KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih). *** 016 AQIDAR AHLUS SUNNAH (Daga Sheikh Muhammad Salih al-Uthaimin).(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


Aqidarmu ita ce: Ba da gaskiya ga Allah, da MalaikunSa da littattafanSa da ManzanninSa, da ranar lahira da kuma imani da qaddara alherinta ko rashinta.
Ga bayanin yadda aqidarmu ta ke bi da bi kamar haka:

1. Muna ba da gaskiya cewa shi Allah shi ne mahalicci, mai tsara dukkan abin alamuran mu, kuma duk wani abin bauta banda Allah qarya ne.

2. Muna kuma ba da gaskiya da sunayenSa da siffofinSa. Wato abin nufi shi ne, muna tabbatar da cewa Allah ta’ala yana da wasu sunaye da wasu siffofi kyawawa, cikakku kuma maxaukaka.

3. Muna kuma ba da gaskiya da kadaituwar Allah cikin duk abin da aka ambata can da farko, cewa shi ne Allah da ba shi da abokin tarayya cikin abin bauta da gaskiya, kuma ba shi da abokin tarayya a cikin sunayenSa, da kuma cikin siffofinSa.
Allah Taala ya ce: “Ubangijin sammai da qassai da abin da ke tsakaninsu. Ka bauta maSa kuma ka daure a kan bauta maSa, ko ka san wani takwara gare Shi?” (Maryam :65).
Mun ba da gaskiya cewa shi ne:
“Allah babu wani abin bauta sai Shi, Shi ne rayayye (da ba ya mutuwa) mai daidaita lamari. Gyangyadi ba ya kama shi, ballantana barci. Shi ke da duk abin da ke cikin sammai da qassai (halittarsa ne, mallakarsa ne kuma bayinsa ne ) wane ne yake da ikon ceton (wani) a gunSa ba da izininSa ba, yana sane da abin da ke gabansu da wanda ke bayansu, kuma babu abin da suka sani game da ilminSa sai wanda Ya so (ya nuna musu). Kujerar sarautarSa ta yawalci sammai da qasa: (wato ta fi su girma) kuma kiyaye su bai gagare Shi ba (kiyaye sama da qasa) Shi ne madaukaki kuma mai girma.(Baqara:255).
Muna kuma ba da gaskiya cewa:
“ Haqiqa Allah Shi ke da ranar Alqiyama, Shi kuma ke saukar da ruwa, kuma Yana sane da abin da ke cikin mahaifa. Kuma babu wata rai da ta san abin da za ta aikata gobe, kuma babu wata rai da ta san qasar da za ta mutu, lallai Allah Masani ne kuma Mai labarin komai.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s