KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 008 SU WANE NE MAGABATA NA QWARAI?(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


Wadannan mutane da aka ambata a nan su ne sahabban Manzon Allah (S.A.W.) ma su martaba da daukaka kuma su abin girmamawa ne ga dukkanin Musulmi. Su ne kuma rukuni na farko na magabatan qwarai. Mafifita daga cikinsu su ne Khulafaur-Rashidun, watau Abubakar da Umar da Usman da Aliyu (R.A.) Wadannan su ne suka karbi jagorancin daular musulunci daga wurin Annabi (S.A.W.) bayan rayuwarsa, kuma suka shimfida adalci, da kare mutuncin dokokin Allah, sannan suka yada saqon musulunci har ya mamaye qasar Larabawa ya kuma fantsama duniya. Wadannan su ne wadanda manzon Allah (S.A.W.) ya umarce mu da riqo da igiyarsu har ma ya qara da cewa mu cije ta da turamen haqoranmu.

Bayan wadannan Halifofi hudu, akwai sahabbai guda goma wadanda annabi ya yi musu albishir da Aljanna, cikinsu akwai Dalhat bin Ubaidillahi, da Zabairu bin Auwam da Saad bin Abi Waqqas, da Said bin Zaid da Abu Ubayda Amir bin Jarrah da kuma Abdurrahman bin Auf. Sannan bayan wadannan akwai ma’abota Badar (wato wadanda suka halarci yaqin Badar), (Sahabbai ne sama da dari uku). Bayan su da akwai wadannan da aka yi wa bushara da Aljannan bayan guda goma na farko ga irin su Fadima yar manzon Allah (S.A.W.) da ‘ya ‘yanta Hassan da Husaini da Thabit bin Qaisu da Bilal bin Rabaha da dai sauransu.

Manzon Allah (S.A.W.) ya yi ambato na alheri zuwa ga wadannan Sahabbai don ya kasance abin wa’azi garemu.

Irin wannan shaida da Manzon Allah (S.A.W.) ya yi wa sahabbansa ya isa darasi a gare mu a kan tabbatar amincinsu, da sahibancinsu, da kasancewar su a kan hanya ta qwarai, kamar yadda ya zo cikin littafin Bukhari. Manzon Allah (S.A.W.) ya ambaci wasu Sahabbansa da ambato na alheri kamar haka: ya ce game da Abdullahi bin Umar, Abdullahi mutum ne salihi. Bilal bin Rabahu Na ji qarar takun takalminka kusa da ni a cikin Aljanna. Ita kuma Fadimatu yar manzon Allah (S.A.W.) ya ce, Fadimatu ita ce shugabar matan Aljanna. Game da Jaafar bin Abi Talib kuma ya ce, Ka yi kama da ni a halitta da halaye.

Wadannan kadan ne daga cikin ambato na alheri da manzon Allah (S.A.W.) ya yi wa sahabbansa don tabbatar da darajarsu. Kuma wannan bayani ba ya nufin sauran sahabban manzon Allah da ba a ambata a nan ba, ba su da wata daukaka ke nan, a’a dukkan sahabban manzon Allah (S.A.W.) suna da daraja da fifiko a kan wasunsu. Annabi (S.A.W.) ya ce cikin Hadisi da aka karbo daga Abu Said Alkudri ya ce, Kada ku tozarta sahabaina, domin na rantse da wanda nunfashina yake hannunsa, da wanin ku zai yi sadaka da abin da ya kai girman dutsen Uhud na zinare, ba zai sami (darajar) wanda ya yi sadaka da cikin tafin hannu, ko ma rabin hakan ba daga cikin sahabbai. (Bukhari ne ya ruwaito Hadisin).

An ruwaito cewa Annabi (S.A.W.) ya yi wannan bayani ne a lokacin da Khalid bin Walid wanda ya karbi musulunci bayan bude Makka ya yi yar jayayya da Abdurrahman bin Auf. Don haka idan har za a samu bambancin daraja a cikin sahabbai saboda fifikon dadewarsu a musulunci da aikin da suka yi wa addini, to ashe wadannan magabata na farko sun tsere wa wadanda suka biyo bayansu daga cikin muminai.

Bayan sahaban manzo Allah (S.A.W.) kuma sai wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa daga tabiai da tabiut tabiun. Wadannan su ne bayin Allah da suka rayu cikin shekaru dari ukun farko na Musulunci. Rukunan nan guda uku, Manzon Allah (S.A.W.) ya ambace su daya bayan daya wajen daraja cikin Hadisi da yake cewa: “Mafi alherin mutane su ne wadanda suka zo a qarnina, sannan kuma sai wadanda suka biyo bayansu, sannan kuma sai wadanda suka biyo bayansu.” (Bukhari ne da Muslim suka ruwaito shi).

Magabata na qwarai da suka rayu cikin wadannan zamuna, haqiqa su ne gaba wajen ilimi da taqawa, gudun duniya, yawan ibada da halaye na qwarai da fahimtar saqon da musulunci ya zo da shi.

Akwai wadansu magabata wadanda suka yi fice wajen qoqarin fahimtar hukunce-hukuncen musulunci, kuma wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen wannan hidima. Daga cikinsu akwai manyan malamai guda hudu da suka hada da Imam Malik Ibn Anas, da Imam Shafii, da Imam Abu Hanifa, da kuma Imam Ahmad Ibn Hambal.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s