SHARHI AKAN WAKAR “NI DAI BARHAMA NAKE BAUTAWA, DAN SHI YA HALICCENI”


SHARHI AKAN WAKAR “NI DAI BARHAMA NAKE BAUTAWA, DAN SHI YA HALICCENI”

Daga Muhammad Rabiu Umar

Dalilin Yin Wakar “Ni Dai Barhama Nake Bautawa, Don Shi Ya Halicce Ni”

A yan kwanakin nan wata waka da wani mawaki ya yi mai take “Ni dai Barhama nake bautawa, don shi ya halicce ni” ta jawo cece-kuce a tsakanin mutane, kuma da yawa daga cikin mutane sun yi mamakin a ce wai musulmi ne ya yi wannan wakar, wanda daga baya-bayan nan gwamnatin Kano ta hanyar hukumar tace finafinan ta bada sammacin a kamo wannan mawaki.

Amma alal-hakika duk wanda ya san irin akidar da take cikin manya-manyan littattafan darikun sufaye – musamman yan tijjaniyya – to ba zai yi mamakin jin irin wannan waka ta fito daga irin masu wannan darika.

Idan muka dauki babban littafin darikar tijjaniyya mai suna “Jawahirul Ma’ani” zamu ga cike yake da akidar “Komai Allah ne” ma’ana duk wani abu da yake duniyar nan Allah ne, kuma in an bauta masa babu laifi, Allah aka bautawa, ga kadan daga cikin abin da ya zo akan haka : Shehu Tijjani ya ce :
“فما في ذوات الوجود كله إلا الله سبحانه وتعالى تجلى بصورها وأسمائها، وما ثمّ إلا أسماؤه وصفاته” (جواهر المعاني : 1/259).

Ma’ana “Babu abin da yake cikin zatin dukkan samammu gaba dayansu sai Allah Subhanahu Wa Ta’ala, shi ne ya bayyana a surarsu da sunayensu. Babu wani abu sai sunayensa da siffofinsa” (Jawahirul Ma’ani 1/259).

Wannan magana tana nuna cewa duk wani abin da yake samamme a wannan duniya to ba komai ba ne face Allah ne, saboda Allah ne ya bayyana a cikin dukkan komai da sunayensa da siffofinsa.
A wani wurin ya ce :

“إن جميع المخلوقات مراتب للحق…فإن الوجود عين واحدة لا تجزؤ فيها على كثرة أجناسها وأنواعها ووحدتها” (جواهر المعاني : 2/92).
Ma’ana : “Dukkan ababen halitta wasu yanki ne na Allah….saboda da dukkan samamme abu daya ne, babu wani yanki-yanki a cikinsa, duk da jinsinsa mai yawa da nau’o’insa da hadewarsa” (Aljawahir 2/92).

Wannan bayani yana nuna cewa duk wata halitta Allah ce ita, kuma komai da muke gani abu daya ne, wanda shi ne Allah!.
Ya sake cewa :
“فكل عابد أو ساجد لغير الله في الظاهر فما عبد ولا سجد إلا لله تعالى، لأنه هو المتجلي في تلك الألباس، وتلك المعبودات كلها تسجد لله تعالى…وقوله “لا إله إلا أنا” يعني لا معبود غيري وإن عبد الأوثان من عبدها فما عبد غيري” (جواهر المعاني : 1/184)
“Duk wani mai bauta ko mai sujjada ga wanin Allah a zahiri, ba wanda ya bautawa ko ya yi wa sujjada sai Allah Ta’ala, saboda shi ne yake bayyana a cikin wadannan abubuwa, kuma duk wadannan abubuwa da ake bautawa suna sujjada ne ga Allah (S.W.T)….sannan fadin Allah “Babu abin bautawa sai ni” yana nufin babu wani abin bautawa, wanda ba ni ba, ko da kuwa masu bautar gumaka sun bauta masu, ba su bautawa wani ba” (Jawahirul Ma’ani 1/184).
Wannan kadan kenan daga cikin mummunar akidar dake cikin wannan babban littafin na darikar tijjaniyya. To yanzu dan uwa mai karatu wanda ya karanta wadannan maganganu, kuma ya yi imani da su, ya yarda da cewa wanda ya yi su, waliyyi ne daga cikin waliyyan Allah, kuma duk abin da yake fada Annabi ne (S.A.W) yake fada masa, a farke a cikin barci, to yaya ba zai ce “Barhama Yake Bautawa ba”!.

