Auren Mutu’ah(Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)


Martani Ga Nuru Darussakalaini, Kashi Na Biyu (2)
Daga nan sai malamin namu ya shiga kokarin karyata ruwayar haramcin mut’a daga Aliyyu bin Abi Dalib, ga abin da yake cewa : ” Ibn Hajar a cikin sharhinsa na Fat’hul-Baariy daga As-suhailiy yace: “Kuma wannan Hadisin yana tattare ne da tsoratarwa akan matsalolinsa; domin a cikinsa akwai hani akan auren mutu’a ranar Khaibar. Kuma wannan (hanin) babu wanda ya sanshi daga Malaman Sira da Ruwwatul-athar (Masu naqalto Hadisi)” (Malam sai aje a duba: Fat’hul-baariy 9/210).
Alhamdu Lillahi, na riga dama tun tuni na duba fathul Bari, amma abin takaici sai na ga ka yi masa karya, babu inda ya fadi wannan maganar da ka fassarata haka, son zuciyarka ne ko kuma jahilcinka, ko kuma na wanda kake kwafowa daga wajensa, domin da kai kake komawa zuwa littattafan malamai kana karantowa da kanka, da ka gane cewa suna maka karya, ko kuma alal-akalli baka fahimtar abin da kake karantowa, ga abin da ibnu Hajar ya kawo daga Suhailiy da larabcinsa, don daliban ilimi da malamai su gwama da abin da ka fassara, su gani ko ka fassara daidai!
قال السهيلي: ويتصل بهذا الحديث تنبيه على إشكال لأن فيه النهي عن نكاح المتعة يوم خيبر، وهذا شيء لا يعرفه أحد من أهل السير ورواة الأثر، قال: فالذي يظهر أنه وقع تقديم وتأخير في لفظ الزهري، وهذا الذي قاله سبقه إليه غيره في النقل عن ابن عيينة. [فتح الباري 9/168 – 169)
Ma’ana : “Yana saduwa da wannan hadisi fadakarwa akan wata matsala, saboda a cikinsa (hadisin) akwai hana auren mut’a a ranar khaibar, wannan kuwa wani abu ne da ba wanda ya san shi cikin malaman tarihi da masu ruwayar hadisi, abin da yake bayyyana shi ne an samu gabatarwa da jinkirtarwa a cikin lafazin Zuhuriy. Sai Ibnu Hajar ya ce, “wannan abin da ya fada (wato suhailiy) wani ya riga shi cirowa daga Ibnu Uyayna”. Mai karatu idan ka koma Fathul Bari zaka ga cewa mas’alar da ake magana a kanta a nan, ita ce shin an haramta auren mut’a ne ranar Khaibar ko kuwa a wani lokacin ne daban aka haramta ta, ba maganar karyata ruwaya ake ba!, shi Assuhailiy yana ganin maganar cewa an haramta mut’a ranar khaibar masu riwaya ba su santa ba, ba wai hadisin ba, kamar yadda Mal Nura yake nunawa. Ba don tsawon abin da yake cikin Fathul Bari ba, da na nakalto shi gaba daya, don mu kara gane amanar nakalin ‘yan shi’a.
Haka Mal Nura ya ci gaba da hakaito maganganun malamai akan cewa yaushe ne aka haramta mut’a, yana mai kafa hujja da su akan karyata hadisin Aliyyu, saboda ya jahilci cewa, ba karyata hadisin suke ba, a’a bayanin tantace lokacin suke, kuma ma wani abin dariya “wai yaro ya tsinci hakori” duk malaman da ya kawo maganganunsu sun tafi akan haramcin mut’a din, sannan a gefe guda kuma sai ya ki ya ciro magangannun malaman da suka ba wa wadancan amsa, ina adalci ga mai karatu, ina tsoron Allah a cikin wannan aiki, in dai da gaske ne ka karanta “Fathul-Bari” akan wannan mas’ala, inda a can ne duk a ka yi maganganun da ka kawo, me yasa baka kawo ra’ayin karshe ba? wanda Al-hafiz Ibnu Hajar ya tabbatar, son zuciya!. Allah ya kiyashe mu!!. Ibnu Hajar ya ce, ”
وأما غزوة خيبر وإن كانت طرق الحديث فيها صحيحة ففيها من كلام أهل العلم ما تقدم. فتح الباري (9 / 170(
Ma’ana : “Amma hadisin yakin khaibar duk da cewa hanyoyinsa ingantattu ne, to akwai maganganun malamai a kansa wadanda suka gabata”. A nan zamu ga Ibnu Hajar baya raunana hadisin, sai dai yana magana ne a kan lokacin haramcin. Kai! Ibnu Hajar ya tafi akan tabbas Aliyyu dan Abi Dalib ya fadi wannan hadisi domin ya ce, )
والحكمة في جمع علي بين النهي عن الحمر والمتعة أن ابن عباس كان يرخص في الأمرين معا”
Ma’ana “Hikimar da sa Aliyyu ya hada tsakanin hanin (Cin naman) jakuna da mut’a shi ne saboda Ibnu Abbas yana yin rangwame a kan al’amuran guda biyun”. Me wannan jawabi yake nunawa Mal Nura!.
