KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 010 AQIDOJIN MASU KOYI DA MAGABATA NA QWARAI(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


Wadannan magabata na qwarai suna da wasu aqidoji da qaidoji da suka shimfida rayuwarsu a kai. Muhimmai daga cikin wadannan aqidoji wadanda suka bambanta tafarkin managartan bayi daga wasun su su ne:

1. Gamsuwa da Alqurani da sunnah wajen alamarin adddininsu wadanda suka hada da aqida, ayyukan ibada, muamala, dabi’o’i, da halayensu. Dukkan abin da ya tabbata cikin Alqurani da sunnah suna karbar sa su yi aiki da shi, abubuwan da kuma suka saba musu, suna watsi da su.

2. Miqa wuya ga abubuwan da Sharia ta tabbatar cikin NASSI (Alqurani da Sunnah) a kan fahimtar magabatan farko. Ba su kasance masu bijirar da hankulansu a kan abin da ya zo cikin NASSI ba, sai dai su bijirar da NASSI a kan hankulansu. Ba sa riqo da wani abu su bar Alqurani da Sunnah.

3. Bin abin da manzon Allah (S.A.W.) ya zo da shi da barin qirqirar abubuwa. Ba sa daga muryarsu sama da sautin manzon Allah (S.A.W.), suna riqo ne da abin da Allah da manzonSa suka yi umarni da shi.

4. Dagewa wajen rungumar Alqurani da sunnah, wato suna mayar da hankulansu ta wajen yi wa Alqurani hidima ta hanyar kiyaye shi, tilawar sa da sanin haqiqanin ma’anarsa. Haka ma ga hadisan Manzon Allah (S.A.W.) wajen sanin ma’anarsu da matsayinsu (wato tantace ingantattun hadisai da raunannu ko marasa asali). Dagewa wajen neman ilimi ta wajen fahimtar addini bisa koyarwar annabi (S.A.W.).

5. Suna matuqar yin riqo da sahihin tafarkin manzon Allah (S.A.W.) ta hanyar amfani da dukkan abin da ya inganta daga Sunnar manzon Allah (S.A.W.), ba tare da bambanta tsakanin hukunci da hadisi guda daya kawai ba, ko makamancin haka.

6. Ba su da wani jagora wanda ake karbar dukkan abin da ya zo da shi, da kuma barin abin da ya saba in banda manzon Allah (S.A.W.). Bayan manzon Allah (S.A.W.) duk wanda ya zo da magana suna auna ta ne, abin da ya dace da sunnah su karba, abin da kuwa ya saba sai su yi watsi da shi.

7. Sun fi kowa neman sanin hadisin manzon Allah (S.A.W.), suna masu himmatuwa wajen neman ilimin tafarkinsa, ayyukansa da maganganunsa da abubuwan da ya tabbatar da su.
Saboda fahimtarsu ga Manzon Allah (S.A.W.) sai suka fi kowa son sa da bin tafarkinsa.

8. Suna miqa wuyansu ga alamarin addini baki daya a kan jagorancin koyarwar manzon Allah (S.A.W.). Suna riqo da igiyar Allah baki daya a kan koyarwar manzon Allah (S.A.W.), ba sa rarraba kawunansu, kuma ba su kasance qungiya-qungiya ba. Sannan kuma ba sa yin tawili ko juya baya ga wani hukunci. Ma’ana, ba sa qyamar juna don son zuciya, rayuwarsu duk tana ratayuwa ga koyarwar manzon Allah (S.A.W.).

9. Ba a samun sabani a tsakaninsu wajen sanin asalin addini da kuma qaidojin da aka gina aqidar musulunci a kansu. Fahimtarsu a kan abin da ya shafi Sunayen Allah da Siffofinsa da ayyukansa duk daya ne. Haka wajen Imani da sanin abin da ya qunsa da abubuwan da ke warware shi da maganganu a kan qaddara da dai sauransu.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s