Alamomin tashin Al-kiyamah guda ‘Dari 100 kashi na ‘daya (1)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)


Alqiyamah ta kusanto, ga wa su daga cikin Alamomin ta, wasu sun faru, wasu suna faruwa, wasu za su faru nan gaba
Alamomi 001-100
1. Aiko Annabi (sallallahu-alaihi-wasallam) {ranar litinin, 21/Ramadan/0013bh daidai da 10/August/610m} yana shekara arba’in 40 da wata shida 6 da kwana goma sha biyu 12 lissafin wata/ shekara talatin da tara 39 wata uku 3 da kwana ishirin 20
2. Wafatin Manzon Allah (sallallahu-alaihi-wasallam) ranar litinin 12/rabi’ul-Auwal/11ah yana da shekara sittin da uku da kwana hu’du
3. Tsagewar wata
4. ‘Karewar Sahabbai
5. Bu’de Baitil-Maqdis
6. ‘Barkewar Annoba;- mai kama da ciwon dabbobi
7. Bayyanar fitintunu masu yawa
8. Bapyyanar tashoshin tauraron ‘Dan Adam
9. Yaqin Siffaini
10. Bayyanar khawarij
11. Masu da’awar Annabta ta qarya
12. Yalwatar Arzi’ki;- Arzi’ki zai yalwata
13. Bayyanar wuta a Hijaz, dutse mai aman wuta
14. Ya’ki da turkawa
15. Bayyanar Azzalumai masu dukan babu dalili
16. Yawan zubar da jini;- kashe-kashe
17. ‘Dauke Amana;- ma su Amana za suyi ‘karanci
18. Koyi da Yahudu da Nasara
19. Baiwa za ta haifi uwargijiyar ta
20. Bayyanar masu masu tsirara-tsirara (ba sa shiga ta addini)
21. Matsiya ta, Matasa takalma masu kiwon awaki, za su yi yin dogayen gine-gine
22. Yin Sallama ga wanda aka sani kawai;- mutane za su daina yi wa mutum Sallama sai sun san shi
23. Ya’duwar kasuwanci;- ko ina zai zama kasuwa
24. Mata za suyi tarayya da mazan su a kasuwanci
25. Wasu tsirarun ‘yan kasuwa za su mamaye kasuwanci;- ya zama ba ayi da kai sai da yardar su
26. Shaidar Zur
27. ‘Boye shaidar gaskiya
28. Yawan Rowa;- mutane za su zama marowata
29. Yanke zumunta
30. Munana maqotaka
31. Ya’duwar laifuffuka
32. Bayyanar jahilci
33. Amincewa maha’inci, da tuhumar mai Amana
34. Mutuwar Mutanen ‘kwarai da Ya’duwar lalatattu
35. Yaki Halal Yaki Haram
36. Rubda ciki akan Baitil-Mali (Asusun-gwamnati)
37. Mayar da dukiyar Amana ganimah
38. Rashin fitar da Zakkah da da’din rai;- mutum ya ga zakka kamar Asara Ce yayi
39. Yin Karatu dan Neman Abun duniya
40. Yi wa mata biyayya da sa’bawa Uwa
41. Fifita Abokai/’Kawaye akan iyaye
42. Hayaniya a masallatai
43. Mafi yawan shuwagabannin Al’ummah za su zama fasiqai
44. ‘Kas’kantattu za su zama manyan gari
45. Girmama mutum don tsoron sharrin sa
46. Za a halatta Zina
47. Halatta Alhariri ga Maza (sa Alhariri ga maza haramun ne, amma za ayi zamanin da za a halatta shi
48. Ya’duwar Kayan maye
49. Ka’de ka’de da raye-raye za su mamaye Al’ummah
50. Masifa da Bala’i za su yi wa Har mutum ya dinga fatan mutuwa
51. Wani Zamani da mutum zai kwana Mumini ya wuni kafiri;- saboda mafi yawan maganganu da aiyuka da ba sa kan Shari’ah
52. ‘Kawata Masallatai da yin gasar Hakan (kaji ana Masallacin mu yafi naku kyau)
53. ‘Kawata gidaje da yi musu kwalliya
54. Yawan Saukar Kwarankwatsa da Aradu
