Auren Mutu’a Haramun Ne Har Zuwa Ranar Alkiya(Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)


Auren Mutu’a Haramun Ne Har Zuwa Ranar Alkiya (Martani Ga Nuraddeen)
Da farko dai ban yi mamakin yadda mal Nura ya bi hujjojin da na kawo, ya yi musu diban karan mahaukaciya ba, saboda dama wannan ce dabi’ar ‘yan shi’a, lauya magana da kawar da kai ga abin yake a fili.
Da farko dai mal Nura ya ce, ” Malam Muhammad Rabi’u ya kawo Aya daga cikin Al-qur’ani maigirma: “Illaa alaa azwaajihim ………” (Al-mu’minuun: 6, da Al-ma’aarij: 30). Sai duk a ciki ba bu inda Allah maxaukakin Sarki ya nuna a cikin Ayar Mut’ah haram ne. Haka nan ba muga inda shi Malam M. Rabi’u ya gano wannan tafsirin daga Malaman Tafsiri da suka nuna wannan ayar ta sauka ne akan hana auren mut’ah ba. Da zai fi kyau ya kawo mana inda Malamai suka ce wannan ayar tana nuni ne akan haramcin Mut’ah”. Haka ya ce, amsa : Duk da na yi bayani a baya, amma a yanzu zan cewa Mal Nura kayanka sun tsinke gindin kaba, inda na gano wannan tafsiri shi ne fadin wani malamin shi’a Alkadi Abu Hanifa Annu’uman bin Muhammad, inda yake cewa “Batancin auren mut’a yana nan a cikin littafin Allah, saboda Allah (S.T.W) yana cewa – sai ya kawo wannan ayar da na kawo, sannan ya ci gaba da cewa – “Allah bai saki kalmar aure ba sai akan mata ko baiwa, sannan ya ambaci saki wanda da shi ne rabuwa tsakanin ma’aurata take wajaba, ya sanya gado tsakanin ma’aurata, sashensu ga sashe, ya wajabta idda akan wadanda aka saki, auren mut’a kuwa ya saba da haka” (Duba “Da’a’imul Islam 2/229). Ga inda na gano tafsirina, a wurin malaminku na shi’a, ba na wahabiyawa ba!. Yanzu raddi ya rage tsakaninka da shi.
Amma maganar Mal Nuraddeen ta cewa ” to ai duk duniya an yi ittifaqi akan Mut’ah aure ne” ban san meye ma’anar ittifaki a wajensa ba, idan yana nufin duk duniya an hadu akan mut’a aure ne, to wannan ya nuna bai san me yake fada ba, domin kuwa da an yi wannan ittifakin da yake fada, da babu bukatar wannan tattaunawar!, ko kuwa yana ganin dimbin musulman duniya, na da, da yanzu da suka tafi a kan auren mut’a haramun ne, su ba sa cikin wadanda suke musulmai ko malamai ko mutanen duniya, ko kuwa aljannu ne. A dai rika dubawa kafin a yi magana!!.
Mal Nura ya ce, ” Domin har yanzu ba bu wata aya da ta shafe hukunci da umarnin da Ubangiji ya yi akan yin auren mutu’a, inda Allah ya ke ce wa: “Famas-tamta’tum bihi minhunna fa’aatuuhunna ujuurahunna fariidhah”, ma’ana: “Kuma matayen da ku ka yi mutu’a da su, wajibi ne ku ba su sadakinsu”. Amma shi Malam Rabi’u saboda ta’assubanci sai ya zo yana fassara “Ujuur” da wai Haya, wanda “Ujuur” jam’ine na “Ajr” kuma ma’anar Kalmar shi ne: “Lada”, ba kamar yadda shi wanna bawan Allahn ya fassara ba”. Da farko dai wannan aya da mal Nura ya kawo ba auren mut’a take nufi ba kaulan wahidan, kuma saboda dogayen bayanan da suke tattare da ita zai fi kyau a ware mata lokaci don tattaunawa a kanta. Amma maganar Mal Nura cewa na fassara “Ujuur” da haya, wannan kire ne da kage gare ni, domin shi kansa ya sani, ni ba dan dagajin larabci ba ne da zan fassara “ujuur” da haya, kurum dai kage ne irin na yan shi’a, yadda abun ya zo a rubutana, don mai karatu ya ga a ina ne na fassara “ujuur” da haya. Ga abin da na ce, “kamar yadda su kansu masu mut’ar suka nuna a littattafansu, saboda ba sa kiranta (Zauj), kamar yadda ba sa bada hakkokin matan aure ingantacce na din–din–din, sun bambanta ta da abubuwa ashirin daga matar aure na din–din–din, ga wasu daga cikin bambance–bambancen da suka fada a littafansu.(A) Matar mut’a matar haya ce : An karbo daga Ubaid dan zurara, daga Abu Abdullahi Ja’afar Assadik yana cewa : “Ka auri dubu daga cikinsu, domin su matan haya ne”. haka nan an karbo daga Abu abdullahi ya ce : “Ai ba ta cikin hudun nan, ita matar haya ce” Duba littafin shi’a “Wasa’ilil Shi’a” j 14 sh 446.
