ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 46( Dr. Mansur Sokoto)


Ayari Na Biyu
A hankali ayarin farko suka ci gaba
da janyo mutane asirce suna kawo
su wurin manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam yana yi masu
sharhin da’awarsa suna ba da
gaskiya da shi. Babu kamar Abubakar
a wannan fage, kasancewar sa
babban mutum mai matsayi wanda
jama’a ke taruwa a gidansa kuma
wanda ya yi imani mai karfi da
wannan sabon kira da ya bayyana a
hannun amintaccensa wanda ba ya
da shakku a kan sa.
A daidai wannan lokacin ne sayyidina
Bilal ya musulunta. Sai kuma Abu
Ubaida bn Al-Jarrah daga gidan
Harith bn Fihr da Abu Salamata bn
Abdil Asad (dan gwaggon manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam;
Barratu ‘yar Abdulmuttalib kuma
abokin shan nononsa) da Arqam bn
Abil Arqam – su biyun daga gidan
Makhzum – da Usman bn Maz’un
(abokin shan nono tare da manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam) da
kannensa biyu; Qudamatu da
Abdullahi. Da Abidatu bn Harith bn
Muttalib bahashime da matarsa
Fatima bint Al-Khattab (kanwar
sayyidina Umar). Da Khabbab bn Al-
Arat. A haka dai sai da suka kai
mutane 40 daga gidaje daban daban.
Daga nan kuma musulunci ya zamo
shi ne labarin da ake tadi a kan sa
duk inda aka zauna a garin Makka.
As-Sirah An-Nabawiyyah, na Ibn
Hisham (1/245-262).
Amma fa yana da matukar wuya
manazarcin tarihi ya iya tantance
jerin musuluntar jama’a a wancan
lokaci. Dalili kuwa shi ne, duk wanda
ya musulunta a wancan hali da ake
ciki ba lalle ne ya san sauran
wadanda suka musulunta ba kai
tsaye. Iyakar huldarsa da manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ne
da mutum daya ko biyu, domin ba
maslaha ba ne a bayyana ma sa
sunayen sauran jama’a da ake tare
da su. Wannan zai fassara maka
sabanin da aka samu wajen jerin
sunayensu, kodayake duk an hadu a
kan cewa, su ne “As-Sabiqun Al-
Awwalun”.
Sa’ad bn Abi Waqqas yana cewa, ni
ne na uku a musulunta kuma a ranar
da na musulunta ba wanda ya sake
musulunta har sai da aka yi sati
daya. Sahih Al-Bukhari, hadisi na
3737.
Ibn Mas’ud (R) yana cewa, ni ne na
shida a shiga musulunci. Al-
Mustadrik na Hakim (3/313).
Ammar bn Yasir ya ce, na musulunta
ne a lokacin da ba kowa tare da
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam sai wasu bayi guda biyar
(yana nufin Bilal, da Zaid, da Amir bn
Fuhairata – bawan Abubakar – da
Yasir da dansa Ammar) da mata biyu
da Abubakar. Sahih Al-Bukhari, hadisi
na 3660.
Ibn mas’ud yana cewa, mutum
bakwai aka fara sanin musuluncinsu;
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam da Abubakar da Ammar da
Sumayya matarsa da Suhaib da Bilal
da Miqdad. Subulul Huda war-Rashad
Fi Sirati khairil Ibad, na Salihi,
(2/306).
Ala kulli halin, wadannan bayin Allah
sun rungumi addinin musulunci da
wuri, kuma sukan hadu da manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a
wasu lokuta don samun karin haske
da sauraron karatun Alkur’ani. Sukan
kuma yi sallah sau daya ko sau biyu
amma fa asirce ta yadda sai an fita
bayan gari a tsakanin duwatsu in da
ko tsuntsu bai iya samun labari.
Jibril Alaihis Salam ya zo da kansa
ya koya ma manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam tsarki da alwala da
sallah. Mukhtasar Sirat Ar-Rasul na
Abdullahi An-Najdee, shafi na 88.
Da farko duk da yaduwar labarin
musulunci a cikin garin Makka ba
wata tsangama da musulmi suka
gamu da ita saboda ba a tuhumar su
da zagin gumaka ko sukar addinin
iyaye da kakanni. Amma daga bisani
sai labarin ya canja kamar yadda
zamu gani a nan gaba.

Advertisements

One thought on “ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 46( Dr. Mansur Sokoto)

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s