BABBAN ARZIKI(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa Page)


Babbabn arziki shine,
Na daya : Son Allah, girmama Allah,
kwadayin rahmar Allah, Tsoran
Azabar Allah, a Bautawa Allah da
iklasi, akan tafarkin manzon tsira,
Na biyu : Son Annabi saw, Girmama
shi, biyayya a gareshi, ( Aqidarka, da
ibadarka, da halayenka, da
mu’amalarka, duk kayi koyi da
Annabi saw, fili da boye, zahiri da
badini,)
Na uku : ka yarda ka amince duk
abinda ya sameka mai dadi da mara
dadi duk daga Allah ne,
Na hudu : ka dinka kallon na kasa
dakai a harkar duniya, na sama da kai
a harkar lahira,
Na biyar : duk abinda zaka ci ko ka
sha, ko ka daura, ka tabbatar halal ne.
Na shida : duk abinda zakayi ka
tabbatar kana da hujja, da zaka kare
kanka a gaban Allah taala ranar
alkiyama
.
Na bakwai : Duk sanda abin duniya
dana lahira suka ci karo, ka fifita na
lahira akan na duniya,
Na takwas : kaso ma dan uwan ka
musulmi abinda kake sowa kanka na
alkhairi.
Na tara : Idan zakayi magana ko
rubutu, ka fadi alkhairi ko kayi shiru,
Na goma : ka yawaita karatun
Alkur’ani mai girma, da zikri da
salatin Annabi saw, da istigfari,
Na sha daya : ka dauki kanka ba kowa
ba, ba komai ba, domin farkon yan
wuta, malamai ne, da attajirai, da
mujahidai, da sukayi aiki, ba don
Allah ba, sai don a fada, kuma an
fada, sunji dadi, don haka suka zama
makamashin Jahannama.
Na sha biyu: kada ka kuskura kabar
duniya da hakkin wani a kanka.
Allah rahmar ka ba dan muba.

Advertisements

5 thoughts on “BABBAN ARZIKI(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa Page)

  1. slm da fatan malam kana lafia ina yimaka fatan alkhairi dan Allah malam nayi bakance idan na aure ta sai nayi azumi amma gashi yarinya ta mutu ba ayi auren ba.sako daga idris shuaibu dake shaka Bus top.

  2. Malam ALLAH yasaka muku da alkhairi akan tunatar damu da kuke akullu yaumin. ALLAH yabaku lada amin summa summa .

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s