Wata kila mai karatu ya ce, to ba Barhama ba ne ya koyar da haka, don haka me ya sa shi mai wakar bai ce “Shi Tijjani yake bautawa ba” sai ya ce Barhama.

Dalili, shi kansa Barhama din wato shehu Ibrahim Inyass haka shi ma ya koyar ya kuma kira muridansa da mabiyansa a kan haka, a cikin littattafansa, ga kadan daga cikin abin da ya fada a kan haka :
Yana cewa :
فإنّ الشّيخَ مظـهرُ ذات ربِّي وعينُ العَين عينُ أبي العباس. (( ديوان تحفة أطايب الأنفاس )) (ص86).
Ma’ana : Lallai hakika shehu shi ne Mazharin zatin Ubangijina. Kuma Hakikanin zati, shi ne zatin Abul Abbasi (wato shehu Tijjani).

Anan zamu ga Inyass yana cewa shehu Tijjani shi ne Allah, kuma duk wani zati na wani abu, ba komai ba ne face zatin shehu Tijjani, don haka komai shehu Tijjani ne, shi kuma Allah ne!!.

A wani wuri cewa ya yi :
خليفةُ الله في أرضٍ لذلك مَن رآكمُ قد رَأى ربَّ البريَّات
Ma’ana : “Khalifan Allah a bayan kasa, don haka duk wanda ya ganku, to lallai ya ga ubangijin halitta”. (Duba littafinsa Diwanu Tuhafatil Adayibil Anfas).

Subhanallahi, don ka ji mai karatu duk wanda ya ga shehu Tijjani to ya ga Allah, Ma’ana da Allah da Shehu Tijjani duk abu daya ne!!!.

Wannan kadan kenan daga cikin akidun da suke cikin littattafan wadannan sufaye, kuma a kansu ne suke kokarin renon mabiyansu, wanda har akwai wata tarbiyya da ake wa muridi, wadda bayan ya yi ta, sai zama Allah, kuma komai ya zama Allah a wurinsa, Sheikh Dahiru Mai gari (Allah Ya Yi masa Rahama) ya yi rubuta akan wannan tarbiyya da darika, ya tabbatar da wadannan abubuwa.

Don yan uwa in ana so a magance ci gaba da faruwar irin wadannan wakoki to dole ne sai an wancakalar da wadancan littattafai, kuma an dawo kan koyarwar Alkur’ani da Hadisi a bisa fahimtar magabata na Kwarai. Allah ya tsare mana Imaninmu Ameen.

316 thoughts on “SHARHI AKAN WAKAR “NI DAI BARHAMA NAKE BAUTAWA, DAN SHI YA HALICCENI”

 1. Duk wanda yafadi gaskiya too zaginsa ‘yan tijaniya suke yi: amma ance kuduba litatifai din ku duk :::::::::::::::::: ku

 2. Duk wanda yafadi gaskiya too zaginsa ‘yan tijaniya suke yi: amma ance kuduba litatifai din ku duk :::::::::::::::::: ku

 3. Shehu shehu new wlh Kai da k karanta jawahirul maani to Dan Kai ayi na suufaye NE Kai jahili k dauka for what to b hurimin k bane

