ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 50( Dr. Mansur Sokoto)


Matakan Fada Da Musulunci
A lokacin da Quraishawa suka lura da
ci gaban musulunci da yaduwarsa
sun bi dukkan hanyoyin da suke
iyawa don ganin sun dakushe shi.
Daga cikin matakan da suka dauka
har da:
1. Kokarin rage ma sa karfin tsaro.
Babu wani mutum da Allah ya taimaki
manzonsa da shi a wannan lokaci
kamar Abu Talib; baffansa. Dalili
kuwa, Quraishawa na jin nauyin sa
matuka. Shi kuma yana ba manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam
cikakken goyon baya da kariya ta
yadda ba su iya cutata ma sa da
kome don jin nauyin baffan nasa.
Saboda haka sai suka fara matsa ma
sa lamba don ya hana dansa ci gaba
da wannan kira da yake yi. Ko kuma
alal akalla ya janye goyon bayan da
yake ba shi, alabashi su kuma su far
ma sa su yi ma sa duk abin da suka
ga dama. Amma Abu Talib bai ba su
hadin kai ba. Sai dai ya gaya ma su
kalamai masu dadi don hana
dumamar yanayi da yamutsa hazo a
tsakanin su.
2. Barazanar taba lafiyarsa
A wannan karon ne baffansa Abu
Talib ya ji ma sa tsoro sosai har ya
kira shi yana rarrashinsa a kan kada
ya janyo ma kansa matsala. Sai
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya daga kai sama ya ce ma
sa, “Ka ga wannan rana”? Ya ce, eh.
Ya ce: “To, ko daga can za su
dosano zafi su cinna man ba zai
hana ni isar da sakon Allah ba”.
Silsilat Al-Ahadis As-Sahiha, hadisi
na 92. A nan ne Abu Talib ya hakura
kuma har ya kara da cewa, jama’a
wannan dan nawa fa bai taba karya
ba. Don haka kawai ku fita batun sa.
Allah gwanin hikima! Duk wannan
dauki ba dadi da ake yi fa shi Abu
Talib bai karbi musulunci ba. Iyaka
dai Allah ya jarabce shi da son
dansa ne so irin na halitta, ba irin
son da musulmi suke yi ma sa a
matsayinsa na masoyin Allah kuma
jekadansa ba. Kuma da a kaddara a
wannan lokacin Abu Talib ya
musulunta to, da Quraishawa sun
hade su gaba daya sun saukar da
mummunar ukuba a kan su. Nabiyyur
Rahmah, na abokinmu Dr.
Muhammad Sani Umar Musa, shafi
na 30.
A nan za ka gane cewa, kafirci ma aji
aji ne. Ina za a hada kafircin Abu
Talib da na Abu Lahabi! In da akwai
wani kafiri da zai shiga aljanna to, da
Abu Talib ne. Amma hukuncin Allah
ya zarata a kan haramta ko
kamshinta a kan kafirai. Suratul A’raf:
50. Amma da yake Allah mai
cikakken adalci ne zai sassafta wa
Abu Talib azabar wuta har ya
kasance a cikin wani kududdufi na
wuta wanda shi ne ma fi sassafcin
wuri a cikin Jahannama da ceton
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam. Sahih Al-Bukhari, hadisi
na 3670 da Sahih Muslim, hadisi na
209.
3. Soke-soke Da Tuhumce-tuhumce
Mushrikai sun dukufa sosai wajen
bata sunan wannan taliki da Allah ya
zabe shi ya aiko shi don ya isar da
sako. Suka ce ma sa mahaukaci,
boka, makaryaci. Kuma wai, ba wani
abu ne yake yi ba sai zuki-ta-mallau!
Amma a banza. Mutane sai kara
fahimtar gaskiya suke yi suna
rungumar ta. Daga bisani sai suka
dukufa wajen daukar
4. Matakin Izgili Da Azabtarwa
Babu wani musulmi da bai gamu da
wani nau’i na muzgunawa da cutarwa
ba a daidai wannan lokaci. Akwai har
wadanda suka yi fice da sunan “Yan
izgili” saboda yadda suka dukufa
wajen cin zarafin manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam da
jama’arsa. Wadannan mutane sun
hada da wasu makwautansa irin su
Uqbatu dan Atu Mu’ait da Adiyyu dan
Hamra’u da Al-Hakam dan Abul Ass
da Ibnul Asda’i Al-Huzali da
sauransu. Shi Abu Lahabi kam ba a
ko maganar cutawar sa shi da
muguwar matarsa Ummu Jamil. In
sha Allahu za mu kawo ma ku wasu
daga cikin miyagun ayyukansu don
su zama wa’azi da jan hankali a gare
mu.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s