Azumi Ranar Ashura


Azumin Ranar Ashura
Wannan ranar ita ce ranar goma
da watan muharram na ko wace
shekara. Watau asalin wannan
azumi tun kafin zuwan musulunci
ne Kuraishawan Jahiliya su ke
yinsa. An ce da shi ne azumin da
aka wajabta har sai da aka rubuta
wa alumma azumin Ramadan sai
shi ya zama na nafila.
Yahudawa sun kasance suna
azumin goma da watan tevet
watau watan goma na shekaransu
domin godiya. Amma an samu
sabani tsakaninsu a dalilin da yasa
aka wajabtachi akan su. Da
musulunci ya zo sai ya bayyana
dalilin cewa wannan ranar farin
cikice da kuma godiya ga Allah
domin ranar da Allah Ya tsirar da
Annabi Musa da mutanensa da ga
Firauna. Saboda haka manzon
Allah – tsira da amincin Allah su
tabbata agareshi- y ace, mu
musulmi mun fi chanchanta da
Annabi Musa saboda haka yayi
umurni da muyi azumin.
To ya yanuwa maza da mata, a
lokacin da muke yin wannan azumi
wanda ya dace da ranar assabar
24th na wannan wata na nubemba,
mu roki Allah Madaukaki da ya
kubutar da mu daga wadannan
kananan firaunoni wadanda suke
watsa barna acikin kasar mu da
soran kasacen musulmi. Kuma ya
kamata mu yalwata wa iyalenmu
da abinci mai yawa da inganci
kamar yadda yazu a wanni hadisi
ko da yake mai rauni ne. wannan
ranar farin ciki ne da kuma ibada
da yin dadi. Babu wurin bakin ciki
ko bacin rai a wannan ranar. Kuma
mu sani fa Allah Mafi karfi yana
sane da abunda ashararun mutane
da azzalumai suke yi. Yana musu
jinkirine domin su kara zurmawa
cikin zunubi.
Ana so mutum ya kara da ranar 9
ko kuma 11 ya hada da ta ashura,
ko ko kuma ya yi azumin kwana
ukun wandan yafi hakanan. Amma
ga wanda akwai azumin ramkuwa
na Ramadan akansa, Imam Malik
yafi rinjayar da gabatar ramuwar
akan ashura domin Allah yafi son a
cika farilla da yin nafila.
Allah ya shiryar damu gaba daya.
Amin.

Advertisements

2 thoughts on “Azumi Ranar Ashura

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s