GA SAKON MALAM SA’ADU ZUNGUR NA WAKA SAMA DA SHEKARA 50 AMMA KAMAR YAU YA GABATAR(Sheikh Isa Ali Pantami)


“Matukar a arewa da karuwai,
yan daudu dasu da magajiya.
Da samari masu ruwan kudi,
Ga mashaya can a gidan giya.
Matukar yayan mu suna bara,
Titi da Loko-lokon Nijeriya.
Hanyar birni da na kauyuka,
Allah baku mu samu abin miya.
Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu mai tanyonsu da dukiya.
Babu shakka yan kudu zasu hau,
Dokin mulkin Nijeriya.
In ko yan kudu sunka hau,
Babu sauran dadi, dada kowa zai
sha wuya.
A Arewa zumunta ta mutu,
Sai karya sai sharholiya.
Camfe-camfe da tsibbace
tsibbacen,
Malaman karya yan damfara.
Sai karya sai kwambon tsiya,
Sai hula mai annakiya.
Ga gorin asali da na dukiya,
Sai kace dan annabi fariya.
Jahilci ya ci lakar mu duk,
Ya sa mana sarka har wuya.
Ya sa mana ankwa hannuwa,
Ya daure kafarmu da tsarkiya.
Bakunan mu ya sa takunkumi,
Ba zalaka sai sharholiya.
Wagga al’umma mai zata yo,
A cikin zarafofin duniya.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya ,
Zaya sha kunya nan duniya “.
“Mu dai hakkin mu gaya muku,
Ko ku karba ko kuyi dariya.
Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.
Gaskiya ba ta neman ado,
ko na zakin muryar zabiya.
Karya ce mai launi bakwai,
ga fari da baki ga rawaya.
Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.
Marigayi Sa’adu Zungur a cikin
waken sa mai suna “Arewa
Jamhuriya ko Mulukiya”.
O Allah forgive us and provide a
way out for us in this World and in
the next.

Advertisements

11 thoughts on “GA SAKON MALAM SA’ADU ZUNGUR NA WAKA SAMA DA SHEKARA 50 AMMA KAMAR YAU YA GABATAR(Sheikh Isa Ali Pantami)

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s