Anan mai karatu zai ga cewa kalmar haya ta zo ne a cikin maganar Abu Abdullahi Ja’afar Assadik, da na hakaito, ba waccan ayar nake fassarawa ba!. Ga yadda maganar ta zo in ya so ya fassara min!.
فعن عبيد الله بن زرارة عن أبي عبد الله – أي جعفر الصادق – أنه قال : تزوج منهن ألفا فإنهن مستأجرات”
وعن عبد السلام عن أبي عبد الله قال : “ليست من الأربع إنما هي “إجارة”.
Wadannan su ne nassosin da na fassara su a waccan makala, amma saboda Mal Nura ba zai iya kare su da hujja ba, sai ya tafi ya harhada wata magana daban ya ce haka na ce! Ya shiga siffata ni da ta’assubanci, to kai kuma fa, dame zan siffata ka!. Ni dai bukata a nan mutane su sani, matar mut’a matar haya ce, in ji a’immar shi’a. Maganar “ujuur” a waccan aya kuwa, sadaki ake nufi ya mal Nura!, ba lada ba irin wadda kuke bayarwa ba idan zaku yi mut’a ba. Ka nemi sani in an gama wannan dagar a fada maka.
Mal Nura ya ce, ” Sannan daga cikin Malaman Ahlus-sunnan da suka tabbatar da wannan ayar ta sauka ne akan halascin Auren Mutu’a akwai: Malam Ahmad bn Hanbali a Musnadinsa, hakanan ma Malam Abubakar Al-Jassas cikin Al-Ahkamul-Qur’an, da Malam Abubakar Al-Baihaqiy cikin Sunanul-Kubrah, da Malam Al-Qaadiy Al-Baidaawiy a Tafsirinsa, da Malam Ibn Kathiir a nasa Tafsirin, da Malam Jalaaluddin Siyuuxiy a Durrul-Manthur, da Malam Al-Qaadiy Ashshaukani a Tafsirinsa, da Malam Shihaabuddiin Aluusi a Tafsirinsa, da Sanaduddukan da suke qarewa da irinsu Ibn Abbas, da Ubayyu xan Ka’abu, da Abdullahi xan Mas’ud, da Imrana xan Hasiinu, da Habibu xan Abi Thaabit, da Sa’idu xan Jubair, da Qutaadatah, da Mujahid”.
Allah sarki, wai ahlus-sunnah zai ruda da irin wadannan maganganu, to anan me yasa baka hakaito maganganunsa ba, ai sai ka ce, sun ce kaza, wane ya ce kaza, mu kuma daliban ilimi sai mu koma mu ga shin abin nan da ka fada gaskiya ne, ko kuwa ka yi halin naku “Takiyya = karya”. Kuma shi ne abin da ya faru a nan din kuwa, da farko dai malamai abin da suke yi, shi ne in sun zo tafsirin waccan ayar sukan kawo maganganun malamai a wajen fassararta, daga ciki sukan hakaito cewa “wasu sun ce ta sauka ne akan auren mut’a”, haka suke cewa, sai ‘yan shi’a irin su Mal Nura su ki fadin hakikanin abin da malami ya fada sai su ce, ya ce, ayar ta sauka ne akan auren mut’a kawai”. yanzu bari mu duba biyu daga cikin malaman can da ya ce sun ce wannan ayar ta sauka ne akan halascin mut’a”. Ibnu kathir ga abin da ya ce,
فَمَا اسْتَمْتَعْتُمْ بِهِ مِنْهُنَّ فَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةً} أي كما تستمتعون بهن فآتوهن مهورهن في مقابلة ذلك، كما قال تعالى: {وَكَيْفَ تَأْخُذُونَهُ وَقَدْ أَفْضَى بَعْضُكُمْ إِلَى بَعْضٍ} وكقوله تعالى: {وَآتُوا النِّسَاءَ صَدُقَاتِهِنَّ نِحْلَةً}، وكقوله: {وَلا يَحِلُّ لَكُمْ أَنْ تَأْخُذُوا مِمَّا آتَيْتُمُوهُنَّ شَيْئاً } وقد استدل بعموم هذه الآية على نكاح المتعة، ولا شك أنه كان مشروعاً في ابتداء الإسلام، ثم نسخ بعد ذلك، وقد ذهب الشافعي وطائفة من العلماء إلى أنه أبيح ثم نسخ مرتين. وقال آخرون: أكثر من ذلك. وقال آخرون: إنما أبيح مرة ثم نسخ مرة، ثم نسخ، ولم يبح بعد ذلك. وقد روي عن ابن عباس وطائفة من الصحابة القول بإباحتها للضرورة، وهو وراية عن الإمام أحمد، وكان ابن عباس وأبي بن كعب وسعيد بن جبير والسدي يقرؤون {فَمَا اسْتَمْتَعْتُمْ بِهِ مِنْهُنَّ إِلَى أَجَلٍ مُسَمّىً فَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةً} ، وقال مجاهد: نزلت في نكاح المتعة، ولكن الجمهور على خلاف ذلك. والعمدة ما ثبت في الصحيحين عن أمير المؤمنين علي بن أبي طالب، قال: نهى رسول الله صلى الله عليه وسلم عن نكاح المتعة، وعن لحوم الحمر الأهلية يوم خيبر. تفسير ابن كثير / دار الفكر – (1 / 586).