 4. assalamu alaikum warahmatullahi wabaraka tuhu ya ikiwanil muslimina. Ina mika godiya ga allah madau kakakin sarki wanda babu wani abin bautawa face shi kadai,bashi datamka aduk fadin duniya gabadayanta, yau allah ya kawomu lokacin da wasu masu qaxafi suke yiwa bayin allah nifaqa da ihanati,gaskiya wadannan bayin allah waliyyaine duniya da lahira domin kuwa allah da manzonsa suka riqa, sunyi koyi da dabi,u kyawawa da halaye nagari irin na fiyayyen halitta wato annabi muhammad s.a.w. Qaulan wa fi,ilan, Shehu munsan al qur ani yariqa gami da zancen abban fadimatu. Shehu aikinsa gyaran zuciyar data dena aiki. ma,ana wadda ta bar ambaton allah awuni da kwana ,allah yasanar damu ya ganar damu mudena yin hassadu alaa ibadullahi.ameen summa ameen…………… Shehu barhama ba allah bane ba manzon allah bane waliyyin allah ne shehu masoyin baban fadima, s.a.w.

 5. AUWAL HADI. KAYI KOKARI AMMA ABANZA, DOMIN KUWA WADANNAN BAYANAI DA WANNAN MALAMIN YAYI AZAHIRI SUKE KAFIRCINE TSAGWARONSA DOMIN BA YADDA ZA’ACE KOMI ZAI IYA ZAMA ALLAH HARMA SHI SHEHUN NAKU YACE SHI WANI SASHINE NA UBANGIJI KAGA KUWA DUK MAI HANKALI WANDA HANKALINSA BAI FITA GANGAR JIKINSABA BAZAI TABA YARDA DACEWA WAI AKWAI WANI ABU DA BAZA’ IYA GANEWABA. DON HAKA INA AMFANI DA WANNAN DAMA IN YI GARGADI GA WADANDA SUKE RIYA CEWA WADANNAN MAGANGANU DA AKA CIROSU ACIKIN JAWAHIRUL MA’ANI BA’A IYA FAHIMTAR HAQIQANIN MA’ANARSU SU DAWO DA HANKALINSU DA BASIRARSU SU GANE CEWA ANA SON NE A KAFIRTASU NE.ALLAH YA FAHIM TARDAMU AMIN

 6. Mudai barhama muke so makiya kai cenko mudai mun san cewa ummar taka ba haka yafada ba
  shi dai yace
  nidai barhama nake so
  yaka mata ku daina yaya ta kar ya
  kaji ku ma kada ka manta cewa Allah zaitamba yeka ko da kalma da yane ranan da baki bazai ceko maiba

 7. ALLAH (S W T) SHINE ABIN BAUTA INDAI HAR MUSMIN KWARAI KAKE ANNABI MUHAMMED {S A W} YANA CEWA ALLAH SHINE ABIN BAUTA BASHIDA ABOKIN TARAYA ASHAHADU ALLA ILLAHA ILLALAH WA HADAHU LASHARIKA LAHU. WA ASHADU ANA MUHAMMADU RASULULAH

 8. Amma dai ‘yan izala kunji kunya wallahi. ya kamata kusanj duk wanda yakeja da waliyyi to da Allah yake fada. kuma wannan Shehu Tijjani da kuketa suka akanshi, jikan Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam ne. kuma wanda duk yake kiyayya da jikokin Annabi to Aljanna saidai ya gani ga wasu. yanzu ga misali “idan nace ina sonka amma kuma banason iyalan ka, ai cewa zakayi dama ba donka nakeyi ba” to kamar haka ne. Idan kana son Annabi dole ne kaso iyalan shi. Ina sonka Shehu Tijjani. Da Shehu Ibrahim Inyass dakuma sauran Waliyyai. kukuma yan izala, Allah ya shirye ku idan ku masu shiryuwa ne.

 9. A’a malam kaje ka tambaye masa nan abun tukkun na shehu yana cewa idan ance maku nace wani abu to ku auna da al-qur’ani da hadisi idan yayi dai dai ko kar6a idan baiyi ba to ku watsarmini dashi duk acikin wannan littafin da wannan mutumin ya kawo

 10. Allah Kaine Allah Babu Abin Bauta Saikai Ya Yan’uwa Yakamata Mutashi Mukoma Makaranta Ta Sunnah Mukaranci Tauhidi Domin Muyaki Jahilci.

