DUKKAN ALHERI NA CIKIN KOYI DA ANNABI MUHAMMAD DUKKAN SHARRI NA CIKIN SABA MASA:(Dr.Ibrahim Jalo Jalingo)


Wajibi ne mu san cewa maganar
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah ita ce gaba da maganar kowa a
duniyan nan komin girmansa a idanun
jama’arsa. Babban Malamin Sunnah
Alhafiz Ibnu Rajab wanda ya mutu a
shekarar hijira ta 795 watau yau
shekaru 640 ke nan da suka wuce, ya
yi wa malamai wata maga da ya
kamata a rubuta da ruwan zinari, ya ce
cikin littafinsa mai suna Alhikamul
Jadiratu Bil Iza’ah shafi na 12:-
((ﻓﺎﻟﻮﺍﺟﺐ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺑﻠﻐﻪ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻋﺮﻓﻪ ﺍﻥ ﻳﺒﻴﻨﻪ ﻟﻼﻣﺔ ﻭﻳﻨﺼﺢ ﻟﻬﻢ
ﻭﻳﺄﻣﺮﻫﻢ ﺑﺎﺗﺒﺎﻉ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺍﻥ ﺧﺎﻟﻒ ﺫﻟﻚ ﺭﺃﻱ ﻋﻈﻴﻢ
ﻣﻦ ﺍﻻﻣﺔ؛ ﻓﺎﻥ ﺍﻣﺮ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺣﻖ ﺍﻥ ﻳﻌﻈﻢ ﻭﻳﻘﺘﺪﻯ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺭﺃﻱ ﺍﻱ ﻣﻌﻈﻢ
ﻗﺪ ﺧﺎﻟﻒ ﺃﻣﺮﻩ ﻓﻲ ﺑﻌﺾ ﺍﻻﺷﻴﺎﺀ ﺧﻄﺎ، ﻭﻣﻦ ﻫﻨﺎ
ﺭﺩ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﺨﺎﻟﻒ ﺳﻨﺔ
ﺻﺤﻴﺤﺔ، ﻭﺭﺑﻤﺎ ﺍﻏﻠﻈﻮﺍ ﻓﻲ ﺍﻟﺮﺩ ﻻ ﺑﻐﻀﺎ ﻟﻪ، ﺑﻞ
ﻫﻮ ﻣﺤﺒﻮﺏ ﻋﻨﺪﻫﻢ ﻣﻌﻈﻢ ﻓﻲ ﻧﻔﻮﺳﻬﻢ، ﻭﻟﻜﻦ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﺣﺐ ﺍﻟﻴﻬﻢ ﻭﺃﻣﺮﻩ ﻓﻮﻕ ﺍﻣﺮ ﻛﻞ
ﻣﺨﻠﻮﻕ، ﻓﺈﺫﺍ ﺗﻌﺎﺭﺽ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻭﺃﻣﺮ ﻏﻴﺮﻩ
ﻓﺄﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻭﻟﻰ ﺍﻥ ﻳﻘﺪﻡ ﻭﻳﺘﺒﻊ ﻭﻻ ﻳﻤﻨﻊ ﻣﻦ
ﺫﻟﻚ ﺗﻌﻈﻴﻢ ﻣﻦ ﺧﺎﻟﻒ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺍﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻐﻔﻮﺭﺍ ﻟﻪ،
ﺑﻞ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻤﺨﺎﻟﻒ ﺍﻟﻤﻐﻔﻮﺭ ﻟﻪ ﻻ ﻳﻜﺮﻩ ﺍﻥ ﻳﺨﺎﻟﻒ
ﺃﻣﺮﻩ ﺍﺫﺍ ﻇﻬﺮ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﺑﺨﻼﻓﻪ ( (. ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((wajibi ne a kan dukkan
wanda umurnin Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah ya isa zuwa
gare shi, ya kuma san shi, ya bayyana
shi ga Al’ummah, ya musu nasiha, ya
umurce su da bin umurninsa koda
kuwa hakan ya saba wa ra’ayin wani
babba a cikin Al’ummah, saboda
umurnin Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah shi ya fi cancantar a
girmama shi, kuma a yi koyi da shi a
kan ra’ayin dukkan wani wanda ake
girmamawa amma kuma umurninsa
ya saba wa umurnin shi cikin sashin
lamura cikin kure, wannan shi ya sa
ma Sahabbai da wadanda suka biyo
bayansu suka yi wa dukkan wanda ya
saba wa Sahihiyar Sunnah raddi, wani
lokaci ma raddi mai kaushi, ba wai
kuma saboda suna nuna kiyayya ba ce
gare shi, a’a yana nan abin so a gare su
kuma abin girmamawa a cikin
rayukansu, to amma Manzon Allah
shi ne mafi soyuwa a gare su, sannan
umurninsa shi yake sama da umurnin
