Khuduba Daga Masallacin Azeez Billah, Hadayek Zeitun, AlQahira,Misra


Khuduba Daga Masallacin Azeez Billah, Hadayek Zeitun, AlQahira,Misra..

Bismillahirrahmanirraheem… Ga Kadan Daga abinda Khudubar Ta kunsa,

Malam yayi maganane kan matsalar da kasar masar take ciki, da irin yanayin abokan gaba da suke neman yi mata illah,

Yace da yawa yanzu mutane hankalinsu ya juya baki daya ga barin tabbatar da shari’ah, addini ya zama wasa. Toh wannan ba karamin hadari bane,

Yace zanga zanga da ake shirin yinsa nan gaba ran 30. Ba karamar bala’I bace, domin wajibi ne ayiwa shugaba da’a akan duk abinda bai tsaba wa Allah ba, kaman yadda annabi yayi umarni ayi.

Sannan ya kara da cewa wannan fita da za’ayi ka iya jawo fitar mutane da yawa daga cikin musulunci, domin duk wasu musulmai da suka dauki makami kan junansu, dashi mai kisan da wadda aka kashe duk suna wuta,

Ya kara da cewa Mu shari’ah mukeso, babu ruwanmu da addini irin ta almaniyyah ko demokradiyyah.

Yaja hankalin mutane sosai na kada mutun ya sake ya bari shaidan yayi wasa da zuciyarsa, ya fita zuwa wannan hayaaniya,

Mutun ya tsaya wurin kare addininsa da iyalansa da dukiyarsa kawai, duk wadda yazo zaiyi wa wa’innan abubuwa ta’addanci toh alokacin zai tashi ya karesu, kuma inya mutu ya zama shahidi.

Amma yace duk wadda ya fita yaje ya mutu a wannan wuri toh ya tabbata yayi mutuwa irin ta jahiliyyah.

Yace dolene ayi hakuri da shi shugaba na yanzu, domin annabi(sallallahu alaihi wasallam) yace ‘Duk wadda yaga wani abin ki tattare da shugabansa to yayi hakuri’

Kuma yana daga cikin wasiyyah da annabi(sallallahu alaihi wasallam) yayi mana, yace ‘Na horeku da ji da kuma biyayya, koda ko an daura muku shugaba bawa daga habasha ne’

Daga Karshe yayi addu’a wa kasar masar da sauran kasashen musulmai baki daya,

Wassalaatu wassalaamu ala rasulillah.

One thought on “Khuduba Daga Masallacin Azeez Billah, Hadayek Zeitun, AlQahira,Misra

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s