ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 55( Dr. Mansur Sokoto)


Musulmi Sun Ci Gaba Da Fuskantar
Wulakanci
Jarrabawa sunnar Allah ce da take
tare da ma’abuta gaskiya a duk inda
suka kasance. Da ita ne Allah yake
rarrabe masu addini da gaskiya da
munafukai masu yin sa kawai don
holewa da jin dadi. Haka kuma
babbar makaranta ce da take horar
da mazaje a kan hakuri da jarunta da
sadaukarwa. Ga wadanda suka
dandane ta ba abin da ya kai
jarabawa dadi saboda tsarkake
zuciya da kaifafa imani da take yi.
Sahabban manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam sun gamu da
jarabawa matuka a farkon al’amari.
Ka daina zancen masu rauni daga
cikin su kamar bayi da marasa
galihu. Manyansu ma ba a bar su
suka sarara ba. Misalinmu na yau a
kan mashahurin dan kasuwa ne,
dattijo, mai abin hannunsa. Amma
saboda kusancinsa da manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam mushrikai
ba su bar shi ba. Wannan dattijo shi
ne babban na hannun daman manzon
Allah; Abubakar Siddiq.
A lokacin da adadin musulmi ya kai
38 sayyadi Abubakar Radhiyallahu
Anhu ya samu manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam yana ba
da shawarar a fito fili ayi da’awa. Sai
ya ce ma sa, “Ya Abubakar! Mu fa
har yanzu ‘yan kadan ne”. Amma
Abubakar bai gushe ba yana nuna
ma sa muhimmancin fitowar har sai
da manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya amince. Musulmi sun
san da wannan shiri da aka yi. Don
haka, a ranar da za a zartar da
wannan shiri kowanensu ya koma
cikin danginsa ya yi garkuwa da su.
A daidai lokacin da masallaci ya cika
ginjim da mutane sai kawai aka ga
sayyidina Abubakar ya mike tsaye – a
lokacin shi kuma manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam yana
zaune. Abubakar ya ce, ya ku jama’a!
Ku bi Allah, ku bi manzonsa. Rufe
bakinsa ke da wuya sai arna suka yo
cah a kan sa. Wasu na dukan sa da
takalmi, wasu da duwatsu, wasu
kuma da duk abinda suka samu iko,
har suka kai shi kasa. Utbatu dan
Rabi’ata ya dare a kan cikinsa yana
dukansa da tsinin takalmansa a fuska
har sai da fuskarsa ta cabe da jini.
Banu Bakr – dangin Abubakar – suka
dauke shi uzurce, ba sa tsammanin
yana da sauran numfashi har suka
kai shi gidansa. Nan take kuma suka
kulla mitin a tsakanin su suka yi
ijma’i a kan cewa, idan ya cika za su
kashe Utbatu duk kuwa abin da
hakan zai iya janyowa. Suka fito fili
suka shelanta haka a bainar jama’a.
Abu Quhafata, mahaifin Abubakar ya
shiga damuwa matuka duk da yake a
lokacin bai musulunta ba. Amma
yana juyayin abin da ya cim ma
dansa. Ga kuma fitinar da hakan za
ta haifar a tsakanin Quraishawa. Can
bayan wani lokaci sai aka samu
Abubakar ya fara jin sauki har yana
son ya yi magana. Da ya samu ikon
buda bakinsa abu na farko da ya ce
shine, ina manzon Allah? Ba wanda
ya iya ba shi amsa a cikin su. Sai
Ummul-Khair mahaifiyarsa ta nace
sai ya ci abinci. Shi kuma ya yi
rantsuwa ba abin da zai shiga
bakinsa sai ya ji labarin manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. Da
mahaifiyarsa ta nuna ma sa ba ta da
masaniya sai ya ce ma ta ki je wajen
Ummu-Jamil bint Al-Khattab –
kanwar Umar – za ta ba ki labari.
