DABI’UN MUMINI A LOKACIN FITINTINU(Sheikh Isa Ali Pantami)


DABI’UN MUMINI A LOKACIN
FITINTINU: Allah ka bamu nasara
Duniya da Lahira,…
Annabi (SAW) yana cewa: Kuyi
gaggawan aikata ayyuka (na
alheri), saboda fitintinu zasuyi
yawa kamar yankin dare mai duhu.
Mutum zai wayi gari yana MUMINI,
gabannin YAMMACI kuma ya
zama KAFIRI. Wani kuma zaiyi
YAMMACI yana MUMINI gabannin
GARI ya waye ya zama KAFIRI.
Saboda zai sayar da ADDININSA
don Neman kayan Duniya (Muslim
ya ruwaito).
DABI’UN MUMINI A CIKIN
FITINTINU sune:
1) JURIYA, DA TAUSASAWA DA
BIN ABU MATAKI-MATAKI. Annabi
(SAW) yana cewa: Tausasawa
idan ya shiga komai yana kyautata
shi. Idan kuma aka cire shi a komai
yana lalacewa (Muslim ya ruwaito).
2) TAQWA DA CIKKAKIYAR
BIYAYYA GA ALLAH. Allah yace:
Wanda yayi taqwa ga Allah. Shi
(Allah) zai sanya masa mafita
(Suratut-Thalaq)
3) HAKURI DA TABBATA KAN
GASKIYA. Don Annabi yace
wadannan kwanaki ne na hakuri
“Ayyaamus-Sabr”
4) ADALCI GA MASOYI DA
MAKIYI. Allah yace: Idan zakuyi
Magana kuyi adalci.
5) ADDUAH. Rokon Allah ginshiki
ne na warware matsala.
Yaa Allah ka kare Rayuwa, da
dukiya da mutuncin bayinKa
Salihai daga Munanan Fitintinu,

Advertisements

7 thoughts on “DABI’UN MUMINI A LOKACIN FITINTINU(Sheikh Isa Ali Pantami)

  1. Malam Allah ya kara maka tsawon rai da aikata aiki nagari arayuwar ka yakareka daka sharrin duyiya da fitununta Yakuma sareka daga azaban kabari Allah yasa Aljannah firdausi itace makoma

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s