KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 013 FA’IDAR KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI.(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


Idan har a ka yi riqo da wannan hanya ta magabata za a sami faidoji masu yawa wadda suka hada da:

(i) TASFIYYA (Tsarkakakke addini): Komawa ga asali zai sa Musulmi su tsarkake addininsu daga dukkan gurbata na daga bidi’o’i da kuma wasu ra’ayoyi da ba su tabbata daga magabata ba.
A cikin wani Hadisi na manzon Allah (S.A.W.) yana cewa: “ Wannan ilimi wanda za su yada shi su ne amintattu daga kowanne qarni. Za su kawar da duk wata karkata da masu shisshigi za su kawo, da qaryatarwar masu qaryatawa da kuma bayanan qarya da jahilai za su bijiro da shi.”
A cikin sharhin Sahih Muslim, Muhammad bin Sirin yana cewa: “Abin da ake nufi da ilmi a nan shi ne addini, don haka sai mutum ya yi hankali da wurin da zai karbi (fatawowinsa) na addini. A kan wannan Hadisi za mu fahimci cewa komawa ga da’awar magabata da wasu bayin Allah ke kira a kansa wani alqawari ne na Allah don tsarkake addini daga bata da son ran wasu mutane.

(ii) TAJDEED (Jaddada addini): Saboda daukakar da Allah ya yi wa addininSa, Ya tanadi hanyoyin farfado da shi bayan wani zamani da aka sami tabewa da kuma qasqanci. Saboda haka komawa ga hanyar magabata shi ne zai ba da damar farfado da asalin musulunci da haqiqanin koyarwarsa da dawo da qarfinsa da kuma martabarsa. Daman Allah ya yi alqawarin tayar da wasu daga cikin bayinSa don jaddada addininSa bayan qarshen kowane qarni kamar yadda wani hadisin manzon Allah (S.A.W.) ya yi bayani, wanda kuma ya zo cikin sunan na Abu Dawud.

(iii) Tarbiyya: Koyar da alumma tsantsar addini ba zai samu ba sai an koma ga hanyar magabata domin su ne malaman addini na asali. Saboda haka komawa ga magabata shi ne zai ba alummar musulmi tarbiya ta fahimtar tsantsar addini.
Sahabban Manzon Allah (S.A.W.) su suka fi dacewa da sunan Al-Rabbaniyya da Allah ya ambata a cikin Suratul Ali Imrana abin da suka sani su koyar da tarbiya ga na bayansu a kai.

(iv) ISLAHUL UMMA (Gyaran alumma): Dukkkan Annabawa sun zo don gyaran alummarsu ne, bayan an dauki lokaci cikin bata da tabewa, kamar yadda Allah (S.W.T.) ya ba mu labari a cikin irin bayanin da annabi Shuaibu ya yi wa jama’arsa: “Ba na nufin komai face gyara gwargwadon yadda na samu dama. Kuma dacewar ta na ga Allah (shi kadai). A gare Shi na dogara kuma zuwa gare shi nake mayar da alamurana. (Hud:88).

Ko da yake babu sauran Annabi ko kuma manzanci bayan Annabi Muhammad (S.A.W.), amma gyaran alumma zai ci gaba don cika hasken addinin Allah. Wannan gyara ba zai inganta ba sai an yi riqo da sahihiyar turba kan jagorancin magabata na qwarai. Wadannan su ne wadanda suka riqi sahihin tafarkin da Manzon Allah (S.A.W.) da Sahabbansa suka rayu a kai. Ba sa nuna qyama ko watsi da ingantacciyar maganar annabi (S.A.W.) ba don ya saba da fahimtar malaminka, shehunansu, ko jagoransu, ko qungiyarsu ba.

A darasi na gaba in shaa Allah za mu ji MATSAYIN WANDA YA SABA WA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s