ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 59( Dr. Mansur Sokoto)


Har Wayau Dai A Kan Musulmin
Farko
3. Mus’ab Bn Umair:
Wani yaro ne matashi a garin Makka.
Sagartacce ne, dan gata. Iyayensa
suna ji da shi matuka, kuma suna
nuna ma sa so na kin karawa. Ga su
masu arziki da wadata. Ba wani
matashi a garin Makka wanda ya kai
kyawon tufansa ko kanshin
turarensa. Kai, ko takalmansa ma
abin kallo ne. Ta fuskar abinci shi
bai ma san ana dumame ba. Ana
haka sai Allah ya jefa musulunci a
zuciyarsa. Ya kuwa tafi har Darul
Arqam ya musulunta. Musuluncinsa
ya kasa boyuwa har iyayensa suka
tsare shi cikin gida suka hana shi
zuwa ko ina. Kuma duk da irin son
da suke yi ma sa amma a kan
musulunci sun nuna ma sa rashin
imani matuka. Suka sanya shi a wani
hali na ban tausayi. Bai samu kansa
ba sai da manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya shirya ayarin
masu gudun hijira sannan Mus’ab ya
sulale ya bi su. A kan hanyar su ta
zuwa Habasha an ba da labarin
yadda ya sha wuya kasancewar babu
wani guzuri a tare da shi. Amma
kuma ‘yan uwansa sahabbai sun
tausaya ma sa, tare da tallafa ma sa
da iya dan abinda suke da shi.
Bayan da ya dawo daga makarantar
Habasha ne manzon Allah ya nada
shi jakada na farko zuwa birnin
Madina in da ya yi amfani da hikima
ya nuna kwarewa wajen kira zuwa ga
musulunci da kyakkyawan salo wajen
isar da sakonsa.
Mus’ab ya samu shahada a yakin
Uhud bai san wani jin dadi na duniya
ba tun bayan wanda ya yi bankwana
da shi da ya karbi musulunci. A
lokacin da ya cika bai mallaki ko rigar
da za ta wadace shi a matsayin
likkafani ba.
Bayan da Allah ya yi ma sahabbai
budi, aka samu wadatar rayuwa da
yawa daga cikin su sukan tuna
Mus’ab sai su fashe da kuka. Me ya
sa? Sukan ce, Mus’ab ya wuce bai ci
kome cikin ladar aikinsa ba. Muna
tsoron kada ya zamo ladar jihadinmu
ce muke cinyewa.
Allah sarki! Sahabbai ladarku tana
wurin Allah. Mene ne kuka ci a
wannan duniya, ku da ba fanka bale
A.C. Babu ruwan firijin, ba wutar
lantarki. Babu sauran kayan alatu da
jin dadi?! Bayan duk azabar da kuka
sha a hannun kafirai kun taimaki
manzo Allah, kun ba da duk abinda
kuka mallaka wajen kafa addininsa.
Wuta kuma Allah da kansa ya ce kun
kubuta daga gare ta:
” ﻭﻛﻨﺘﻢ ﻋﻠﯽ ﺷﻔﺎ ﺣﻔﺮﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺭ ﻓﺄﻧﻘﺬﻛﻢ ﻣﻨﻬﺎ ”
“Kun kasance a kan gabar wuta sai
(Allah) ya kubutar da ku daga gare
ta” Suratu Ali Imran: 103.
Mus’ab ya kamata ya zama abin koyi
ga duk wani saurayi da yake cikin
lokacinsa. Samun yardar Allah ya fi
samun abin duniya. In da uwayensa
sun san irin daukakar duniya da ta
lahira da ya samu a kan hakurinsa da
ba su takura ma sa yadda suka yi ba.
Amma shiriya haske ne da Allah yake
jefa shi a cikin zukatan wadanda ya
zaba daga cikin bayinsa.
Ya Allah! Ka yi muna rabo da arzikin
samun shiriya da tabbatuwa a kan ta
har mai karar da jin dadi – kuma mai
sadar da mummunai zuwa ga jin dadi
– ta cim mana.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s