Ummu-Jamil ba ta yarda ta ce komai
game da manzon Allah ba don ba ta
san manufar tambayar ba. Amma sai
ta yi dabara. Ta ce, idan kina so mu
je in duba dan naki. Hankalin Ummu-
Jamil ya tashi matuka ganin irin halin
da ta tarar da Abubakar. Ba ta san
lokacin da ta rusa kuka ba har da
hargowa tana la’antar Utbatu da
wadanda suka goyu bayan shi.
Sa’annan sai ya tambaye ta labarin
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam. Sai ta ce ma sa, ga
ummarka nan tana jin ka. Ya ce, kar
ki damu da ita. Gaya mini kawai. Sai
ta ce, lafiyarsa kalau. “A ina yake?”
Ya tambaye ta. Ta ce, “A Darul
Arqam”. Ya kalli mamarsa ya ce ma
ta wallahi kome ba zan ci ko in sha
ba sai na ga manzon Allah. Nan take
suka yi shawarar a saurara har sai
dare ya yi, kafafu sun dauke. Sannan
su biyun suka dauke shi yana dogara
ga kafadunsu har suka zo da shi
gidan Arqam wurin manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam. Manzon
Allah kuwa ya nuna alhininsa matuka,
sannan ya rungume shi, ya sumbace
shi. Musulmi suka taso suna ta ba
shi hakuri. Abubakar ya tabbatar ma
su da cewa wannan ba komai ba ne a
bisa tafarkin Allah. Sannan ya roki
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam yana mai cewa, ga uwata
nan ya manzon Allah. Tana so na
matuka, kuma tana kyautata min. Kai
kuma mutum ne mai albarka. Ka kira
ta zuwa ga musulunci sannan ka yi
ma ta addu’a ko Allah zai sa ta
rabauta, ta kubuta daga wuta.
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya yi ma ta wa’azi kuma a
nan wurin ba ta daga ba sai da ta
musulunta. Duba: As-Sirah an-
Nabawiyyah, na Ibn Kathir
(1/439-440) da Al-Bidayah Wan-
Nihaya, (3/30) da kuma Mihnatul
Muslimin fil Ahd Al-Makki, na Dr.
Sulaiman as-Suwaikit, shafi na 79.
Ka ji mazaje masu imani, masu kishin
bayyanar addini, da sadaukarwa a
kan sa. Ka ga kuma yadda son
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya kama zuciyar wannan
mutum har ba ya iya cin abinci ko ya
sha ruwa bayan duk wannan azabar
da ya sha sai ya ga masoyin nasa, ya
samu natsuwa a kan lafiyarsa. Babu
shakka musulmi a wancan lokaci
mutane ne masu kaifin basira. Kana
iya gane haka in ka dubi matakan da
Ummu-Jamil kanwar Umar ta dauka.
Ba ta fada ma Ummul-Khairi kome ba
game da manzon Allah tun da ba ta
san niyyarta ba, amma kuma sai ta yi
dabarar zuwa da kanta wajen sa. A
nan ma sai da ta yi taka-tsantsan
wajen ba da amsar tambayarsa.
Kuma a cikin kukan da ta yi da
la’antar kafirai akwai jan hankalin
Ummul-Khair don ta gane bacin
tafarkinsu. Haka kuma saurarawar da
suka yi har dare ya yi, kafafu suka
dauke. Dabara ce wacce take da
muhimmanci. Domin wurin da
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam yake tare da sahabbansa
wani sirri ne da bai dace a daidai
wannan lokaci a tona shi ba. Shi
kuma sayyadi Abubakar wannan halin
da yake ciki bai hana shi nuna
fatarsa na shiriya ga mahaifiyarsa ba.
Kuma sai Allah cikin rahamarsa ya sa
aka dace.
To, idan irin wannan babban mutum,
dattijo, mai yawan alheri, mai kwarjini
da karbuwa ga jama’a an yi ma sa
haka. Ya kake zato ga bayin Allah
marasa galihu, masu rauni?
Za mu ji sashen jarrabawar da wasun
su suka sha in Allah ya so.
Mu kwana lafiya.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s