ga wadda ta ke tallata
kanta wa duniya baki daya???
Wadanda su ke ganin saboda kirar
da Allah yai musu, ba wanda zai
gani bai hadiyi yawu ba, sai muce:
Manzon Allah yace: “ Akwai wassu
‘yan Wutan da babu su a
zamanina, cikinsu akwai: “Mata ma
su shigar tsirara, ko sun sa tufafi
jikinsu a baiyyane ya ke, sun
karkace suna kokarin karkatar da
mutane, Ba za su shiga Aljanna
ba, kamshin ta ma, ba za su ji ba”
Allah ka raba mu da wannan
rashin rabo!! Ameen
Rashin Aure ya ke sa Wassu shiga
wannan sana’a, don ragewa kai
gauri da gaunin Tuzurunta ka,
Maganin wannan karbar Sunnar
Manzo ta hanyar Aure. Wanda ya
sanki ‘ya mace ba zai aure ki ba, in
kuma ya aura. Ba za ki yi kima a
idanunsa ba,har Abada. Tsalle
daya shi ke jefa mutum Rijiya.
Ya ‘Yar uwata ki rasa abin wasa da
shi, sai Mutuncinki da na ‘yayanki,
Allah ya halasta wassu wasanni,
ya kuma sanya cikekkiyar nutsuwa
cikin karatun Alqur’ani. Balle uwa
Uba wasan miji da mata, Ki
sumbace shi, a baki lada, ki fada
masa magana mai dadi ki samu
lada, Dukkan abin da zakiyiwa
mijinki na kyautatawa lada, Balle
uwa uba…
Cikin Mata akwai kamammu ko
nan cikin Facebook, adadinsu
kuma kara yawa ya ke, Wannan
yasa na rubuta wannan makala
don ‘Yar uwa kada jirgin Annabi
nuhu ya ta shi ban da ke ciki.
Annabi Mai tsira da aminci yace:
‘’WANDA YA TUBA DAGA LAIFI
KAMAR WANDA BAI TABA YIN
LEFIN NE BA”
‘Ya Allah ka tsare mana Kannanmu
da Yayan Musulmai.
AMEEEEEEEEEEEEE
EEEEEEEEEEEEEEN

Advertisements

102 thoughts on “‘YAN MATAN FACEBOOK(Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe)

  1. Allah ya karawa malam lapia.Yakareshi daga sharrin masu sharri yasaka maka da gidan anjanna FIRDAUSI ameeen

  2. Allha saka da Alkayree ya nunamana gaskia gaskia ce yabamu ikon binta ya kuma karemu daga sharrin shedan da rudin dunia.yabamu ikon bin Qurani da sunnar manzo Allah saw

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s