Mafita Ga Musulmai


Duk matsalar da musulmai suke ciki yau. Ba laifin kowa sai laifin kawunansu. Allah baya zaluntar bawansa komai, sai dai bawan ya zalunce kansa.. Allah(subhanahu wata’ala) yace:

ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﺎ ﻳﻈﻠﻢ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺷﻴﺌﺎ ﻭﻟﻜﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ
ﺃﻧﻔﺴﻬﻢ ﻳﻈﻠﻤﻮﻥ.
Lalle ne Allah ba Ya zãluntar
mutãne da kõme, amma mutãnen
ne ke zãluntar kansu.

Saboda haka in Mutane suna zama cikin jin dadi da nishadi, sai suka saba masa suka ki bin dokokinsa, toh hakika sai Allah ya jarrabesu…..

ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﺎ ﻳﻐﻴﺮ ﻣﺎ ﺑﻘﻮﻡ ﺣﺘﻰ
ﻳﻐﻴﺮﻭﺍ ﻣﺎ ﺑﺄﻧﻔﺴﻬﻢ
Lalle ne Allah bã Ya canja abin da
yake ga mutãne sai sun canja abin
da yake ga zukatansu.

Saboda haka ‘yan’uwa hanya dayace tak zata kaimu ga fita daga cikin wannan matsasi da wahala. Hanyar kuwa itace ‘Bin Tafarkin magabatanmu salihai na farko, ta yadda suka sami izza a lokacin da Duniyar kafurci take Kewaye dasu, toh muma haka zamubi mu sami izza in mukabi tafarkin yadda suka bi. ‘Muyi riko da dokar Allah, sannan mu kaurace wa Zunubai manya da kanana. Sannan kuma muso juna.

Allah yasa mudace ya yaye mana duk wata matsalolinmu…

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s