ME YA FARU A KARBALA? 10(Dr. Mansur Sokoto)


Nadin Yarima Mai jiran gado
Kamar yadda muka fadi a baya,
HUSAINI Radiyallahu Anhu ya bi
umurnin wansa Al Hasan wajen yin
biyayya ga gwamnatin sayyidina
Mu’awiyah har sanda Allah ya
kawo karshenta a shekara ta 60H.
To, amma kafin haka Mu’awiyah ya
ayyana Yazid a matsayin Yarima
wanda zai gaje shi idan ajalinsa ya
cim masa. A nan ne Husaini ya cije
ya ce ba zai bada goyon baya ba.
Husaini ba shi kadai ya dauki
wannan matsayi ba. Akwai wasu
mutane uku da suka hada da
Abdullahi dan Umar da
Abdurrahman dan Abubakar da
kuma Abdullahi dan Zubair. Su
hudun basu bada goyon baya ba,
kuma dukkansu ‘ya’yan manya ne
kamar yadda muka gani. Ko
wannensu babansa na cikin
mutane goman da aka yi amanna
‘yan aljanna ne don sanarwar da
bakin da ba ya karya ya bayar a
kan su. Amma HUSAINI ya dara
sauran don shi yana da tasa
bushara ta kashin kansa. Amma
dai duk da haka wannan lamarin
ya ci gaba yadda aka tsara shi.
Mutane kuma sun yi mubaya’a ga
Yazid a matsayin Yarima.
Me ya sa sayyidina Mu’awiyah ya
nada Yarima? Kuma don me ya
zabi dansa YAZIDU? Amsa ita ce,
Sanin gaibu sai Allah.
Ku biyo mu don ku ji namu
hasashe a kan matsalar.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s