ME YA FARU A KARBALA 8(Dr. Mansur Sokoto)


Matsayin Sayyidina Hussaini game
da gwamnatin Yazid
Kafin mu je can, yana da kyau
muyi waiwaye game da gwamnatin
da ta kawo shi mulki, ina nufin
gwamnatin babansa Mu’awiyah.
Abinda aka sani ne cewa, har
zuwa lokacin wafatin sayyidina Ali
(R.A) ba wani nadadden sarkin
musulmi in ba shi sayyidina Ali din
ba. Babu kuma wanda yake
da’awar son ya karbi wannan
mukami daga wurinsa. Ya dai yaki
mutanen Jamal ne a kan sun dauki
mataki kan ‘yan tawayen da suka yi
juyin mulki suka kashe sayyidina
Usman; surukin manzon Allah, ba
tare da izninsa ba. Sannan ya yaki
Mu’awiya da rundunarsa a kan sun
ki yi masa Mubaya’a sai ya cika
masu sharadin da suka gindaya
ma sa na kashe ‘yan tawayen da
muka fada. Amma bayan da
sayyidina Ali ya samu shahada ta
hannun Abdurrahman bin Muljam
(daya daga cikin ‘yan Shi’ar da
suka ware daga cikin jama’arsa
kuma suka kafirta shi, suka yake
shi). A nan sai mutanen Iraq suka
nada dansa AlHasan, a yayin da
mutanen Sham suka nada tsohon
gwamnansu Mu’awiyah. Ba kuma
wani bangaren da ya tuntubi wani
a wajen aiwatar da muradinsa.
Wannan shi ne karo na farko a
tarihin musulunci da aka samu
sarkin musulmi biyu a lokaci guda.
Don warware wannan takaddama
ne Al Hasan Radiyallahu Anhu ya
gayyaci Mu’awiyah da kansa don
su sasanta, daga karshe kuma ya
sauka ya gabatar da Mu’awiyah, ya
kuma sanya mutanen Iraqi yin
haka. Wannan shi ya tabbatar da
busharar da Manzon rahama ya yi
a kan sa cewa, jikan nan nawa zai
zama shugaba, kuma a dalilinsa
Allah zai kawo karshen wata
tarzoma da zata barke a tsakanin
manyan bangarori biyu na
musulmi. Sahihul Bukhari, hadisi
na 2704 da Al Jami’ na Tirmidhi,
hadisi na 3775.
Don kada wani ya dauka cewa, a
littattafan Sunnah kawai aka
tabbatar da wannan mubaya’a da
AlHasan ya yi ma Mu’awiyah don
dunke barakar da ke tsakanin
musulmi zan kawo nassi daya
daga cikin mafi tsarkin littafan Shi’a
a gurinsu shine Bihar Al- Anwar na
Majlisi. Tare da akwai su wadanda
na tara su a wuri guda sun fi a
kirga. Ga abinda Majlisi ya ce:
” ﻭﻣﻦ ﻛﻼﻣﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻣﺎ ﻛﺘﺒﻪ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺼﻠﺢ
ﺍﻟﺬﻱ ﺍﺳﺘﻘﺮ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺑﻴﻦ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﺣﻴﺚ ﺭﺃﻯ ﺣﻘﻦ
ﺍﻟﺪﻣﺎﺀ ﻭﺇﻃﻔﺎﺀ ﺍﻟﻔﺘﻨﺔ، ﻭﻫﻮ: ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ
ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ، ﻫﺬﺍ ﻣﺎ ﺻﺎﻟﺢ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺑﻦ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ
ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺳﻔﻴﺎﻥ: ﺻﺎﻟﺤﻪ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ
ﻳﺴﻠﻢ ﺇﻟﻴﻪ ﻭﻻﻳﺔ ﺃﻣﺮ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ، ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﻳﻌﻤﻞ ﻓﻴﻬﻢ
ﺑﻜﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻨﺔ ﺭﺳﻮﻟﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺍﻟﻪ
ﻭﺳﻴﺮﺓ ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﻴﻦ، ﻭﻟﻴﺲ ﻟﻤﻌﺎﻭﻳﺔ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ
ﺳﻔﻴﺎﻥ ﺃﻥ ﻳﻌﻬﺪ ﺇﻟﻰ ﺃﺣﺪ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻩ ﻋﻬﺪﺍ ﺑﻞ ﻳﻜﻮﻥ
ﺍﻷﻣﺮ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻩ ﺷﻮﺭﻯ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ “.
