344 thoughts on “SHARHI AKAN WAKAR “NI DAI BARHAMA NAKE BAUTAWA, DAN SHI YA HALICCENI”

  1. Assalamu alaikum, malam a hakikannin
    gaskiya kayi kuskure mai yawa domin su
    litattafan sufaye ba’a daukarsu kai tsaye
    ayi musu fassara ba tare da neman ilimi
    akansu ba, kamar yanda kai kayi, kamar
    yanda aka sanine shi ilimi fanni biyu ne
    akwai ilimi na shari’a, akwai na hakika
    ma’ana mu’arifa watau sanin Allah,
    dukkansu dolen mu muyi imani dasu kuma
    mu yarda dasu, ya isheka hujja da kasan
    cewa Annabi musa a.s mai daraja ta uku
    acikin ulul azmi, Allah swt ya umarceshi da
    yaje ya nemi ilimi a wajen wani wanda ba
    Annabi ba, ba kuma mursali ba, domin ya
    nuna mana iliminsa fa fanni biyu ne, kai
    kuma daya kake takama dashi shine na
    shari’a, malam inason kasani fa shi Allah
    baya sanuwa ga wanda bai nemi ilimin
    saninsa bafa, ta wace hanya zakayi gyara
    akan abinda baka saniba, kuma gyaran ma
    ga wadanda suka tohu suka ginu suka kare
    acikin sanin Allah, ta yaya zaka shiga gonar
    da ba takaba bakasan me aka shukaba
    kace zakayi noma acikinta, anya babu
    kuskure kuwa? kai wannan barna ce me
    yawa. Acikin bayanan da kayi akwai
    wadanda suke lallai akwaisu a cikin
    jawahiril ma’ani amma kasancewar baka
    da ilimin abin ba zaka san abin da ake nufi
    da haka ba. shawara ta anan itace don
    Allah ku kiyaye da shiga harkar dabata
    shafeku ba musanman irin wannan domin
    wallahi zaka fada halaka, amma in ka tsaya
    matsayinka sai a zauna lafiya nagode

    Like

Leave a reply to yusuf a. Adam still annabin dai s.a.w Cancel reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.