Yanzu don Allah duk mai hankalin da ya karanta wannan bayani na Mal Ibnu Kathir ya zo ya ce, shi ma ya ce ayar ta sauka a kan halascin mut’a kawai. A ji tsoron Allah Mal Nura, ku daina yi wa almajiranku karya don kun ga basa karatu!. To kamar yadda Ibnu kathir din nan ya kawo duk sauran malamai haka suka kawo, kuma sukan kawo maganar Mut’a ne a magana ta biyu da sigatut “Tamrid” Allah ya sa kasan sigatut “Tamrid”!!. Ga misali na biyu Al-imamul Baidawiy, ga abin da ya ce,
فما استمتعتم به منهن ( فمن تمتعتم به من المنكوحات أو فما استمتعتم به منهن من جماع أو عقد عليهن ) فآتوهن أجورهن ( مهورهن فإن المهر في مقابلة الاستمتاع ) فريضة ( حال من الأجور بمعنى مفروضة أو صفة مصدر محذوف أي إيتاء مفروضا أو مصدر مؤكد ) ولا جناح عليكم فيما تراضيتم به من بعد الفريضة ( فيما يزاد على المسمى أو يحط عنه بالتراضي أو فيما تراضيا به من نفقة أو مقام أو فراق وقيل نزلت الآية في المتعة التي كانت ثلاثة أيام حين فتحت مكة ثم نسخت. (تفسير البيضاوي 2/171).
Allah ya kiyashe mu da son rai!. Wani abin sha’awa ma hatta wasu daga malaman shi’a ma haka suka yi a tafsirinsu. Addabarsi ya ce a cikin tafsirinsa (Majma’ul Bayan 5/71) – bayan ya hakaito maganar cewa ayar tana nufin auren dindindin, sai ya ce : “kuma an ce tana nufin auren mut’a…wannan shi ne ra’ayinmu Al-imamiyya”. Ka ga anan ya kawo magana biyu a kan ayar, ya gabatar da maganar auren dindindin, sannan ya yi maganar mut’a da cewa “An ce” haka nan Dusi ya yi a cikin tafsirinsa “Attibyan 3/165” ya kawo duka magannun biyun. Don haka maganar wannan aya ta surar Nisa’i tana nufin mut’a ne kai tsaye, magana ce sabanin abin da mafi yawancin malamai suka tafi a kai, a je a yi karatu sosai Sheikh Nura!.
Sannan Mal Nura ya ce, “DOMIN ABIN LURA ANAN SHINE, SU WAXANNAN AYOYIN GUDA BIYU SUN SAUKA NE A MAKKA, ITA KUWA AYAR DAKE MAGANA KAN MUTU’A TA SAUKA NE A MADINA. KUMA ABIN DA YA RIGA SAUKA BAYA SHAFE WANDA YA ZO DAGA BAYA”. Amsa : wannan magana ce da ta ginu ne akan wancan ra’ayi mai rauni, wanda yake ganin ayar ta sauka ne don bayanin auren mut’a, don haka dole ne ya ce an shafe ta, amma wanda dama yake ganin ayar ba tana magana ba ne akan auren mut’a ba, to baya bukatar ya ce daya ta shafe daya, dukkaninsu suna nan suna aiki.
