ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)


ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam
Fitowa Ta 39

Daga Cikin Fifikonsa
5. Daukakar Al’ummarsa (kashi na biyu)
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yakan nuna damuwa a kan abubuwan da Allah ya kaddara faruwarsu na fitinu da za a jarabci al’ummarsa da su. Yana yawan jan kunne a kan duk wata fitina da zata bayyana a cikin al’ummarsa musamman kuma karshen zamani. Yakan lurar da al’ummarsa irin matakan da ya kamata su dauka idan fitinun sun faru. Misali, a hadisin Irbad bn Sariya, lokacin da Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi ma su wasici cewa ya yi, “Duk wanda ya yi tsawon rai a cikinku to, zai ga sabani mai yawa”. Yana nuni zuwa ga rabuwar al’umma ta hanyar bayyanar bidi’oi da kungiyoyi masu kawar da al’umma daga tafarkinsa. Don haka sai ya ba da mafita: “Ina umurninku da bin sunnata da sunnar halifofina shiryayyu”. Saboda wadannan halifofin nasa sun kwankwadi sunnarsa kuma ba zasu kauce ma ta ba ko da taki daya. Sannan ya ce, “Ku yi hattara da fararrin abubuwa, domin duk abin da aka farar a cikin addini bidi’a ne, kuma dukkan bidi’a bata ce”.
Jinkayin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ga al’umma bai tsaya a nan duniya ba. A lahira ma al’ummarsa zata gamu da shi.
Abdullahi dan Amr ya ruwaito hadisi cewa, manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya karanta fadar annabi Ibrahim in da yake cewa: “Ya Ubangijina! Hakika wadannan gumaka sun batar da mutane da yawa. To, duk wanda ya bi ni yana tare da ni, wanda kuma ya saba ma ni kai mai gafara ne, mai jinkai”. Da kuma fadar annabi Isah Alahis Salam: “Idan ka yi ma su azaba to, su bayinka ne. Idan kuma ka gafarta ma su to, kai buwayayye ne, mai cikakkiyar gwaninta”. Sai manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya daga hannayensa yana cewa, “Ya Allah! Al’ummata! Al’ummata! Sai ya rinka kuka. Madaukakin sarki sai ya ce da Jibril Alaihis Salam, ka je wurin Muhammad – Ubangijinka shi ne ma fi sani – ka tambaye shi me yake yi wa kuka? Sai Jibril Alaihis Salam ya zo ya tambaye shi. Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce, sha’anin al’ummata ya dame ni. Jibril Alaihis Salam ya koma ya sanar da Ubangiji – Ubangiji kuwa shi ne ma fi sani. Sai ya ce ma sa, ka koma ka gaya ma Muhammad (Sallallahu Alaihi wasallam) “Hakika, Mu, za mu yardar da kai game da al’ummarka. Ba za mu bata ranka ba”. Sahih Muslim, hadisi na 202. Duba kuma sharhin Imam Nawawi (3/79).
Wannan alkawari da Madaukakin sarki ya yi ma annabinsa babu shakka zai cika shi. Babbar hanyar da Allah zai cika ma sa wannan alkawari kuwa ita ce ta hanyar ba shi ceto. Kuma tun a nan duniya Allah ya bai wa manzonsa zabi tsakanin a shigar da rabin al’ummarsa aljanna ko kuma a ba shi damar yin ceto. Amma sai ya zabi na biyun don ya tabbatar zai fi zama rahama ga al’ummar tasa. Don haka, manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce, duk muminin da ba ya shirka lalle cetona zai riske shi. Sahih Al-Bukhari, hadisi na 6305.
A lokacin da kowa yake ta kansa filin alkiyama, manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam zai je ya surmuyar da kansa gaban al’arshi yana sujada ga Ubangijin girma da daukaka, ya rinka ganawa da shi yana fadanci. Zai yabi Allah da wasu kalmomi da Allah ne zai yi ma sa ilhamar su. Sannan idan Allah ya ce ma sa “Ya Muhammad! Ka daga kanka. An yi ma izni ka nemi duk abin da kake so za a ba ka”. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam zai tashi ya yi godiya ga Allah yana mai cewa, “Ya Allah! Ni dai al’ummata! Ya Allah! Ni dai al’ummata!” A nan ne sarki mai rahama zai ce ma sa, “Mun ware ma al’ummarka – wadanda ba hisabi a kan su – kofar dama ta aljanna. Kuma suna iya shiga tare da sauran jama’a ta sauran kofofi”. Sahih Al-Bukhari, hadisi na 1712.
A wata ruwaya Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce, “Za a ware ma ni wadanda zan shigar da su aljanna har sai na yi mayawa ta hudu sai a ce ma ni, ai yanzu babu wanda ya rage sai wanda Alkur’ani ya daure, wanda ya zama wajibi ya tabbata a wuta”. Sahih Al-Bukhari, hadisi na 4476.
Kada mu manta cewa, tun a duniya Allah ya bai wa kowane annabi addu’a karbabbiya, sai manzonmu ya ajiye tasa saboda mu a wannan rana.
Kafin haka, duk annabawa da manzannin Allah (amincin Allah ya dada tabbata a gare su gaba daya) sun amince ba wanda zai nemi ceton mutanen duniya, ya nemi Allah ya yi ma su hisabi sai annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam. Duba karin bayani a cikin Fathul Bari na Ibn Hajar (12/374-375) da Sharhin Nawawi a kan Sahih Muslim (3/75).
Kafin mu dakata da zancen darajojin fiyayyen halitta zai yi kyau mu fadi wasu daga cikin darajojin da ake jingina ma sa bisa jahilci ko son zuciya, domin nasiha gare mu da tsarkake addinin Allah daga gurbata. Bayan haka sai mu koma kan sha’anin rayuwarsa mai albarka.
Allah ya taimake mu.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s