KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 003 WAJIBCIN TSAYUWA A KAN LITTAFIN ALLAH DA SUNNAR ANNABI (S.A.W.)(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


Har illa yau, Allah (S.W.A) Ya ambaci falalar da ya yi wa wannan al’umma da ya aiko mata da Annabi (S.A.W.) don Ya bayyana mata saqon Alkur’ani da SunnarSa. Kamar yadda yake fada cewa: “Lallai ne Allah Ya Yi babbar falala a kan muminai, da Ya aika a cikinsu Manzo daga garesu, yana karantar musu ayoyinSa kuma yana tsarkake su kuma yana karantar da su littafi da hikima, alhali sun kasance a gabannin haka lallai suna cikin bata bayyananne.” Wannan aya ta tabbatar da aiko Manzon tsira (S.A.W.) da Allah ya yi, zuwa ga mutane don ya karanta littafin Allah ya tsarkake muminai da imani ya kuma koyar da su littafi da kuma hikima, (wato qarin bayani daga bakin Manzon Allah (S.A.W.) don ya kubutar da bayinSa daga bata zuwa ga shiriya.
Imam Shafii ya yi bayani game da Littafi da hikima da Allah Ya ambata a wannan aya, a inda yake cewa, Maanar littafi shi ne Alqurani, hikima kuma ita ce Sunnar Manzon Allah (S.A.W.). Domin shi Alqurani cike yake da hikima, don haka ambaton hikima a wannan aya a bayan an ambaci littafin Allah, nuni ne da cewa ba Alqurani ake nufi da hikima ba a nan. Kasancewar Annabi ne aka saukar masa da Alqurani, sai Allah Ya wajabta mana bin ManzonSa da karbar umarninSa. Ya kuma tsare shi da tsarkake shi, ba ya hukunci face da wahayi daga Allah. To ashe babu abin da ya fi dacewa da hikimar da Allah ya ambata a nan sai Sunnar Manzon (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi).

A wata ayar kuma Allah (S.W.T.) Ya wajabta mana biyayya gare shi da ManzonSa da kuma majibinta alamarinmu, sannan Ya umarce mu da komawa zuwa gare shi da ManzonSa idan mun sami sabani don ya nuna mana shiriya tana tare da riqo ga Allah da ManzonSa. To yaya za mu yi riqo da Manzon Allah idan ba mu riqe Sunnarsa ba, don yin hujja da ita a cikin alamuran rayuwarmu? Allah (S.W.T.) Yana cewa: “Kuma abin da Manzo ya zo muku da shi, to ku riqe shi, abin da kuma ya hana ku, to ku hanu daga shi….” (Hashr:7).
Akwai wata ayar kuma wadda take gargadin mutane kamar haka: “….Wadannan da suke saba wa umarninSa su ji tsoron kada wata fitina ta same su, ko wata azaba mai radadi ta riske su.” (Nur:63).
Ibn Kathir ya ce, “Umarnin da ake nufi a nan shi ne na Manzon Allah (SAW.), watau bin hanyarsa da tsarin rayuwarsa da Sunnarsa da Shariarsa. Sannan da auna maganganu da ayyukanmu da maganganu da ayyukan Manzon Allah (S.A.W.), idan sun dace to shi ke nan, idan kuma sun saba ba za a karbi wadannan ayyuka ba kamar yadda ya tabbata daga manzon Allah (S.A.W.) cikin maganarsa mai inganci cewa, Wanda ya aikata wani aiki wanda ba ya cikin umarninmu to an mayar masa aikinsa.

Haka nan cikin Alqurani, Allah (S.W.T.) Ya jaddada umarni da riqo da tafarkin Manzon Allah (S.A.W.) don amfanin kanmu, ba don amfanin shi Manzon tsiran ba: “Ka ce ku yi da’a ga Allah da ManzonSa, idan kuka juya baya, to abin da aka aza masa kawai ke kansa, ku kuma a kanku akwai abin da aka aza muku. Kuma idan kun yi masa da’a za ku shiryu. Kuma babu abin da yake a kan Manzo face isarwa bayyananniya.” (Nur:54).

Wadannan ayoyi da ke wajabta mana bin Allah tare da ManzonSa suna nuni ne ga riqo da littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (S.A.W.). Sannan kuma wadannan abubuwa guda biyu duk asalinsu guda ne, don haka ba ya halatta a yarda da tafarki daya amma a yi watsi da daya tafarkin. Wanda ya yi haka to ya juya baya ke nan ga wadannan tafarkai baki daya.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s