ALAMOMIN CIKAWA DA IMANI GUDA 21(Malam Aminu Ibrahim Daurawa)


ALAMOMIN CIKAWA DA IMANI
GUDA 21
Wannan duniyar cike take da rikici,
da musifu, da bala’o’i, da tashin
hankali da jarrabawa, da matsaloli,
babbar nasara shine, cikawa da
imani,
Malamai sunyi bayanai gamai da
wasu alamomi, idan mutum ya cika
da su, ana yi masa fata na gari
Sune
1- cikawa da kalmar shahada
2- mutuwa da gumin goshi
3- mutuwa a daren Juma’a ko
ranar Juma’a
4- Shahada a filin yakin daukaka
Addinin Allah
5- Mutuwa a tafarkin Allah
6- mutuwa da Annoba
7- mutuwa da sababin ciwon ciki
8- mutuwa da dalilin nutsewa a
ruwa
9- mutuwa karkashin gini
10- mutuwa da kunar wuta
11- mutuwa da ciwon kaluluwa
12- mace ta mutu a wajen haihuwa
13- wanda aka kashe shi, wajen
tsare dukiyar sa
14- wanda aka kashe shi wajen
tsare iyalan sa
15-wanda aka kashe shi, saboda
addinin sa
16- wanda ak kashe shi wajen
kare kansa
17- wanda ya mutu da ciwon tarin
fuka
18- wanda aka kashe shi, akan
hakkin sa
19- wanda ya mutu wajen gadin
addini da dukkiyar Al’umma
20- wanda ya mutu yana cikin aikin
alkhairi, kamar sallah dawafi,
azumi sujjada, da makamantansu,
21- wanda ya mutu mutane suna ta
yi masa sheda ta gari,
Dalilan wadannan bayanai, daga
littafin Allah da sunnar Annabi saw,
suna cikin littafin Ahkamul Janaiz
na Shaik Albaniy da salatul
Mumina na Dr Saeed alqahdaniy
Allah yasa mu cika da imani Amin

55 thoughts on “ALAMOMIN CIKAWA DA IMANI GUDA 21(Malam Aminu Ibrahim Daurawa)

Leave a reply to Adam abualamin Cancel reply

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.