ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Majalisi Na 61( Dr. Mansur Sokoto)


Abdullahi Bn Mas’ud
A can baya mun ga yadda wannan
sahabi ya bayyana irin halin da ake
ciki a garin Makka, in da ya ce babu
wanda ya kubuta daga cikin musulmi
daga shan azaba a hannun
mushrikai. To, shi ma din kansa fa
bai kubuta daga shan azabar ba.
Sanadiyyar musuluntar Abdullahi bn
Mas’ud tana komawa ne ga tsarkin
zuciyarsa da kyawon halinsa. A
lokacin yana yaro karami ne Uqbatu
bn Abi Mu’ait ya sa shi kiwon tumaki.
Watarana yana kiwon sa sai manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam tare
da rakkiyar Abubakar suka bi ta wurin
sa. Sai manzon Allah ya ce ma sa,
yaro ko ana samun madara a
wurinka? Sai ya ce, eh. Akwai madara
bawan Allah. Amma fa ni ba kayana
ne ba, kiwo aka ba ni. Sai manzon
Allah ya ce ma sa to, nuna ma ni
tunkiyar da ba a fara barbararta ba.
Ma’ana wacce ba ta ma san zancen
daukar ciki ba balle ayi maganar
haifuwa da shayarwa. Sai Ibnu
Mas’ud ya je ya kamo ma sa wata
‘yar budurwar tunkiya. Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam sai ya
shafi hantsarta, nan take ta dararo da
madara, suka diba a wata kwarya
suka sha suka koshi. Sai ya ce da
hantsarta, ki dakata. Nan take sai
madarar ta dauke. Ganin wannan
abin al’ajabi ya sa, Ibn Mas’ud ya
biyo manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya ce ma sa koya min irin
wannan karatun naka. Sai manzon
Allah ya yi murmushi, ya shafi kansa,
ya ce, “Allah ya jikanka. Ai kai yaro
ne sa’ar daukar karatu”. Al-Bidaya
Wan-Nihaya na Ibn Kathir (3/32) da
Siyar A’alam An-Nubala’ na Dhahabi
(1/465).
Ibn Mas’ud ya kasance mutum ne
mai dan karamin jiki sosai, mai ‘yan
kananan kafafu. Amma wannan
kankanin jikin nasa a cike yake da
imani makil. Don shi ne mutum na
farko da ya bayyana karatun Alkur’ani
a garin Makka bayan manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam. Haka
kawai kuwa a cikin tadi wasu
sahabbai suka ce, jama’a fa
Quraishawa ba su taba jin an karanta
ma su littafin Allah mai albarka a fili
ba. Ko a cikin mu akwai wanda zai
iya fitowa ya karanta ma su? Ibn
Mas’ud ya ce, ni zan yi. Suka ce ma
sa, haba! Wane kai. Muna son wanda
idan an taba shi gidansu za a tada
jijiya. Ya ce, ku dai bari ku gani. Sai
kuwa ya je daidai Ka’aba in da kowa
da kowa ke haduwa. Kulob-kulob
dinsu ana ta ma-sha-a da shan giya.
Sai ya fara tilawar Suratur Rahman.
Da farko hankalinsu bai gaskata
cewa Qur’ani ne yake karantawa ba
saboda ba su tsammanin haka.
Amma da suka ahamo sai suka bi shi
da duka har suka yamutsa fuskarsa.
Sahabbai suka ce, ka ga abin da
muka ji ma ka tsoro kenan. Abdullahi
ya ce, wallahi ban taba jin an cire
min tsoron su ba kamar yanzu. Kuma
ko gobe ma zan iya kara wa. Suka
ce, a’a. Don Allah ka bari. Haka ma
ya isa. Ai ko yanzu sun ji abinda ba
sa so kuma suke fargaba. Usd Al-
Gaba na Ibn Al-Athir (3/385-386).
Duba kuma Mihnat Al-Muslimeen Fi
Al-Ahd Al-Makkee, na Suwaikit, shafi
na 88.
Daga nan mai karatu zai fahimci irin
nau’in mutanen da suka amshi
musulunci tun da farko. Zababbu ne,
masu hankali, amintattu, wadanda
Allah ya gwada ma su karamomin
habibinsa shugaban talikai Sallallahu
Alaihi wasallam. Suka kuwa bi shi bil
hakki suna masu neman yardar Allah.
To, bayan shekaru 23 suna dibar
karatu a wurin sa da tarbiyya kuma
sun yi jihadi tare da shi wajen tsayar
da addinin Allah haka kwatsam su yi
ridda! Wai da sunan suna kyamar
wanda yake so ya nada ma su a
matsayin wanda zai gaje shi daga
cikin su? Wannan maganar wane irin
hankali yake karbar ta?

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s