SUNA NA GARI LAMIRI(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)


Suna yana da mahaimmanci a
rayuwar mutum, wannan yasa
sharia tayi umarni da asa suna mai
kyau mai maana, domin suna,
yana tasiri, akan mutum, ko gari ko
kasa ko Kabila, ko Unguwa, wajan
alkhari, ko sharri,
Abu Dauda ya ruwaito, Manzon
Allah saw, ya canga sunaye
kamar : Al’as, Aziz,
Atalata,Shedan, Alhakam,
Gurab,hubab. Ya canga Shihab ya
sa masa Hisham, Harbu ya sa
masa Salmu, ya sawa, Al’mudaji’u,
Almunbaisu, wata kasa ana kiranta
afiratu, ya sa mata suna khadiratu,
akwai wata unguwa mai suna,
shiibullalati, zuwa Shiibul huda,
akwai wata kabila mai suna Banuz-
Zina zuwa Banur-rishidati, banu
Mugwiyati zuwa banu,rishida,
( Sunanu Abi Dauda babin canga
mummunan suna 3- 217)
Sunaye da baa sawa mutum, sun
kasu kashi shida
1- Sunan daya kebanta da Allah,
kamar Allahu, Al’kaliq,
2- Sunayan shedan kamar Iblis,
Shedan,
3- sunayan manyan kafurai wanda
sukayi fice dashi, kamar Karuna
Hamana, Fir’auna
4- Sunaye masu nuna tashin
hankali, kamar Fitina, Gobara,
Hatsari, Bala’i, Musifa,
5- Sunayn da basu da Maana, ko
fassara mai kyau
6- irin sunayan da matasa suke
sawa kansu, na mawaka, ko yan
kwallo, ko wasu fajirai.
A wannan zamani, akwai jahilci,
kwarai gamai da sunayan da ake
sawa yara, ana lura ne kawai da
dadin suna a baki, amma idan anyi
binciki sai kaga sunan wani naman
dawa ne, ko wani abu mai cutarwa,
don haka wajibi a kula sunan da
zaa sa ya cika wadannan ka’idoji :
1- Sunayan da suke nuna bauta ga
Allah, Kamar Abdullah,
Abdurrahman, Abdurrahim
2- Sunayan Annabawa, Kamar
Muhammad, Ahmad, Ibrahim,
Musa, Isah, Haruna, Idris, Yusuf,
3- Sunayan Sahabbai, Abubakar,
Umar, Usman, Aliyyu, Mus’ab,
Anas,
4- sunaye masu Ma’ana, na
alkhairi, da Albarka, kamar ,
lubabatu, Lubnah, sakina, Husna,
ya kamata kafin asa suna adinka
bincike akan ma’anarsa.

Advertisements

3 thoughts on “SUNA NA GARI LAMIRI(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s