ALKAKI DA RUWAN ZUMA2(Dr. Mansur Sokoto)


ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Sayyadi
Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wa Ala
Alihi Wasallam 2
Matsayin Wannan Tarihi
Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya fifita
tarihin ma’aikinsa a kan na sauran ‘yan
adam da duniya take ji da su.
1. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam shi kadai ne wanda aka
haifa a cikin hasken rana, kamar yadda
wani bature yake cewa. Abin nufi,
babu wani abin da zaka so ka sani
game da rayuwarsa wanda ma’abotansa
ba su sanar da mu ba. Tun daga
rayuwarsa ta cikin gida har
zamantakewarsa da masoyansa da
magabta. Kai, har abinda mutane ke
boyewa na sirrin rayuwarsu, shi
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam an bayyana nasa
domin shi abin koyi ne ga musulmi fai
da boye.
Dubi yadda aka sifaita mana jikinsa
kamar kana zaune a gabansa. Hatta da
farin gashin da yake a gemunsa an
qirge mana yawansa. Motsinsa kowane
iri an bayyana shi a cikin tarihinsa. Tun
daga yadda yake zama da tafiya da cin
abinci da sa sutura da kawaici da
magana da komai da komai. Dubi “As-
Shama’il Al-Muhammadiyyah” na
Imam Abu Isa At-Tirmidhi ko kuma
“Zad Al-Ma’ad” na Ibnul Qayyim
misali ba abin da ba zaka gani ba
wanda ya danganci nasa salo na
rayuwa wanda shi ne samfurin rayuwar
da Allah yake so bani Adama su koya.
Tambayi mabiyan annabi Isah (AS) me
suka sani game da rayuwarsa?
Ballantana duk sauran addinai irin na
gargajiya da makamantansu!
2. Sai kuma ingancin da kaffatanin
wannan tarihi yake da shi. Saboda
babu na-ji-na-ji a cikinsa. Kome aka
fada an san wanda ya cirato shi kuma
ta ina ya cirato shi. Don haka in ka ga
ana rigima kan wata magana da ta
danganci rayuwar Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam
to, ma’abota sani ne ba su zo ba. Yanzu
suna fayyace maka kowace ruwaya da
matsayinta.
3. Ga shi kuma wannan tarihi ya cika
ya batse ta kowace fuska. Rayuwar
kowa akwai a cikinsa. Karamin yaro,
maraya, matashi, dattijo, maigida,
talaka, malami, mai sarauta, dan
kasuwa, jagora, soja, farar hula,
liman.. Kai har da dan gudun hijira bai
rasa abin koyi a cikin wannan
tsarkakakken tarihi.
4. Tsaftataccen tarihi ne da ba abin
yasuwa a cikin sa. Ko sau daya ba zaka
ji wani sharri ko zalunci ko duk wani
abinda lafiyayyen hankali yake kyama
ba a cikin sa. Rayuwa ce ta wanda
Allah ya aiko shi don ya zama rahama
ga talikai. Dubi duk kaifin adawar
mutanen Makka, kai har da
algungumai Yahudawan da suka yi
makwautaka da shi a Madina. Ka taba
jin wanda ya tuhumce shi da wata
magana ko aiki mai zubar da mutunci?
5. Tare da haka kuma wannan rayuwa
ce mai saukin koyi. Ba ta wuce iya
ikon dan adam da aka halicce shi a kai
ba. In ban da mu’ujizoji – kamar Isra’i
da Mi’iraji – mene ne dan adam ba zai
iya kwaikwayon Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam
ba a cikin sa?

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s