ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)


ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa ta 15
Sunansa da Asalinsa:
Cikakken sunan manzonmu shi ne
MUHAMMAD
(Ma’anarsa: abin godewa. Ba a taba jin
wannan suna ba gabanin sa. Wannan
suna yana da rassa. Su ne; Mahmood
da Haamid da Humaid da Hamdaan).
Dan ABDULLAHI
Dan ABDULMUTTALIB
(Sunansa na yanka shi ne SHAIBA. Za
mu fadi dalilin kiran sa
Abdulmuttalib).
Dan HASHIM
(Sunansa na yanka AMRU).
Dan ABDUMANAF
(Sunansa na yanka MUGHIRA).
Dan QUSAYYU
(Ana kuma ce ma sa ZAIDU. Shi ne
ya gina Mash’arul Haram a Muzdalifa
in da alhazai ke taruwa in an sauko
Arafat domin hutawa da ambaton
Allah.
Duba: An-Nasab Wal Musahara, na
Ala’uddin Al-Mudarris, bugun
Mu’assat Al-Mukhtar, Alqahira, 2005,
shafi na 59.
Dan KILABU
(Sunansa na yanka shi ne HAKEEM
ko kuma URWA, amma lakabinsa ya
rinjaye shi. An kira shi Kilab ne
saboda yana zuwa farauta da karnuka).
Dan MURRATA Dan KA’ABU
(Ana ce ma KA’ABU Abu Husais.
Yana daga cikin manyan mutane da
larabawa ke bugun gaba da su. Shi ne
ya fara hada jama’a ranar jum’ah. A
lokacin suna kiran ta “Yaumul Aruba”;
ranar larabawa).
Dan LU’AYYU Dan GALIBU Dan
FIHRU
(Shi ne QURAISH wanda ake jingina
kabilar gaba dayanta zuwa gare shi.
Shi ne kuma ya ci galaba a kan wani
barde da ake kira Hassan Al-Himyari a
lokacin da ya zo da niyyar ya kwashe
duwatsun Ka’aba don ya mayar da su
Yemen. Wasu kuma suka ce asalin
wannan sunan na wani mahaukacin kifi
ne da ya tare ayarin larabawa suna
tafiya a cikin jirgin ruwa, saman teku.
Sai mutane suka firgita matuka a
kansa. Ba tare da bata lokaci ba
wannan sadauki daga cikin kakannin
fiyayyen halitta ya fitar da mashi ya
kifa ma sa. Cikin ikon Allah sai kibiyar
ta kafe kifin. Da jirgi ya kusanto wurin
da Quraishu yake kafe ba tare da tsoro
ba Bayajidan larabawa ya sa takobi ya
farke cikinsa, ya kuma gutsure kansa.
Sannan ya nemi taimakon jama’a aka
shigar da namansa a jirgi suka isa da
shi Makka. Daga nan ne aka sa ma sa
wannan suna Quraish; sunan kifin da
ya hallaka wanda ya tashi hallaka
ayarinsu.
Duba: Subhul A’asha na Qalqashandi
(1/352) da kuma Ayyamul Arab Fil
Jahiliyya, na Muhammad Jad Al-
Maula.
Sunan baban Quraish: MALIK Dan
NADHRU
(Sunan Nadhru na yanka: QAIS).
Dan KINANATA Dan
KHUZAIMATA Dan MUDRIKATA
(Sunansa na yanka AMIR).
Dan ILYAS
(Shi ne mutum na farko da ya fara
hadaya; sadaukar da dabba a yanka ta
don girmama dakin Allah).
Dan MUDHAR
(Mutum ne mai kyakkyawar murya
wanda shi ya fara “Hida’u” irin shewar
da ake ma rakuma don su samu kuzarin
tafiya).
Dan NAZAR Dan MA’AD
(Gwarzo ne, sadauki; da ba a taba kada
shi wurin yaki ba).
Dan ADNAN
(Adnan shi ne kaka na 20 ga manzon
Allah (S). Kuma iyakacin abinda ake
da tabbacinsa kenan dangane da
nasabarsa. Amma an tabbata cewa, shi
Adnan jika ne ga annabi Isma’il dan
annabi Ibrahim Alaihimas Salam. An
kuma ce Isma’il (AS) shi ne kakan
Adnan na 38. Shi kuma Isma’il shi ne
jikan annabi Nuhu na 11. Idan muka
lisafta zamu ga tsakanin manzon Allah
(S) da annabi Nuhu (AS) akwai
kakanni 70 cif har da mutum 3 kenan.
Amma fa inganci da tabbaci yana ga
iyaye 20 na farko da muka fada daga
mahaifinsa Abdullahi zuwa Adnan. Ar-
Rahiq Al-Makhtum, shafi na 57-58.
Zamu yi sharhi a kan wannan nasaba
tsarkakakkiya in Allah ya so.
Ku dakace mu.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s