ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 49( Dr. Mansur Sokoto)


An Fara Kai Ruwa Rana Tsakanin
Musulunci Da Kafirci
Fara bayyana da’awar musulunci ke
da wuya sai duk inda hankalin
shugabannin Quraishawa yake ya
tashi, suka kalli musulunci a
matsayin wani gungu na ‘yan tawaye
da ya zo ya tarwatsa tarayyar
kasarsu, ya wautar da hankalinsu da
na iyayensu, a yayin da zukata masu
tsarki daga cikin jama’a suka rika
shiga guda guda a cikin addinin. Da
lokacin aikin Hajji ya gabato sai suka
ji tsoron kada manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya samu
damar tallata da’awarsa ga ba’ki ‘yan
kasashen waje da zasu halarci aikin
Hajji. Don haka, sai suka hadu a
gidan Walid bn Mughira domin su
shawarta. A nan ne fa Allah ya tona
asirinsu. Domin kuwa da aka hadu
sai gaba daya suka ce, to, Walid kai
ne dattijo mai yawan shekaru da
gogewa ga al’amurran rayuwa a
cikinmu. Don haka ya kamata mu san
ra’ayinka a kan wannan sabon abu da
dan garinmu ya zo da shi don mu
san abin da za mu fada ma baki idan
suka gabato. Sai Walid ya ce, a’a. Ai
ni mai yanke hukunci ne. Don haka
ku fada sai in ji naku ra’ayi tukuna.
Sai wasu suka ce, to mu muna ganin
boka ne kawai. Walid ya ce, haba!
Yaushe za a hada kalaman
Muhammadu da na boka? Suka ce, to
mahaukaci ne. Ya ce, ai duk mai
hankali ya san bai fi Muhammadu
hankali da kome ba. Suka ce, to
mawaki ne. Ya ce, tun yaushe muke
jin mawaka da zizar maganarsu?
Wane nau’i ne na waka da ma’auninta
ba mu saba da shi ba? Suka ce, to
kenan dai dabo yake yi yana sihirce
mutane. Ya ce, anya! A dai sake
dubawa. Wallahi wannan abin da
Muhammadu yake karantawa wani
irin dandano ne yake da shi. Akwai
wata irin nakiya a samansa. Kasansa
gwanin dadi ne. Rassan kamar
nunannun ‘ya’yan itace ne. Duk abin
da ka fadi game da shi take ana gane
karya kake yi. Amma dai kawai mu
tsaya a kan cewa dabo ne yake yi tun
da mun ga yana raba da da mahaifi,
ya shiga tsakanin wa da kanensa ko
mata da mijinta, kuma ya raba mutum
da danginsa.
Da haka suka tashi zukatansu a cike
da ruduwa domin sun san ba su yi
ma hankulansu da zukatansu adalci
ba. Da mahajjata suka gabato sai
kuwa suka shiga kamfen batunci a
kan da’awar manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam tsakanin gaskiya da
karya. Abinka da sha’anin gaskiya
wannan yekuwa tasu ba abin da ta
kara ma wannan kira sai karbuwa da
shiga zukatan jama’a. Aka watse
daga aikin Hajji duk in da ka je ba
abin da ake yi sai tadi a kan wannan
sabon addini. Babu abin da ya fi ba
mutane mamaki kamar matsayin da
Abu Lahabi ya dauka wanda shi ne
baffan manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam na bin sa a duk in da ya
shiga yana kiran mutane “Ya ku
mutane! Ku sheda babu wanda ya
cancanci bauta sai Allah don ku
samu babban rabo”. Shi kuma sai
yana fadin “Ku fita batunsa karya
yake yi”!
Daga wannan shekarar ne fa labarin
musulunci ya yadu a cikin sassan
duniya. Ba in da zaka je baka ji ana
tattaunawa a kan sa ba.
Raudhat Al-Anwar Fi Sirat An-Nabiy
Al-Mukhtar, na Mubarakfuri, shafi na
30-31.
To, ko wadanne irin matakai ne
Quraishawa suka dauka ganin sun
dakile hasken musulunci? Sai ku
dakace mu a darasi na gaba. Allah ya
nuna mana.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s