“Daga cikin maganarsa (AlHasan
A.S) a cikin takardar sulhu da ya
tabbata a tsakanin sa da
Mu’awiyah a lokacin da ya ga ya
dace a daina zubar da jinainan
musulmi, a kashe wutar fitina. Ga
abinda Al-Hasan din ya rubuta:
“Bismillahir Rahmanir Rahim.
Wannan sulhu ne da AlHasan dan
Ali dan Abu dalib ya yi da
Mu’awiyah dan Abu Sufyan a kan
zai mika masa ragamar
shugabancin musulmi bisa
sharadin zai yi aiki a cikinsu da
littafin Allah da sunnar manzonsa
(SAWW) da kuma tsarin tafiyar
halifofi mutanen kirki. Kuma
Mu’awiyah dan Abu Sufyan ba shi
da hakken ya mayar da ita ga wani
bayansa, sai dai a bar al’amarin ya
zama abin shawara da tattaunawa
a bayan sa a tsakanin musulmi.
Duba: Bihar Al-Anwar (65/44) da
kuma littafin Al-Gadhir na Al-amini
(6/11).
Wannan takarda ta tabbatar da
abubuwa kamar haka:
1. Sayyadi AlHasan (R.A) mutum
ne mai hangen nesa da tausayin
al’ummar ma’aiki (SAWW).
2. Kuma ya yarda da musuluncin
sayyadi Mu’awiyah da cancantar
sa ga jan ragamar al’umma.
3. Bai dauka cewa, shugabancin
musulmi dole ne sai yan gidan
annabta ba. Ballantana cewa, wai
annabi (SAWW) ya yi wasici da
haka kamar yadda ‘yan shi’a na
baya baya suke cewa. A’a shi kam
yana tare da Ahlussunnah da suka
ce mulki abin shawara ne da
tattaunawa a tsakanin musulmi
kamar yadda Allah Ta’ala ya ce:
(( ﻭﺃﻣﺮﻫﻢ ﺷﻮﺭﻯ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﻭﻣﻤﺎ ﺭﺯﻗﻨﺎﻫﻢ ﻳﻨﻔﻘﻮﻥ))
“Kuma al’amarinsu (su musulmi)
shawara ne a tsakanin su, kuma
daga cikin abinda muka azurta su
suna ciyarwa (saboda Allah)
4. Ya amince da cewa, musulunci
shine bin littafin Allah da sunnar
manzonsa.
5. Ya yarda da halifofi hudu da
suka gabace shi gaba daya
(Abubakar da Umar da Usman da
Ali Radhiyallahu anhum) kuma
yana ganin su gaba daya a
matsayin mutanen kirki wadanda
duk shugaba ya kamata ya
kwatanta tsarin tafi da mulki irin
nasu.
6. Bisa wannan riwaya ya tabbatar
ma Mu’awiyah bai da alhakin nada
kowa a bayansa.
Wasu ruwayoyin ma cewa suka yi
ya yi masa sharadin idan ya ga
alamun ajali ya mayar da
shugabancin gare shi, shi
AlHasan. Amma kamar yadda
muka tabbatar a littafin “Kaddara
Ta Riga Fata” ba wani sharadi da
ya inganta a cikin wannan sulhu.
Yanzu dai mun tabbatar da
kasancewar halifancin sayyidina
Mu’awiyah halastacce kuma
wanda ya samu haduwar kan
al’ummar musulmi na duka
bangarori biyu masu fada da juna
wadanda kuma a hadisin da muka
kawo game da AlHasan manzon
Allah (S) ya kira su duka da sunan
musulmi.
Sai mu koma kan Yazid.
Bismillah..
Ku dakace mu.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s