ALKAKI DA RUWAN ZUMA36( Dr. Mansur Sokoto)


Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da
Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi
Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala
Alihi Wasallam
Fitowa Ta 36
Daga Cikin Fifikonsa
4. Darajar Sahabbansa (kashi na
biyu)
Akwai wasu abubuwan da sahabban
manzon Allah suka kebanta da su da
suka fifita su a kan sauran musulmi
da ke bayan su:
1. Zamantakewarsu da manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam da ganin
mu’ujizoji da karamomin da Allah da
darajanta shi da su ya sanya ma su
tsarkin zuciya game da son Allah da
manzonsa. Duba a Suratun Nisa’i
yadda Allah yake ba da shedar
kyakkyawar niyyar da suke da ita
wurin jihadi. Allah ya ce:
(( ﻭَﻻ ﺗَﻬِﻨُﻮﺍ ﻓِﻲ ﺍﺑْﺘِﻐَﺎﺀِ ﺍﻟْﻘَﻮْﻡِ ﺇِﻥْ ﺗَﻜُﻮﻧُﻮﺍ ﺗَﺄْﻟَﻤُﻮﻥَ
ﻓَﺈِﻧَّﻬُﻢْ ﻳَﺄْﻟَﻤُﻮﻥَ ﻛَﻤَﺎ ﺗَﺄْﻟَﻤُﻮﻥَ ﻭَﺗَﺮْﺟُﻮﻥَ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻣَﺎ ﻻ
ﻳَﺮْﺟُﻮﻥَ ﻭَﻛَﺎﻥَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠِﻴﻤًﺎ ﺣَﻜِﻴﻤًﺎ ( ( ]ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ 104: ]
Ma’ana: “Kuma kada ku yi rauni
wajen neman mutanen (kafirai). Idan
har kuna jin zafi to, su ma fa suna jin
sa kamar yadda kuke ji, sa’annan
kuna da wata fata daga Allah wacce
su ba su da ita”. Suratun Nisa’i: 104.
A Suratul Fath, madaukakin sarki ya
ba da irin wannan sheda in da yake
cewa:
(( ﻟﻘﺪ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺇﺫ ﻳﺒﺎﻳﻌﻮﻧﻚ ﺗﺤﺖ
ﺍﻟﺸﺠﺮﺓ ﻓﻌﻠﻢ ﻣﺎ ﻗﻠﻮﺑﻬﻢ ﻓﺄﻧﺰﻝ ﺍﻟﺴﻜﻴﻨﺔ ﻋﻠﻴﻬﻢ
ﻭﺃﺛﺎﺑﻬﻢ ﻓﺘﺤﺎ ﻗﺮﻳﺒﺎ ))
Ma’ana: “Hakika, Allah ya yarda da
mummunai a lokacin da suke yi maka
mubaya’a a karkashin bishiyar nan,
sai ya dubi abin da ke cikin
zukatansu sai ya saukar ma su da
natsuwa kima ya saka ma su da budi
kusa kusa”. Suratul Fath:18. Duba
kuma Suratu Ali Imran: 154
Ka ga a nan ga yardar da Allah ya yi
da su, ga kuma shedar gaskiyar
imanin da ke cikin zukatansu.
2. Suna da gaggawa wajen bin
umurnin Allah da manzonsa da kai
matuka wajen ibada tare da yin ta
bisa koyarwar manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam.
Misali, a cikin yan kalilan shekaru ne
suka karbi canjin da manzo ya zo ma
su da shi daga ilahirin al’adun da
suka gada daga iyaye da kakanni, sai
suka koma wata al’umma daban bisa
samfurin dan adam da Allah yake so.
