ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 52( Dr. Mansur Sokoto)


Musulunci Ya Ci Gaba Da Yaduwa A
Sauran Sassa
Kafin mu koma kan irin azabar da
musulmi suka dandana a hannun
mushrikai, za mu yi tsokaci game da
yaduwar musulunci a wannan zamani
da muke magana a kan sa zuwa
sauran sassan yankunan larabawa.
Duk da irin muzgunawar da manzon
rahama Sallallahu Alaihi Wasallam
yake gamuwa da ita a cikin Makka da
cin zarafin da danginsa Quraishawa
suke ma sa, gami da kanfe na
batunci. Duk wadannan ba su hana
addinin musulunci ya ci gaba da
mikawa zuwa kasashen waje ba. Kai,
saboda irin yadda ake maganarsa a
garuruwa ne ma wasu masu tsarkin
zuciya da neman gaskiya suka yo
tattaki zuwa birnin Makka don
tantancewa da gane gaskiya, kuma
cikin iyawar Allah da suka samu
gaskiyar nan take suka karbe ta.
Daga cikin wadanda Allah ya yi ma
wannan baiwa akwai:
1. Abu Dhar Al-Gifari:
Gifara kabila ce da take kan hanyar
matafiya mutanen Makka idan zasu je
Madina. Tana a cikin yankin Yanbu’
na yanzu, ‘yan kilomitoci kadan zuwa
Madina. A wajen su ne kuma gunkin
Manata yake. A gidajen wannan
kabilar ne labarin bayyanar manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya je
ma su, sai Abu Dharr ya aiki kanensa
Unais don ya nemo ma sa gaskiyar
labarin. Da dan uwan nasa ya zo sai
ya ce ma sa, ni dai na ga wani
mutum mai alamun kirki yana kira
zuwa ga alheri. Abu Dharr ya ce, bari
in je da kaina. Da ya zo Makka bai
nemi labari wurin kowa ba sai ya
lizimci kawaici kwana da kwanaki
yana kiwon hankalin mutane, har
Allah cikin ikonsa ya hada shi da Ali
dan Abu Talib Radhiyallahu Anhu
wanda – a cikin hikima – ya kai shi
wajen manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam. Ba tare da bata lokaci ba
Abu Dharr ya musulunta. A nan ne fa
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya ba shi shawarar ya
komawarsa gida salun alun bakinsa
kanen kafarsa. Amma Abu Dhar ya
ce, sam. Shi fa bai ga abin boyo ga
addinin gaskiya ba. Ai kuwa
shelantawarsa ke da wuya da furta
kalimar shahada sai kafirai suka yi
ma sa caa! kamar zasu kashe shi. Da
kyar Abbas – baffan manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam – ya
kwace shi a hannunsu yana tsoratar
da su daga martanin kabilarsa. Duk
da haka kuma kashegari Abu Dharr
bai bar Makka ba sai da ya sake
shelanta musulunci. Da zai tafi gida
kuma manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya neme shi da ya kira
mutanensa – idan ya je – zuwa ga
musulunci. Sahih Al-Bukhari, hadisi
na 3522 da Sahih Muslim, hadisi na
2474.
Da komawar sa gida sai duk ‘yan
gidansu suka musulunta. Cikin su
har da mahaifiyarsa. A rana daya
rabin garin suka musulunta bayan da
ya tara su ya ba su labarin manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.
Sauran rabi kuma suka ce, idan
manzon Allah ya zo zasu yi masa
mubaya’a hannu da hannu. Kuma da
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya yi hijira zuwa Madina
sai duk suka cika alkawari; suka
same shi a can suka mika
hannayensu suka yi ma sa mubaya’a.
Sahih Muslim, hadisi na 2473.
Wannan tabbataccen labarin yana
nuna mana ko wane irin mutum ne
shi Abu Dharr. Babu shakka yana
cikin irin nau’in mutanen da jita-jita
ba ta girgiza su. Haka kuma ba sa
shayin bayyana ra’ayinsu ko sama na
ruwan kibau kasa na aman wuta.
Kamar yadda zamu gano kaifin
hankalinsa da basirarsa tare da
tsarkin zuciyarsa. Abin da ya sanya
shi bai yi jayayya ba ko kadan da aka
karanta ma sa sakon musulunci.
Haka kuma zamu ga yadda
mutanensa suka amince da shi.
Dalilin da ya sa suka karbi musulunci
nan take. Tun kafin bayyanar
musulunci Abu Dhar mutum ne mai
taka-tsantsan da kirdadon gaskiya a
cikin duk lamurransa. Da irin
wadannan tsarkakakkun bayin Allah
ne Allah ya fara aza tubalin
addininsa.
Zamu kawo wasu ire-irensa wadanda
jita-jitar da ake yadawa kan manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ta
zamo dalilin shiriyar su. Allah ya
shiryar da mu zuwa ga gaskiya.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s