Mal Nura ya ce ” Haka nan dai a cikin wannan bayanin nasa na xaya Malamin ya ce: “saboda ba sa kiranta (Zauj)” to ai wannan kalma ma ta yaya mu Shii’ah za mu kirawo Mutu’a da “Zauj” [زَوْج], ai wannan ba ta ba da wata ma’ana ta hankali ba, domin ma’anar “Zauj” shi ne “Miji”?!.
Amsa : Karamin sani kukumi ne, wa ya ce maka kalmar “Zauj” bata nufin mata, sai miji, a’a kalmar “zauj” Mal Nura tana nufin mata ko miji, a larabci, kusan ma alkur’ani yana amfani ne da kalmar “Zauj” a kan mata. A kara dubawa Ya Sheikh Nura! Don haka “zauj” da na fada mata nake nufi ba aure ba!.
Mal Nura ya ci gaba da cewa, ” hattana Malamanku suna kiran Mutu’a ne da Aure, ka iya dubawa cikin Sahiih Muslim, babi guda mawallafin littafin ya yi ya sa masa suna: “Baab Nikaahul-mut’ati”, wanda ka duba duk qaamus xin duniyar nan “Nikaahu” ma’anarsu xaya da “Zawaaj” kuma duka suna nufin Aure ne!”
Amsa : Allah sarki, kiran mut’a da nikahu ko zawaj, wannan baya nuna halascinta, isdilahi ne na malamai, me zaka ce akan fadin malamai “Bai’ul Ina” Bai’un Najash” “Nikahush Shigar” da sauransu, duk wannan yana nuna kenan wadannan abubuwa halal ne, a’a, ko daya, akan kira abu ne da yadda masu shi suke kira, don a gane shi, wani abin mamaki ma shi ne Mal Nura ya buga misali da Imam Muslim a cikin sahihinsa, amma da yana fahimta, da ya gane cewa, wannan kalmar ta “nikah” ba tana nuna yarda ba, domin shi kansa Imam Muslim tsarin yadda ya kawo hadisan yana nuna maka wasu sun shafe wasu.
Mal Nura ya ci gaba da cewa, ” Amma maganar Malam Rabi’u da ya ke cewa ba bu Gado a cikin Mut’ah, ya ke ganin ko ince Malaman Sunna suke ganin wannan kan iya warware auren na Mutu’ah wannan tsantsar jahilci ne da rashin sanin menene Shari’a.” Amsa : Wannan ya nuna cewa mal Nura baya fahimtar abin da yake karanta wa, ai ni a bayanina na kawo maganar matar mut’a bata gado ne a wajen bayanin bambancin auren dindindin da na mut’a, ba wai na kawo wannan bayani ba ne don shi ne dalilin da yake haramta mut’a ba. don haka abin da ya kamata a ce mal Nura ya yi anan shi ne, ya ce, a’a tana da gado, don haka babu wani bambanci tsakanin mut’a da auren dindindin. Sannan misalin mal Nura da ya kawo yana nuna cewa shi ne ma bai san shari’ar ba, saboda a auren mut’a ba gado, saboda ba aure ba ne, haya ce, don haka ma idan sun shardanta wa juna gado, wasu malaman shi’ar suka ce, akwai matsala, kamar yadda khomaini ya fada. (Duba Zubdatul Ahkam shafi na 248, da Tahriril Wasila 2/288). Annajafi – Malamin Shi’a – a cikin “Jawahirul Kalam” ya ce, : “A zahiri ko a bayyane wajen kebantar gado ga mata hudu sabanin matar mut’a, wadda take hayarta aka dauko a matsayin baiwa”. Don haka ko dai nine ban san shari’ar musulunci ba, ko kuma malamanku na shi’a!.
Amma kamanta matar mut’a da kwarkwara da Mal Nura ya yi, wani salo ne na wofintar da hankulan masu karatu, saboda dai ita kwarkwara a musulunci ba ta da matsayin matar mutum, wannan ma ya sa ko raba kwana da ita ma ba wajibi ba ne, haka ma ba a lissafinta a cikin mata hudun da musulunci ya yarda miji ya aura, ashe kenan in dai Mal Nura ya yarda da kamanta matar mut’a da kwarkwara, to ya yarda kenan bata cikin matan aure na dindindin. Amma kasancewar kwarkwara ba haramun ba ce, wannan saboda babu wani nassin da ya haramta ta, sabanin matar mut’a, haramun ce, Allah da Manzonsa sun haramtata har zuwa ranar Alkiyama!. (Mu hadu a kashi na biyu)

Advertisements

3 thoughts on “Auren Mutu’a Haramun Ne Har Zuwa Ranar Alkiya(Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)

  1. Hafizakallahu ina kai ina biyewa wanda kama sunan shima karya alwala yake sufa mutane ne wanda saidai ka kafa musu hujja da littafansu.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s