ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 58( Dr. Mansur Sokoto)


Musulmi Suna Ci Gaba Da Juriya
2. Khalid bn Sa’id bn Al-Ass:
Wani bawan Allah ne saurayi da Allah
ya nufe shi da samun shiriya tun da
wuri. A cikin bacci ya yi mafarkin
yana kan gabar wuta. Ga wasu
mutane suna ta kokarin ingiza shi.
Shi kuma Muhammadu Sallallahu
Alaihi Wasallam yana rirrike shi yana
hana shi afkawa a ciki. Ko da ya
farka a tsorace sai ya nufi wajen
sayyidi Abubakar a matsayinsa na
aboki kuma makusancin manzon
Allah, ya kwashe labarin mafarkinsa
ya fada ma sa. Abubakar (RA) ya ce
ma sa, kaiconka! Wallahi Allah na
nufin alheri gare ka. Mu je in kai ka
wurin manzon Allah. Da suka je ya
saurari alkur’ani sai ya musulunta.
Amma saboda irin halin da ake ciki
sai ya boye musuluncinsa kamar
yadda sauran musulmi a wannan
lokaci suke yi. Yau da gobe mahaifin
Khalid ya ji kamshin wainar da ake
toyawa don ya ga dabi’unsa sun
canja kuma yanzu ba koyaushe ne
ake sanin in da ya tafi ba. Sai ya sa
ma sa ‘yan leken asiri wadanda suka
tabbatar ma sa inda dan nasa yake
zuwa. Ya kuwa yi ma sa fada matuka
har ya kai ga dukan sa da wata
sanda wadda ya kakkarya ta a kan
sa. Daga bisani ya daure shi a gida
kuma ya hana mutanen gida su yi
magana da shi. Khalid yana ta hakuri
yana kai kukansa zuwa ga Allah. Da
Sa’id ya kasa shawo kan dansa ya
bar musulunci ya koma ga addinin
gado sai ya dauki wani mataki na
gaba. Shi ne matakin hana shi
abinci. Sai da ya kwana uku ba tare
da an ba shi ko kurbin ruwa ya sa a
bakinsa ba. Sannan mahaifinsa ya ga
babu makawa ga barin sa, sai ya
sake shi. Daga nan ya kara sakin
jikinsa a wurin manzon Allah.
Manzon Allah yana darajanta Khalid a
kan hakurinsa da karfin imaninsa.
Daga bisani Khalid na cikin wadanda
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya tura su gudun hijira don
kariyar lafiyarsu da imaninsu da
kuma samar ma su da isasshiyar
horarwa don fuskantar matakin da
yake tafe wanda yake bukatar jan
damara a nan gaba.
Duba labarin Khalid a cikin Siyar
A’alam An Nubala’ na Dhahabi
(1/260).

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s