 11. kai agaskiya yan izala kuna nuna kanku kuna ganin mutane suna sallah suna azumi suna Zakka suna zuwa aikin hajji(makka),sannan akullum kowane fdaya daga cikin su yana fadin LA’ILAHA ILLALLAH akalla sau 300 arana, amma duk da haka baku yarda cewa su musulmine ba.To yakamata ku kawo wasu shikashikan musuluncin wata kila akwai wasu bayan wadannan,idan kuwa har baku kawo ba to ya tabbata ku jahilai ne,domin ANNABI SAWW shidai wadannan ya koya mana.
  maganar SHEHU tijjani da SHEHU Ibrahim kuma kun jahilci abin da suke nufi,wannan shine gaskiyar magana

 12. Aka fassara al qur’ani ma balle sufanci wallahi kuji tsoron allah kaji wai sufanci kar kabiyewa son xuciyan ka kafada wa halaka

 13. Wa ake kira ni barhama Na kira zo mu tafi,r.t.a.kuma Shehu yace MAMIN DUA’AHADUN BI AIYI MAKANATIN ILLAHU KUNTU MUJIBUHU WA ALIMA.tau munkirai kuy hatara,kundai ji kuma kungani tunnan duniya,idan tsutazu yazo mutuwa da haushin kare yake karewa,ma ana da kukan kare ustaz,yake mutuwa.nine abubakari Na rijau kusani,wato babawo

 14. barhama binka tilasne ga halitta dole kanwar naki! to ni akanlamarin shehu bani tsoron mutuwa itama mutuwar ta mace cikinai dajiyar dankwa shine yayita yakirata da mutuwa maganarga danai sallama kawai kayyi shiru eh ni rayuwata nabaka shehu kai yanda kaso!!! shehu yace fakullu suwa haza wara’awara’i inji shehu kai still inyass no going back from alsheik anas abdulhamid anaconda member of bahrul hakikati barkum

 15. Duk da cewa ni ban da wani kungiya amma alal hakika in dai haka yake rubuce a Jawahirul Maani gaskiya bisa ilimin Arabiyyah da Al-Qur’ani da Hadisi da Fiqhu da na samu zan iya cewa wannan Babban Kuskure ne. Sannan bugu da kari samun rabuwan kan Al-Umma Musulmi ma shi ya fi muni gaskiya. A zamanin yanzu da yawa daga cikin Al-Umma su na fifita kungiyoyinsu akan Addini wanda hakan bai dace ba. Ba ruwan Allah da kai dan Izala, Darika,Shia ko ma menene. Kawai ka bi Al-Qur’ani Manzon Allah… Allah ka sa mu gane gaskiya kuma ka bamu ikon bi. Ka kuma tsare mu daga bin karairayi da son zukatunmu… Ka kuma hada kan Musulmi baki daya…. Ameeen… Ni ne naku: Abdul-Basid

 16. hakika cikakken tauhidi shine, kaidaita Allah da bauta shi kadai, sannan bin sunnar annabi Muhammad s.a.w
  yaku yan tijjaniya kukanku kunsan inda akidarku ta dosa. dama can ba’a ginata saboda bin umarnin Allah ba. kuna fifita shehunan Ku akan ALLAH DA ANNABIB SA mude fatanmu Allah yakarbi rayuwar mu akan sunna

 17. Kai maqaryace wannan ba jawahirillma aaniy bane saidai jawahirul qaryanku da kukawallafa. Inada jawahirulma aaniy duk shafin dakukace naduba babushi.
  Inaa kukasami naku?

 18. kai jama’a dikwanda yahada alh da wani dai yayi shirka babba sannan alh baye yafe shirka haba yan uwa yakamata migane gaskiya kuma yakamata mikama sunnah hannu bibbiyu alh yasa mudace ameen summa ameen

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s