55. Yawan Rubuce-Rubuce;- Ya’duwar Rubutuce-Rubuce marasa amfani (jaridu da mujallu, da littafai da internet) ba a tunanin amfanin rubutun kawai da an rubuta
56. Wanda suka ‘kware a ro’ko da ziga, su suka fi samun ku’di
57. Za shagala da karanta wasu abubuwa a bar Al’qur’ani
58. ‘Karancin Malaman fi’khu da yawan Gardawa
59. Neman Ilimi a wajen ‘kananan mutane;- ‘karamin Mutum wanda ba ya aiki da ilimin sa
60. Yawan mutuwar ba-zata
61. Shugabancin Wawaye (kuma suna ganin kan su wayaiyu)
62. Lokaci zai dinga sauri
63. Banzaye za su mamaye kafafan ya’da labarai;- Mutumin da ba kowa ba, kuma bai zan komai ba, zai dinga magana kan abubuwan da suka shafi Al’ummah
64. Ma’daukaki a duniya shine banza ‘dan banza;- kaga ana ta rububin wani wanda bai da amfanin komai saboda wani shirme da yake Misali;- ‘Yan Bal da Mawa’ka
65. Mai da cikin masallatai Hanyoyi
66. Sadakin Aure zai yi tsada, sai kuma ya zo yai arha
67. Dawakai za su yi tsada sai kuma su zo su yi arha
68. Kasuwanci zai yi sau’ki (ta yadda zaka sai Abu ko ka sayar daga ‘dakin ka, ba tare da ka je ko ina ba) Misali;- yanar gizo
69. Kafiran duniya za su yi taron dangi akan musulmi
70. Mutane za su dinga gudun limanci a cikin Sallah (saboda ba cikakken Albashi)
71. Aukuwar Mafarkin Mumini (in Mumini yai mafarki sai Abu ya faru
72. Yawan ‘karaya
73. yawan gaba
74. Girgizar ‘kasa
75. Yawan Mata
76. ‘Karancin Maza
77. Aikata Sa’bo a filigahh
78. Mai da karatun Al’qur’ani hanyar Neman ku’di
79. ‘Kiba, mutane za su yi ta ‘kiba mai yawa
80. Bayyanar mutane masu yin shaida tun ba a tambaye su ba
81. Masu Bakance ba sa cikawa
82. Masu ‘karfi za su danne raunana
83.’Rashin Hukunci da Alqur’ani
84. Yawan rumawa da ‘karancin larabawa
85. Ya’duwar ku’di
86. ‘Kasa za ta fitar da taskokin ta
87. MòZa a dinga shafe halittar wasu mutane suna komawa wata 88.Halitta daban
89. Tsagewar ‘kasa, ta ha’diye mutane
90. Wasu ‘kwarangwazai, duwatsun da ba a San su ba za su dinga 91. fa’dowa mutane aka
92. Yawan ambaliyar ruwa
93. Ruwan ‘bala’i;- wanda ba ya fidda shuka ko tsiWwFitina da za ta 93.wata fitina za ta’barke tsakanin larabawa Har ta kusa ‘karar da su
94. Bishiya za ta yi magana don taimakawa musulmi
95. Dutse zai magana don taimakawa musulmi
96. Ya’kin Musulmi da Yahudu
97. Kogin furat zai ‘kafe, a hango Dutsen Gwal a ciki
98. Zamanin da za a yiwa masu addini kallon ba wayayyu ba
99. ‘Kasashen larabawa za su samu ci-gaba mai yawa
100.Bayyanar wata Babbar fitina da zata shafi kowa
Mu ha’du a darasi na gaba
Allah ya kare mu sharrin fitintunu

Advertisements

4 thoughts on “Alamomin tashin Al-kiyamah guda ‘Dari 100 kashi na ‘daya (1)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

  1. ALLAH YA SAKA DA ALHERI YA KARA SANI DA IKON SANARWA,DOMIN KARUWAR “YAN UWA MUSULMI.MUN GODE,MUN GODE,MUN GODE.

  2. Allahu akbar Allah kadaukaka musulunci da musulmai aduk inda muke kuma kakare mana malamammu na sunnah

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s