AQIIDAR SHEIK BIN BAZ DA SAURAN AHLUS SUNNAH GAME DA RUQYAH DA YIN MAGANA DA ALJANI: 17/2/1435 H 20/12/2013 M(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)


Wani dan’uwa ya tambaye mu cewa:
Ko mene ne aqiidar marigayi
Sheik Abdulaziz Bin Baz shugaban
majalisar malamai ta Saudiyya game
da Ruqyah da kuma yiwuwar a yi
magana da aljani ta harshen mutum?
Mutumin ya ce ya yi wannan
tambayar ce saboda ya ji wasu
malaman na cewa hakan kfirci ne
kuma bokanci ne!
AMSA:
Gaskiya ne Muutazilaawa da Shi’ah
Raafidhah da ‘Yan dogara da hankali
sun tafi a kan cewa ba zai yiwu ba
sam a ce aljani na iya shiga cikin
jikin mutum, ballantana ma a ce wai
wani mutum zai iya yin magana da
aljanin ta harshen wanda aljanin ya
shige shi, su wadannan kungiyoyin
bidi’ah suna ganin masu yarda da
hakan a matsayin wasu bokaye ko
ma wasu kafirai. Amma su Ahlus
Sunnah Wal Jama’ah, saboda dogara
da Alkur’ani da Sunnah da suke yi, su
sun yi imani da cewa: aljani na iya
shiga cikin jikin mutum saboda ya
cutar da shi, haka nan kuma sun
yarda da cewa: mutum na iya
magana da aljani ta harshen wanda
aljanin ya shige shi.
Lalle da yake shi Sheik Abdul-Azizi
Bin Abdullah Bin Baz yana daga cikin
shugabannin Ahlus Sunnah Wal
Jama’ah na Duniya, lalle wannan shi
ne aqiidarsa shi ma, ga ma abin da
yake cewa cikin littafinsa mai suna:
Iidhaahul Haqqi Fii Dukhuulil Jinniyyi
Fil Insiyyi shafi na 6-7:-
{ ﺗﻠﺒﺲ ﺍﻟﺠﻦ ﺑﺒﻌﺾ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﺎﺕ ﻓﻲ ﺍﻟﺮﻳﺎﺽ ﻓﻘﺮﺍ
ﻋﻠﻴﻪ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻤﺸﺎﻳﺦ ﻭﺫﻛﺮ ﺍﻟﺠﻨﻲ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻭﻭﻋﻈﻪ
ﻭﺍﺧﺒﺮﻩ ﺑﺎﻥ ﺍﻟﻈﻠﻢ ﺣﺮﺍﻡ ﻭﻛﺒﻴﺮﺓ ﻋﻈﻴﻤﺔ، ﻭﺩﻋﺎﻩ ﺍﻟﻰ
ﺍﻻﺳﻼﻡ ﻓﺎﺳﻠﻢ، ﺛﻢ ﺟﺎﺀﻭﺍ ﻋﻨﺪﻱ ﺑﺎﻟﻤﺮﺍﺓ ﻓﺴﺎﻟﺘﻪ ﻋﻦ
ﺍﺳﺒﺎﺏ ﺩﺧﻮﻟﻪ ﻓﻴﻬﺎ ﻓﺎﺧﺒﺮﻧﻲ ﺑﺎﻻﺳﺒﺎﺏ ﻭﻧﻄﻖ
ﺑﻠﺴﺎﻥ ﺍﻟﻤﺮﺍﺓ ﻟﻜﻨﻪ ﻛﻼﻡ ﺭﺟﻞ ﻭﻟﻴﺲ ﻛﻼﻡ ﺍﻣﺮﺍﺓ،
ﻭﻫﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻜﺮﺳﻲ ﺍﻟﺬﻱ ﺑﺠﻮﺍﺭﻱ ﻭﺍﺧﻮﻫﺎ ﻭﺍﺧﺘﻬﺎ
ﻭﺑﻌﺾ ﺍﻟﻤﺸﺎﻳﺦ ﻳﺸﻬﺪﻭﻥ ﺫﻟﻚ ﻭﻳﺴﻤﻌﻮﻥ ﻛﻼﻡ
ﺍﻟﺠﻨﻲ ﻭﻗﺪ ﺍﻋﻠﻦ ﺍﺳﻼﻣﻪ ﺻﺮﻳﺤﺎ، ﻓﻨﺼﺤﺘﻪ ﻭﺍﻭﺻﻴﺘﻪ
ﺑﺘﻘﻮﻯ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻳﺨﺮﺝ ﻣﻦ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻤﺮﺍﺓ ﻭﻳﺒﺘﻌﺪ ﻋﻦ
ﻇﻠﻤﻬﺎ ﻓﺎﺟﺎﺑﻨﻲ ﺍﻟﻰ ﺫﻟﻚ ﻭﻗﺎﻝ : ﺍﻧﺎ ﻣﻘﺘﻨﻊ
ﺑﺎﻻﺳﻼﻡ، ﻭﻏﺎﺩﺭ ﺍﻟﻤﺮﺍﺓ ﺍﻟﻤﺬﻛﻮﺭﺓ ﺑﻠﺴﺎﻧﻬﺎ ﺍﻟﻤﻌﺘﺎﺩ
ﻭﺷﻌﺮﺕ ﺑﺴﻼﻣﺘﻬﺎ ﻭﺭﺍﺣﺘﻬﺎ ﻣﻦ ﺗﻌﺒﻪ، ﺛﻢ ﻋﺎﺩﺕ
ﺍﻟﻲ ﺑﻌﺪ ﺷﻬﺮ ﻭﺍﺧﺒﺮﺗﻨﻲ ﺑﺎﻧﻬﺎ ﺑﺨﻴﺮ ﻭﻋﺎﻓﻴﺔ .{
ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Aljani ya cakuda da sashin
wasu mata musulmi a Riyadh sai
sashin malamai ya yi masa karatu, ya
tunatar da aljanin girman Allah, ya yi
masa wa’azi, ya ba shi labarin cewa
zalunci haramun ne kuma zunubi ne
mai girma, kuma ya kira shi zuwa ga
Musulunci ya musulunta, sannan sai
suka zo wajena tare da matar na
tambaye shi dalilan shigarsa cikinta,
ya gaya mini dalilan, ya yi magana a
bisa harshen matar sai dai maganar
namiji ne ba maganar mace ba, ita
kuwa tana zaune cikin kujera a kusa
da ni, dan’uwanta da ‘yar’uwarta da
sashin wasu maluma suna shaidar
haka suna kuma jin maganar aljanin,
alhalin ya bayyanar da shiga
musuluncinsa a fili, sai na yi masa
nasiha, na yi masa wasiyyar ya ji
tsoron Allah ya fita daga wannan
matar, ya nisanci zaluntar ta, sai ya
amsa mini zuwa ga hakan ya ce: Ni
na gamsu da Musulunci, ya bar
matar da aka ambata ta harshenta
wanda aka sani, ta kuma fahimci
lafiyarta da samun hutunta daga
gajiyar da ya sa mata, sannan ta
dawo wurina bayan wata guda ta
gaya mini cewa tana cikin alheri da
lafiya)). Intaha.
Muna rokon Allah Ya tabbatar da
dugaduganmu a kan sunnar Annabi
mai tsira da amincin Allah, Ya raba
mu da fadawa cikin sharrin yan
bidi’ah. Ameen.

Advertisements

One thought on “AQIIDAR SHEIK BIN BAZ DA SAURAN AHLUS SUNNAH GAME DA RUQYAH DA YIN MAGANA DA ALJANI: 17/2/1435 H 20/12/2013 M(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s