SUNAN ALLAH.MAFI GIRMA (ISMULLAH AL’A’AZAM)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)


Allah subhanahu-wata’ala yana da sunaye, mafi kyau ku kirashi da su,
bincike akan sunan Allah subhanahu-wata’ala mafi girma, yana tukewa cikin hadisai guda hudu, wanda Annabi saw ya ambata,
acikin wadannan hadisai, an sami sunayen Allah subhanahu-wata’ala guda goma sha daya, acikin su, sunan Allah subhanahu-wata’ala mafi girma yake, don haka malamai suka ce, duk sanda za kayi roko ko Neman wata bukata, ka fara yiwa Allah subhanahu-wata’ala kirari, da kamun kafa da fadanci, da wadannan sunaye goma sha daya, domin ragowar sunayen Alllah, suna komawa zuwa garesu,
Sune:
1- Allah
2- Alwahidu
3- Al’ahadu
4- Assamadu
5- Al’Hayyu
6- Al’Qayyumu
7- Arrahmanu
8- Arraheemu
9- Al’Mannaanu
10- Badius-samawati. Wal-ardi
11 Zul jalaali, Wal ikram
Wadannnan sunaye na Alllah sune, wadanda bincike ya tabbatar, mafi girman sunan Allah subhanahu-wata’ala , Ya Allah, muna ta wassali, da fadanci, da kirari, da roko da su, ka biya mana bukatun mu na alkhairi duniya, da lahira, ka daukaka musulunci da musulmi, ka karya kafirci da kafurai da munafukai, ka tabbatar damu, akan tafarkin Annabi saw da sahabbansa, kasa mu cika da imani, ka samu cikin ceton Annabi saw.

Advertisements

5 thoughts on “SUNAN ALLAH.MAFI GIRMA (ISMULLAH AL’A’AZAM)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

  1. Pingback: SUNAN ALLAH.MAFI GIRMA (ISMULLAH AL’A’AZAM)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa) | sijangebii's Blog

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s