SHI’A DA KAFIRTA MUSULMI!!!(Sheikh Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)


Duk mai bibiyar tattaunawar da ake yi tsakanin ‘yan shi’a yan sha biyu da yan uwa Ahlussunnah a fcbk zai ga yadda yan shi’a suke yawan tuhumar Ahlussunnah da cewa suna kafirta musulmi, wani lokacinma ba a kan wannan abu ake tattaunawar ba, amma sai sun san yadda suka lankwaso zance, suka karkatar da hankulan mutane zuwa ga waccan tuhuma ta karya, maras asali a cikin littattafan Sunnah.
Amma abin da zai baka mamaki shi ne a duk cikin kungiyoyin addini babu kungiyar da ta kai shi’a kafirta musulmi, tare da zagi da cin mutuncin bayin Allah, wannan abu ne da yake kunshe a cikin manya-manyan littattafansu, ba wai tuhuma ba ce ta karya maras asali irin wadda suke wa Ahlussunnah, don haka ma bari mu kawo kadan daga cikin irin dimbin riwayoyinsu da suke tabbatar da haka, watakila wasu daga cikinsu wadanda aka rude su da karya da takiyya su sake nazari, su fahimci gaskiya.
1- Babban malaminsu Alkulainiy ya kawo riwaya a cikin littafinsa mai suna Alkafi 8/246 daga limaminsu muhammad Al-bakir yana cewa, “Mutane sun yi ridda bayan Annabi s.a.w sai mutum uku, Almikdada dan Aswad, da Salman Al-farisiy, da Abu zarril Gifari”.
2 – hakanan dai ya zo a cikin Alkafi 1/233 Imaminsu Arrida yana cewa “Babu wanda yake kan addinin Musulunci wanda bamu ba kuma ba dan shi’armu ba”.
3 – A wata riwayar a cikin Arrauda Minal Kafi 8/2109) daga limaminsu Abu Ja’afar yana cewa, “Ya kai Abu Hamza wallahi dukkan mutane gabadayansu yan zina ne banda yan shi’armu”.
4- Babban Malaminsu Ni’imatullahi Aljaza’iriy yana bayanin hukuncin Nawasib – wato Ahlussunnah – ya ce ” Kafirai ne su, najasa ce da IJMA’IN DUKKAN MALAMAN SHI’A IMAMIYYAH, sun fi yahudu da nasara sharri. Alamar Nasibi kuwa ita ce gabatar da wanin Aliyyu a wajen khalifanci”. Duba Al-anwarun Nu’umaniyya 2/206 – 207).
Wannan kadan kenan daga cikin irin riwayoyi da dimbin maganganun malaman shi’a a kan kafirta duk wanda ba dan shi’a ba, kuma wannan ita ce akidar duk wani dan shi’a na gaskiya, shi ne yana ganin kafircin wanda duk ba shi’a ba ne, kai yana ganinsa dan zina ne, kamar yadda muke gani suna rubutawa a facebook yayin tattaunawa da su.
A bangare guda kuma baza ka samu irin wannan kafirtawar ba a litattafan Sunnah, kai hatta shehun Musulunci Ibnu Taimiyyah da Shehun musulunci Muhammad Bin Abdulwahab wadanda kullun ake tuhuma da yi musu karya cewa su suka kawo kafirta musulmi baza samu irin wannan a cikin litattafansu ba, sai dai a lankwasa musu magana ko a yi mata mummunar fahimta. Allah ka tsare da bata, ka dora mu akan madaidaiciyar hanya.

Advertisements

One thought on “SHI’A DA KAFIRTA MUSULMI!!!(Sheikh Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s