Kuma a cikin shekaru 10 kacal suka
yi jihadi da yada da’awar musulunci
suka ci nasarorin da a shekaru 100
aikin yana da wuya in ba don
karfafawar Allah da taimakonsa a
gare su ba. Don haka ne madaukakin
sarki yake cewa:
(( ﻟﻜﻦ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻣﻌﻪ ﺟﺎﻫﺪﻭﺍ ﺑﺄﻣﻮﺍﻟﻬﻢ
ﻭﺃﻧﻔﺴﻬﻢ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺃﻭﻟﺌﻚ ﻟﻬﻢ ﺍﻟﺨﻴﺮﺍﺕ
ﻭﺃﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ ﺍﻟﻤﻔﻠﺤﻮﻥ * ﺃﻋﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻬﻢ ﺟﻨﺎﺕ ﺗﺠﺮﻱ
ﻣﻦ ﺗﺤﺘﻬﺎ ﺍﻷﻧﻬﺎﺭ ﺧﺎﻟﺪﻳﻦ ﻓﻴﻬﺎ، ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻔﻮﺯ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ (
( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ : ٨٨- ٨٩
3. Ga su da cikakkiyar fahimtar
musulunci bisa karantarwar manzon
Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Don
haka, ba su faifayewa ba su kasawa.
Shi ya sa Allah ya ce ma Ahlulkitabi,
“Idan sun yi imani da irin abin da
kuka yi imani da shi to fa sun
shiriya”. Suratul Baqarah: 137. Ashe
imaninsu ma shi ne samfurin imanin
da Allah ya amince da shi. Ba
mamaki, sahabbai ba su yi bidi’a ba.
Duk bidi’oi sun bayyana ne a karshen
zamaninsu kuma sune suka yi fada
da su, suka kare sunnar da baban
Qasim ya bar su a kan ta.
4. Suna sadaukar da duk abin da
suka mallaka tun daga kudi har
lokaci da karfin jiki zuwa jininsu da
rayuwarsu don daukakar addini. Dubi
irin yabon da Allah ya yi ma su a
cikin Suratul Hashr: 8-10 bayan ya
kasa su kashi biyu; Muhajiruna da
Ansar. Ya yabi wadancan a kan
hijirarsu da hakuri a kan cutar
mushrikai da tsarkin zukatansu wajen
neman yardar Allah. Su kuma
wadannan ya yabe su da taimakon
Allah da manzo da karbar bakuncin
‘yan uwansu muhajirai da kaunar su
da karrama su da fifita su a kan
kawunansu. Sannan ya sifaita
wadancan da “masu gaskiya”,
wadannan kuma da “masu rabauta”.
A Suratut Taubah: 100 kuma sai
Allah ya shelanta cewa, ya yarda da
su duka kuma sun yarda da shi.
A ranar da sayyidi Umar bn Khattabi
ya musulunta, adadin sahabbai ya
cika 40 cif, sai Allah ya ce ma
manzonsa:
(( ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲُّ ﺣَﺴْﺒُﻚَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻭَﻣَﻦِ ﺍﺗَّﺒَﻌَﻚَ ﻣِﻦَ
ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ ( ( ] ﺍﻷﻧﻔﺎﻝ 64: ]
“Ya kai annabi! Allah ya ishe ka,
kuma wadanda suka bi ka daga cikin
mummunai sun ishe ka” Suratul
Anfal: 64.
5. Ga su da kyawawan dabi’u da
suka koya daga manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam. Don haka
suka fi kowa adalci da karimci da
gaskiya da jarunta da rikon amana.
Ita kam karya ba a san ta ba ma sam,
sai bayan zamaninsu. Domin ko kafin
su musulunta babban abin kunya ce
a wurin su kamar yadda muka gani a
can baya. Ba mamaki a samu daya
ko biyu daga cikinsu Shedan ya
samu sa’ar su sun yi karya sannan
suka tuba. Amma ba dabi’arsu ce ba.
Ba ka ji Allah ya yabe su ba da cewa:
(( ﺃﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ ﺍﻟﺼﺎﺩﻗﻮﻥ ))
“Wadancan su ne masu gaskiya”
Suratul Hujurat: 15 da Suratul Hashr:
8. Don haka, gaskiya ita ce siffarsu
ba karya ba.
Da wadannan kyawawan dabi’iun ne,
gami da jihadi da son Allah da manzo
suka zamo “mafificiyar al’ummar da
aka fitar ma mutane” kamar yadda
Allah ya fade su a Suratu Ali imran:
110.
Ku biyo mu don jin wasu daga cikin
darajojin da Allah ya kebanci wasu
daidaikunsu da su.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s