KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 011 AQIDOJIN MASU KOYI DA MAGABATA NA QWARAI(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


10. Barin musayya cikin alamarin addinin da kusantar ma’abota husumar, saboda kasancewar husuma mafarar rarrabuwa ce da fitina wanda kuma tushensu shi ne bibiko (Ta’assubanci) da bin son rai. Khalifa Umar Ibn Abdull-Aziz yana cewa: “Dukkan wanda ya mayar da addininsa abin musayya to zai kasance cikin rudani (ya tashi daga wannan raayi yau ya koma wani gobe).” Haka kuma Jaafar Ibn Muhammad na fadar cewa: “Ina horon ku da barin yawan husuma cikin addini domin (yin haka) yana shagaltar da zuciya ya kuma gadar da munafinci.”

11. Qoqarin hada muryar musulmi a kan gaskiya da neman gusar da duk abin da ake jayayya da rarrabuwa a tsakaninsu. Suna yin haka ne domin sanin cewa haduwar kan musulmi alheri ne, rarrabuwa kuma fitina ce.

12. Sun kasance ma’abota kira zuwa ga addinin Allah cikin hikima da wa’azi mai kyau, idan kuwa za su yi jayayya ne a kan fahimtar addini, to suna jayayya ne da abin da ya fi kyau na neman maslaha da isar da sahihin saqon Musulunci.

13. Suna masu gyara a cikin alumma, suna gyara abin da mutane suka barnata, su kuma kawo maslaha a tsakanin mutane su kuma toshe hanyar barna.

Zukatansu da maganganunsu sun karkata wajen girmama sahabban Manzon Allah (S.A.W.) wajen nuna so da yabo zuwa garesu, tare kuma da bin tafarkinsu. Sun qudurce cewa sahabban Manzon Allah (S.A.W.) su ne mafifita a cikin wannan alumma wadda Allah da manzonSa suka yaba wa, kuma ya wajaba ga kowane musulmi ya yi koyi da su cikin addini.

14. Ba sa nuna soyayyarsu ko adawarsu ga kowa sai a kan asasin addini. Ba sa rinjayar da komai don kawunansu, ko yin fushi da wani ko jibintar wani, irin na Jahiliyya, ko don bibikon mazhaba ko qungiyanci. Sun kasance dukkan wilayarsu ga addini ne, suna jibintar mutum don Allah, sannan su bijire don Allah. Wanda ya dauka cewa yarda da wane ko bin tafarkin wani malami shi ne kawai Musulunci, to ya tabe. Babu wanda saba wa umarninsa ke iya kaiwa ga kafirci ko halaka sai annabi (S.A.W.), domin kowa na iya kuskure banda annabi (S.A.W.). Don haka babu wani Shehin Malami, ko shugaban wata qungiya da bin sa shi ne Musulunci, bijire masa kuma shi ne kafirci. Dukkan biyayya zuwa ga Allah da nnabi (S.A.W.) ta ke. Addini kuma ana yin sa ne bisa yadda Allah (S.W.T.) Ya ke so kuma annabi (S.A.W.) ya sunnatar mana a kan fahimta da koyarwar magabata na qwarai.

A darasi na gaba za mu shiga MANUFA DA FAIDAR KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s