ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 53( Dr. Mansur Sokoto)


Musulunci Ya Ci Gaba Da Yaduwa
2.Musuluntar Amru bn Abasata.
Wannan shi kuma wani bawan Allah
ne da ya kasance yana kyamar
ayyukan jahiliyyah. Don haka da ya ji
ana zagin manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam cewa ya bar tafarkin
da aka sani sai ya niko gari ya nufato
Makka. Ko da ya zo ana tsakiyar
lokacin da musulmi suke shan azaba.
Da kyar da dabara ya samu kebanta
da ma’aiki. Sai ya tambaye shi “mene
ne kai?” Ya ce ma sa “Ni annabi ne”.
Ya ce, mene ne annabi? Ya ce: “Allah
ne ya aiko ni”. Ya ce: Da me ya aiko
ka?”.
Ya ce: “Ya aiko ni da sada zumunta,
da karya gumaka. Kuma ya ce, kada a
bauta ma kowa sai shi kadai”. Amru
ya ce: “To yanzu wa ke tare da kai?”
Ya ce: “Akwai da, akwai kuma bawa”.
A nan ne fa Amru ya ba da gaskiya
kuma ya kulla niyyar zama a wurin
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam duk da halin da ya tarar
ake ciki domin ya koyi addini. Amma
sai manzon Allah ya lurar da shi
cewa, Makka ba ta zaunuwa a gare
ka tare da mu a yanzu. “Ba ka ganin
halin da muke ciki da jama’a?” “Kai
dai ka tafi kawai garinku. Idan ka ji
Allah ya ba ni rinjaye sai ka zo ka
same ni”.
Amru bn Abasata sai ya koma
garinsu yana bibiyar labarin manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam har
sai da ya ji zuwan sa Madina da
yadda Allah ya daukaka shi sannan
ya zo ya same shi. Da suka hada
fuska sai ya ce ma manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam “Ko ka
sheda ni?” Manzon Allah ya ce,
kwarai kuwa. Ai kai ne ka same ni a
Makka. Sannan sai manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya koya
ma sa yadda ake sallah da lokutanta
kuma ya sanar da shi falalarta. Sahih
Muslim, hadisi na 832.
Amru bn Abasata yakan ce ni ne na 4
a shiga musulunci. Domin ya fahimci
waccan magana ta manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam “akwai da,
akwai kuma bawa” a matsayin cewa,
mutum 2 kawai ke tare da shi, manzo
shi ne na ukunsu. Alhalin kuwa a
daidai lokacin da ya musulunta
adadin musulmi na da yawa matuka
amma suna cikin rauni sosai. Don
haka daga cikin siyasar manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ba ya
bayyana adadinsu da sunayensu
saboda dalilai na tsaro. As-Sirah An-
Nabawiyyah, na Ibn Kathir (1/443).
Daga cikin darussan wannan karatu
mun lura masu tsarkin zukata
wadanda suka fi kusa da fitira irin
shi wannan bawan Allah su ne suka
fi saukin fahimtar gaskiya da kuma
karbar ta. Dubi yadda ya rinka kula
da bin labarin manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam har inda
ya gano lokacin da ya yi hijira da
inda ya tafi sa’annan ya bi shi ya
koyi addini. Haka kuma mun ga irin
halin matsatsi da musulmi suke ciki
a wancan lokaci wanda har ya sa
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam yana gudun ajiye baki da
ke son su zauna wurin sa su koyi
musulunci. Ga kuma yadda manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yake
kula da fahimtar masu zuwa wurin sa
kuma ya sheda su kome dadewar
lokaci. Amsar da manzon Allah ya ba
shi a lokacin da ya tambaye shi “Da
me Allah ya aiko ka?” Ita ce: “Ya aiko
ni da sada zumunta, da karya
gumaka”. Don haka addini hakke biyu
ne; na Allah da na bayinsa. Duk
wanda ya tozarta daya to babu
shakka ya samu tawaya a addininsa.
Allah muke roko ya inganta
imaninmu.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s