ko wace halitta. Saboda haka idan
umurnin Manzon Allah ya yi karo da
umurnin waninsa, to umurnin Manzon
Allah shi ya fi cancantar a gabatar
kuma a bi, wannan kuwa ba zai hana a
girmama mutumin da ya saba wa
umurnin Manzon Allah ba matukar
dai ana gafarta wa kuren cikin
Sahari’ah, kuma shi wannan da ya yi
sabon cikin kure ba zai nuna kyamar a
saba wa umurninsa matukar dai
umurnin Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah ya bayyana a matsayin
mai saba masa)).
******************************
*******
Sannan Sheik Uthmanu Dan Fodiyo
ya yi wata magana mai kyawun gaske
wacce za ta amfanar da masu wa’azi a
cikin littafin Ihya’us Sunnah shafi na
8:-
(( ﻗﺪ ﺍﻧﻌﻘﺪ ﺍﻹﺟﻤﺎﻉ ﻋﻠﻰ ﺍﻥ ﺁﺭﺍﺀ ﺍﻟﻤﺠﺘﻬﺪﻳﻦ ﻛﻠﻬﺎ
ﻣﺴﺎﻟﻚ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﻃﺮﻕ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮﺍﺕ ﻓﻤﻦ ﺳﻠﻚ
ﻣﻨﻬﺎ ﻃﺮﻳﻘﺎ ﻭﺻﻠﻪ ﺍﻟﻰ ﻣﺎ ﻭﺻﻠﻮﺍ ﺍﻟﻴﻪ ﺣﻘﺎ ﻭﻣﻦ
ﻋﺪﻝ ﻋﻨﻪ ﻗﻴﻞ ﻟﻪ ﺳﺤﻘﺎ! ﻭﻳﺠﻮﺯ ﺗﻘﻠﻴﺪﻫﻢ ﻓﻲ ﻛﻞ
ﺭﺃﻱ ﺍﻻ ﻣﺎ ﺧﺎﻟﻒ ﻧﺺ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﺍﻭ ﻧﺺ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻭ
ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ ﺍﻭ ﺍﻟﻘﻴﺎﺱ ﺍﻟﺠﻠﻲ، ﻓﺎﻓﻬﻢ ( (. ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ijma’i ya kullu a kan cewa:
dukkan ra’ayoyin Mujtahidai mashiga
ce ta zuwa Aljanna, kuma hanyoyi ne
na alkhairai, wanda duk ya bi wata
hanya cikinsu tabbas za ta kai shi inda
suka kai, wanda kuma ya baude ga
barin su sai a ce da shi tir. Sannan
yana halatta a yi koyi da su cikin ko
wane ra’ayi, amma banda abin da
ra’ayin da ya saba wa nassin Alkur’ani,
ko nassin Hadithi, ko saba wa
Ka’idodi, da Ijma’i, ko Kiyasi Jaliyyi,
ka fahimta)).
******************************
****
Wannan yana wajabta cewa: Dukkan
abin da Annabi mai tsira da amincin
Allah ya yi umurni da yin sa, to wajibi
ne daliban ilmi su bayyanar da shi ga
Al’ummah, sannan da za a samu wani
mai son zuciya da zai yi kokarin hana
su yin hakan to ba za su saurara masa
ba, wannan shi ne daidai kuma shi ne
hanyar Annabi da sauran Maluman
Sunnah. Sannan haramun ne a kan
kowane Musulmi ya bi ijtihadin wani
malami komin girmansa matukar dai
ijtihadin nasa ya saba wa nassin
Alkur’ani, ko nassin Hadithi, ko nassin
Ijma’i, ko Kiyasi Jaliyyi, kamar dai
yadda Sheik Uthmanu Dan Fodiyo ya
bayyana wa dukkan al’ummar
Musulmi.
Muna rokon Allah da Ya tabbatar da
dugaduganmu a kan bin sunnar
Annabi mai tsira da amincin Allah.
Ameen.

Advertisements

One thought on “DUKKAN ALHERI NA CIKIN KOYI DA ANNABI MUHAMMAD DUKKAN SHARRI NA CIKIN SABA MASA:(Dr.Ibrahim Jalo Jalingo)

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s