ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 51( Dr. Mansur Sokoto)


Wasu Daga Cikin Yan Kungiyar Masu
“Izgili”
A can baya mun ga irin matakan da
arna suka dauka don dakile addinin
musulunci amma ba su ci nasara ba.
Don haka sai suka koma ga cin zarafi
da amfani da karfin tuwo. Mun ga
kuma matsayin da Abu Lahabi ya
dauka na bayyananniyar adawa shi
da muguwar matarsa. A nan za mu
kawo wasu daga cikin fitattun
mushrikai – ban da shi – wadanda
suka taka muguwar rawa irin tasa
wajen muzguna ma manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam da
sahabbansa da kuma irin hakurin da
wadannan bayin Allah suka yi,
sannan daga bisani mu ji umurnin da
Allah ya ba su.
1. Abu Jahli bn Hisham:
Zanannen sunansa shi ne Amru dan
Hisham dan Mughira. Dan babban
gida ne daga yankin Makhzumawa;
gidan da ke jayayya da Banu Hashim
tun kafin bayyanar musulunci. An yi
ma sa lakabi da Abul Hakam saboda
baiwar da Allah ya yi ma sa ta kaifin
wayo, wanda a kan sa kawai
Quraishawa suka keta dokar
kwamitinsu na dattawa wanda ba a
bari kowa ya halarci zaman sa sai ya
kai shekaru 50. Amma shi da
shekaru 25 aka nemi ya fara halartar
sa, don irin kaifin basirarsa. Musulmi
sun canja ma sa wannan lakabi na
“Abul Hakam” (dan wayo) zuwa Abu
Jahli (dibgagge) kasancewar
basirarsa ta dakile daga bin gaskiya
a lokacin da manzo ya zo da ita.
Abu Jahli na cikin wadanda ba su jin
kunyar cutata ma manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam har a
bainar jama’a. Bukhari ya ruwaito irin
wulakancin da Abu Jahli ya taba yi
wa manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam a cikin dakin Allah mai
alfarma inda ya yaba ma sa mahaifar
rakumi a kan wuyansa tana tsiyaya
da jini da kazanta a daidai lokacin da
manzon yake sujuda. Kuma aka rasa
wanda zai dauke ma sa ita har sai da
Allah ya kawo ‘yarsa Fatima wacce
ba wani dattijon da ke iya yi ma ta
kome saboda kankantarta. Sahih Al-
Bukhari, hadisi na 1794.
2. Sai kuma Uqbatu dan Abu Mu’ait:
Shi kuma wannan dan gidan Umayya
ne. Kuma shi ne ya taba shake
wuyan rigar manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam a lokacin da yake
sallah. Bai sake shi ba har sai da
sayyidi Abubakar Radhiyallahu Anhu
ya lura da shi ya rugo ya cafke shi ta
wajen kafadunsa ya tunkude shi yana
karanta fadar Allah Ta’ala: “Haka
kawai za ku kashe mutum don ya ce
Allah ne ubangijina! Alhalin kuma ya
zo ma ku da hujjoji daga wurin
ubangijinku?” Suratu Gafir: 28. Sahih
Al-Bukhari, hadisi na 3678.
3. Akwai kuma Asi bn Wa’il wanda
Allah ya saukar da aya ta 78-80 a
cikin Suratu Maryam a kan
sha’aninsa. Ya kasance mai yawan
izgili da bayyana adawa ga manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da
sahabbansa. Duba: Sahih Al-Bukhari,
hadisi na 2091 da Sahih Muslim,
hadisi na 2795.
4. Akwai kuma Walid bn Mughira,
baffan Abu Jahli wanda Allah ya
yalwata ma sa arziki, ya ba shi
wadatar haifuwa. Amma sai ya
kasance kuri yake ma Allah da
wadannan ni’imomi da ya yi ma sa.
Ya taba jin karatun Qur’ani daga
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam har ya ratsa jikinsa, ya
gaya ma mutane cewa, wannan
magana ta fi karfin mutum ko aljani,
kuma dandanonta ya fi karfin a
misalta. Amma da suka kira shi a
gaban kwamitin dattawa sai ya
waske; ya ce, ai Qur’ani siddabaru ne
kawai mai sa masoya su raba gari su
koma gaba. A kan sa Allah Ta’ala ya
saukar da ayoyin Suratul Muddassir
daga ta 11 zuwa ta 30. As-Sirah An-
Nabawiyyah na Ibn Ishaq
(1/332-334) da Al-Mustadrik na
Hakim (2/506) kuma Hakim din ya
inganta shi tare da amincewar Imam
Ad-Dhahabi.
5. Akwai kuma Nadhr bn Al-Harith
daga gidan Abdud-Dar. Mutum ne da
ya yi tafiye tafiye a kasashen waje ya
zo da labarai masu nashadantarwa.
Kuma da su ne yake kokarin dauke
hankalin mutane daga ayoyin Allah
da manzo yake karantawa. Nur Al-
Yaqeen, na Sheikh Muhammad Al-
Khudary, shafi na 38.
6. Akwai Aswad bn Abd-Yaguth
wanda ya fito daga gidan kawunnen
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam amma yana nufin sa da
izgili, yana cewa, “Yau Muhammadu
ko an samu wani sako daga sama?”.
Nur Al-Yaqeen, na Sheikh
Muhammad Al-Khudary, a wurin da
ya gabata.
7. Akwai kuma Aswad bn
Abdulmuttalib Al-Asadi, dan kabilar
Banu Asad. A matsayin kane yake
wurin uwarmu Nana Khadija. Amma
Allah bai yi ma sa rabo ba, sai ya yi
rajista da wannan batattar kungiya ta
masu izgili wadda Allah ya saukar da
karshen Suratul Mutaffifun a kan su
da kuma aya ta 95 zuwa 96 a cikin
Suratu Hijr. Duba littafin da muka
fada a sama. Sannan ku dakace mu
sai darasi na gaba. Allah ya hada mu
da alheri.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s