KOWA NA CIKIN HASARA SAI MUTUMIN DA KAWAI YA SIFFANTU DA SIFFOFI HUDU(Ibrahim Jalo Jalingo)


ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ} :ﻭﺍﻟﻌﺼﺮ)١( ﺍﻥ ﺍﻻﻧﺴﺎﻥ ﻟﻔﻲ ﺧﺴﺮ
)٢( ﺍﻻ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﻣﻨﻮﺍ ﻭﻋﻤﻠﻮﺍ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﺎﺕ ﻭﺗﻮﺍﺻﻮﺍ
ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﺗﻮﺍﺻﻮﺍ ﺑﺎﻟﺼﺒﺮ)٣ )}.
Ma’ana: {1. Ina rantsuwa da
zamani. 2. Lalle ne mutum yana
cikin hasara. 3. Face wadanda
suka yi Imani, kuma suka aikata
ayyuka masu kyau, (suka bi
Sunnah cikin ayyukansu) kuma
suka yi wa juna wasiyya da bin
gaskiya, kuma suka yi wa juna
wasiyya da yin hakuri}. Intaha.
Allah Madaukakin Sarki Ya
bayyana mana a wannan Sura
cewa duk wanda bai hada siffofi
hudu tare da shi ba to kuwa yana
cikin hasara ko ma wane ne shi,
siffofin kuwa su ne kamar haka:-
Siffa ta farko: Ya zamanto mai
Imani.
Siffa ta biyu: Ya zamanto mai bin
Sunnah cikin ayyukansa.
Siffa ta uku: Ya zamanto mai yi wa
‘yan’uwansa wasiyya ne da
lazimtar bin gaskiya.
Siffa ta hudu: Ya zamanto mai yi
wa ‘yan’uwansa wasiyya ne da
lazimtar yin hakuri a kan hanyar
gaskiya da suke kanta.
Allah Ya taimake mu Ya sanya mu
cikin wadanda za su siffantu da
wadannan fiffofin. Ameen.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s