GIRMAMA SALLAH


Tambaya zuwa ga ‘yan’uwa Musulmai!!!
Dun Allah ya zakaji in akace maka yau shugaban kasanku ko wani attajiri a garinku zai kawo maka ziyara kuzo ku gana, sannan yazone da zimman ka fada masa bukatunka ya biya maka? Ya zaka tarbeshi?
Shin zaka iya kuna tattaunawa dashi kana kallon wani wuri?
Shin zaka iya kana tattaunawa dashi har ka dinga wani tunanin da zai mance dakai kana tare dashi?
Shin zaka iya kana tattaunawa dashi kana hanzari, kana so yayi ya tafi? Amsa wannan tambayoyin sannan kayiwa kanka hukunci, meyasa inkana sallah kake sanya tunani a zuciyarka har ka mance kana sallah?
Meyasa inkana sallah kakeyin sauri sauri ka kammala?
Meyasa inkana sallah kake juye juye?
Shin kasan da waye kake gana kuwa? Toh inbaka sani ba, da zaran ka fara sallah toh kana ganawa da Allah ne, mahaliccinka, mahaliccin shugaban kasanka, da attajirin garinku da kowa da komai, ya zama wajibi a gareka ka girmama matsayinka gaban Allah madaukakin tsarki domin samun Tsira. Allah shiryar damu, Ka rabamu da sharrin shaidan…

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s