KASAN KANKA DA KANKA ( TAMBAYOYI 50)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)


Muna cikin wani zamani, da
mutane, sunfi damuwa da bayani
akan wasu fiye da kansu, sunfi
binciko laifin wasu fiye da nasu,
Sayyadina Umar Yace kuyi kanku
hisabi kafin ayi muku, Abubawan
da suke jawo tsira, Bautawa Allah
shi kadai da iklasi, akan sunnar
Manzon Allah, a cikin Akida, da
Ibada, Da mu’amalah, da Halaye
masu kyau, yi kanka tambaya,
hamsin don kasan matsayinka :
Allah yasa mu dace :
1- waye ya yika ?
2- mai yasa ya yika ?
3- kai waye ?
4- A ina kake ?
5- mai kake yi ?
6- Ina zaka ?
7- mai zai faru ?
8- mai kafi so a rayuwarka ?
9- mai kafi ki rayuwarka?
10- Duk abinda kakeyi, kana da
hujja a sharia?
11- su waye abokanka?
12- Yaya zamanka da iyayanka?
13- Yaya zamanka yake da
iyalanka?
14- Wace kungiya kakeyi don me?
15- A kwai wani yanzu haka da
bakwa shiri da shi?
16- Tsakaninka da Allah ka taba
cin amanar wani?
17 Kanayin karya?
18- Kana Dun guma ashariya?
19- Yaya zamanaka da
makotanka?
20- Wace shedar ilmi kake dauke
da ita?
21- kana salloli a Jam’i musamman
a masallaci?
22- yaya alakar ka da danginka
take ?
23- shin kana sada zumunta?
24- shin kana bayar da sadaka ?
25- shin kana karanta Alkur’ani mai
girma?
26- kana azumin litinin da
Alhamis?
27- kana sallar Shafi’i da wuturi?
28- kana zuwa asibiti domin ziyarar
marasa lafiya?
29- Kana yawan saba alkawari ?
30shin kana azumtar kwanaki
masu haske, ranar sha uku, sha
hudu, sha biyar?
31- shin kana kiyamul- laili?
32-kana umarni da kyakyawa da
hani da mummuna?
33- kana zuwa aiki akan kari kuma
ka tashi akan lokaci?
34- kana zuwa gaban malami
domin daukar karatu?
35-ka tabbatar abinda kake ci halal
ne?
36- kana kuwa damuwa da halin
da yan uwanka musulmi suke ciki?
37- kana taimaka marayu kuwa?
38- salati nawa kake yiwa Annabi
saw kullum?
39- Istigfari nawa kakeyi kullum?
40- kana zuwa makabarta domin
tuna lahira?
41- kana zuwa taaziyya da sallar
Jana’iza?
42- ka taba yin kuka saboda tsoran
Allah?
43- shin kana yiwa dukkan
musulmi sallama ko kuwa sai
wanda ka sani?
44- kanayin rantsuwa akan karya
kuwa?
45- kana shan taba ko wiwi ko giya
ko hodar iblis?
46- kana jin kade- kade, da wake-
wake?
47- kana aske gemunka?
48- ka taba karbar cin hanci?
49- kana kyautawa iyalanka?
50- kana gaba da wani kuwa?

Advertisements

44 thoughts on “KASAN KANKA DA KANKA ( TAMBAYOYI 50)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

 1. Salam malam menene hukanci mai saurin bacin rai da kuma fishi sanan kuma bashida hakuri daga aliyu unguwa uku matsula layin dan jos

 2. Allah gafarta malam, menene hukuncin wanda yake gyaran girar idanu, ba wai ya aske ta gaba daya ba, yayi mata gyara ne, kamar gyaran fuska. Na gode

 3. Assalamu Alaikum.mallam danAllah ina da tambaya wai ko ya halarta idan mutum.na neman biyan bukata ya zubarda jinin dabba duk dan Allah ya biya masa bukatar sa

 4. assalamu alaiku Allah yasakama Mal da alkairi amen Mal tanbayata ananshine Mal zan iya takar yarinyar da zan aura innabiya sadaki kafin adauramana aure
  wassalam Mal ahuta lfy

 5. ALLAH YA SAKAWA DUK WANDA YA BA DA GUDUMMAWA WAJEN ILMANTAR DA AL’UMMAR MUSULMI TA WANNAN SASHIN SADARWAR DA ALHERI.

  • SALAM, malam, name taba sakin mata sau biyu sai tayi aure har ta haihu a wajen wani ya fito ta dawo hannu name muka sake rabuwa. ko zamu sake daura aure? Allah ya taimaki malam.

 6. Allah ya sakawa malam da alkhairi malam meye hukuncin mai zinar hannu kuma wani hanya zai bi ya kubuta! daga alameen mai littafi

 7. Assalamu alaikum, Malan Allah ya sakamaka da alkhairi ya sanya aljanna ce sakamakonka, kuma ya sa ka kara jajircewa wajen fadakar da yan uwa musulmai Allah ya karamaka ilmi da Taqwa da wadata. AMEEN

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s