KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 005 WAJIBCIN TSAYUWA A KAN LITTAFIN ALLAH DA SUNNAR ANNABI (S.A.W.).(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


Bayan kammalar sakon Musulunci a zamanin Annabi (S.A.W.), shi Manzon tsiran ya isar da saqon Musulunci kamar yadda aka umarce shi. Ummul-muminina Aishatu (R.A.) ta ruwaito cewa wanda duk ya yi da’awar Annabi Muhammad (S.A.W.) ya boye wani abu cikin abin da aka saukar masa, haqiqa ya yi qarya. Sai ta kafa hujja da wata aya cikin Suratul Ma’idah: “Ya kai manzo, ka isar da abin da aka saukar maka daga Ubangijinka, kuma idan ba ka isar ba, to tamkar ba ka isar da manzanci ba ke nan. Kuma Allah yana tsaron ka daga mutane. Lallai ne Allah ba ya shiryar da mutane kafirai.” (Ma’ida:67).
Fadar Ubangiji cewa, idan ba ka isar (da saqon Allah ba) to tamkar ba ka isar da manzanci ba ke nan (baki daya) yana nuni ne da cewa manzon Allah (S.A.W.) bai rage ko da aya guda ba cikin abin da aka yi masa wahayi. Domin kuwa kowane Musulmi ya yarda da cewa manzon tsira ya isar da saqon Allah ga mutanen duniya, shi kansa Annabi (S.A.W.) a cikin wani Hadisi mai inganci na Imamu Muslim, a jawabin da ya gabatar lokacin Hajjin ban kwana ya ambaci cewa: “Ya Ubangiji shin na isar da saqo? Ya Ubangiji ka yi mini shaida (a kan haka).”

Kasancewar saqon Musulunci ya kammala kuma Manzon Allah (S.A.W.) ya isar da dukkan abin da aka umarce shi da isawar, kamar yadda ya ke tattare cikin littafin Allah da Sunnar ManzonSa, to babu wani zabi da Musulmi ke da shi illa ya bi wannan tafarki bayyananne. Allah (S.W.T.) Yana cewa: “Kuma ba ya halatta ga mumini da kuma mumina a lokacin da Allah da ManzonSa suka hukunta wani umarni, su kasance suna da wani zabi daga almarinsa wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, to ya bace bacewa bayyananniya.”

Kamar yadda ba a neman zabi wajen bin umarnin Allah da ManzonSa, haka ma ba a bambantawa tsakanin bin littafin Allah da kuma bin Sunnar Manzon Rahama (S.A.W.) Domin duk hanyoyin biyu tafarki guda ne, ba a cewa wannan bai zo cikin Alqurani ba sai dai an ambace shi a cikin Hadisi, don haka bai zama umarni ne daga Allah ba. Abin da duk ya tabbata daga Hadisi, to ya zamo hukunci ne daga Allah ko da kuwa Alqurani bai zo da shi ba. Haka Imam Shafi’i ya ambata a cikin littafinsa mai suna AL-RISALA a inda yake cewa, Abin da Annabi ya sunnanta wanda babu hukuncin Allah a cikinsa (daga Alqurani), to Sunnar a nan ita ce hukuncin Allah, kamar yadda Ubangiji ya bayyana mana cikin littafinsa mai girma cewa: “Kuma lallai kai kana shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya, hanyar Allah.” (Shura: 52-53).

Wannan hanya ita ce tafarkin kasancewa tare da Annabi da Salihan bayi. Allah (S.W.T.) Yana cewa: “Kuma wadannan da suka yi da’a ga Allah da ManzonSa, to suna tare da wadanda Allah Ya yi ni’ima a kansu, daga Annabawa da masu yawan gaskatawa, da masu Shahada da Salihai. Wadannan sun kyautatu ga zaben abokan tafiya.” (Nisa’i: 69).

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s