Mal Nura ya karyata ruwayoyin da suka zo cewa Ibnu Abbas ya dawo daga fatawar halaccin mut’a bisa dogaro da maganar Ibnu Baddal da Al-hafiz Ibnu Hajar ya hakaito cewa “an rawaito dawowarsa (Ibnu Abbas daga halaccinta) da sanadodi masu rauni” haka Ibnu Baddal ya ce, ba yadda Mal Nura ya fassara ba!. To amma anan mal Nura bai kawo bayanin shi Ibnu Hajar din ba, da ya yi a baya cewa, wadannan sanadodi sashensu yana karfafa sashe” فهذه أخبار يقوى بعضها ببعض” ma’ana : “Wadannan labarurruka sashensu yana karfafa da sashe” (Duba 9/172). Kaga kenan anan maganar ibnu Baddal da ibnu Hajar babu karo ga wanda ya san abin da ake nufi, ba wanda ya yi wa ilimi haye ba!.
Daga sai Mal Nura ya kawo ruwaya akan mut’ar hajji, saboda ya wofintar da hankalin masu karatu, to kifi yana ganinka mai jar koma!. Amma sukan da ka yi Imam Tirmiziy dama wannan halinku ne, amma dai na gaba ya yi gaba!.
Mal Nura ya ci gaba da cewa : “”An kasance ana yin Mutu’a guda biyu zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) to ni na hana kuma zanyi azaba akansu, Mutu’ar Aure da Mutu’ar Hajji” (Sharhul-Ma’aanil-Athar: 2/146, Malam Ahmad bn Muhammad bn Salmatul-Azdi). Amma sai ga shi su Ahlus-sunna din sun saki hani daya daga hani biyun da Umar din yayi sun kama daya. Domin kuwa har yanzu suna riqo da Mut’atul-haj, wato Hajin Tamattu’i, bayan shi gaba daya biyun ya hana, wannan wane irin son rai ne?! Tabbas da ace akwai wani abu dake nuna shafewar daga Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da ya dan jona shi a maganar sa, da bai tsaya danganta abin gare shi shi kadai ba. Don haka a kan kansa, maganganun shafewar inkarin maganar Halifan ne”.
Da farko dai mal Nura yaki cewa komai akan ruwayar Ibnu Majah da na yi ishara zuwa gareta a bayanina, saboda a cikinta Sayyidina Umar ya nuna cewa ba shi ne ya hana mut’a ba, Manzon Allah ne (S.A.W) ya hana, sai Mal Nura ya kawar da kai daga gareta, saboda zata warware abin da yake so ya gina na cewa Umar shi ne ya hana mut’a ba Manzon Allah (S.A.W) ba. Amma dangane da ruwayar da ya kawo, to sai me?, ai dama dukkan malamai sun yarda da cewa, sayyidina Umar shi ne wanda ya shaharar da hanin mut’a, saboda ya ji wasu suna aikatawa, don haka ya fito ya hana, a matsayinsa na shugaba, shi ne abin da waccan ruwaya take tabbatarwa. Amma maganar cewa Ahlus-sunnah sun dau daya hanin ba su dau dayan ba, wannan ba haka ba ne, shi dai Mal Nura ne bai sani ba, amma da yana karatu zai ga bayanan malamai dangane da yin tamattu’i a wajen aikin hajji, da kuma amsa da suke bayarwa na cewa Manzon Allah (S.A.W) ya yi, kuma ya yi umarni da a yi, sabanin mut’ar aure Manzon Allah ya hana kamar yadda ya gabata.
Sannan sai Mal Nura ya ce, “Malam Rabiu ya kawo Hadisin Rabii’u bn Sabrata Al-Juhaniy da ya ke cewa auren mutu’a haram ne. To amma da shi Malam Rabi’u idanuwansa sun kai kan wadannan Hadisan da suka zo a wannan lambta (1406) da bai yi hanzarin kawo shi a matsayin hujja ba. Saboda Hadisin farko ma na wannan lambar (1406) ko kuma a wata daba’ar Hadisi na (3485), yana nuna tsantsar halasci ne, kuma Manzon nema ya umarta a lokacin da aje ayi auren mutu’ar a wannan Yaqin, wanda karshen maganar ma ga abin da Manzon (S) ya ce: “….. Duk wanda ya kasance a tare da shi akwai wannan matar ta mutu’a to ya sake ta”.
Amsa : Ban san me mal Nura yake so ya nuna a nan ba, ai wannan hadisin da ya kawo yana daya daga cikin hadisan da suke nuna cewa Mut’a da halal ce, amma daga baya aka haramta ta, kuma wannan shi ne abin da Imam Muslim ya nuna, wajen fara kawo irin wadannan hadisai a farkon babu Nikahil Mut’a” sannan ya kawo wadanda suke nuna haramci, don haka ba wani abu ka fada a nan ba. Kuma wannan ita ce amsar hauragiyar da ka yi ta yi, wajen kawo hadisan halaccin mut’a da haramcinta, kana ce wa sun yi karo da juna, saboda baka san cewa babu sabani ba akan da halal ce, amma daga baya Manzon Allah (S.A.W) ya haramta ta, wadanda duk wadannan ruwayoyi suna nan, babu kuma wanda zai ce karo da juna ne sai wanda bai yi karatu ba!. (Mu Hadu A Kashi Na Uku).

Advertisements

2 thoughts on “Auren Mutu’ah(Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s