ME YA FARU A KARBALA 30(Dr. Mansur Sokoto)


Halin Da Ake Ciki A Makka
Rundunar Husain bn Numair
wacce take tsare da Ibnuz Zubair
da jama’arsa suna can suna dako
a wajen birnin Makka, ba su samu
labarin mutuwar sarki Yazidu ba
sai bayan sati 3 cur. Abu kadan ya
rage wannan runduna ta hada kai
da Ibnuz Zubair bayan da suka
samu wannan labari. Amma
abinda ya kawo cikas shine, bin
Numair ya nemi ya dora hannunsa
a kan na Ibnuz Zubair ya yi masa
caffa amma da sharadin su yafe
duk jinainan da suka gudana a
baya; a zauna lafiya. Shi kuma
Ibnuz Zubair (R.A) sai ya ki
amincewa da wannan sharadi. A
nan ne bin Numair ya juya yana
nadama, ya ce, “Dubi yadda nake
kiran sa zuwa sarauta yana neman
ci gaba da fitina”. Ashe dai Allah
bai nufe shi da zama sarki na
hakikani ba.
A birnin Dimashka an sha
takaddama sosai bayan mutuwar
Yazid a kan wa zai gaje shi tunda
shi bai bar wasici ba. Daga bisani
dai aka nasa dansa Mu’awiya
karami. Amma ina dadin mulki a
lokacin tashin hankali? Ba da
jimawa ba shi kuma ya yi murabus
ya bar karagar sarauta wayam ba
mai bukata. A nan ne Umawiyyawa
suka bukaci su je su sasanta da
Ibnuz Zubair suyi ma sa mubaya’a
a Makka. Kuma sai dai
madaukakin sarki ya hukunta
nadin Marwan bin al-Hakam bayan
sun jitu a kan sa. Shine kuma
wanda sarautar ta ci gaba daga
bisani a cikin zuriyarsa.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s