KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih). *** 019 AQIDAR AHLUS SUNNAH (Daga Sheikh Muhammad Salih al-Uthaimin).(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


12. Muna kuma ba da gaskiya cewa: Lallai su wadannan dangogi biyu na Iradar Allah, duk sun rataya ne da hikimar Allah. Duk abin da Allah Ya hukunta a kan bayinSa tun farkon halitta ko kuma Ya qallafa wa bayinSa na ibada duk tare da hikima ce, ko mun gano hikimar ko ba mu gano ba, saboda qarancin ilimi da yake tare da mu, ko kuma ya zamana hankalinmu ne bai kai ga fahimtar haka ba. Allah Ta’ala Ya ce:
“Ashe kuwa Allah ba Shi ne Fiyeyyen Masu hikima ba?” (Tin:8).
Ya kuma ce:
“Wane ne ya fi Allah iya hukunci a wurin mutane da suka sakankance (da Allah)?” (Ma’ida 50).

13. Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai Allah (Ta’ala) Yana son waliyyanSa, su kuma suna son Shi. Allah (S.W.T.) Ya ce:
“Ka ce in dai kun kasance kuna son Allah, to ku bi Ni, Allah zai so ku.”. (Ali Imraan:31)
Ya kuma ce:
“Da sannu Allah Zai zo da wasu mutane Yana son su suna son Shi.” (Ma’ida:54).
Ya kuma ce:
“Allah Yana son masu haquri.” Ali Imraan:146).
Ya kuma ce:
“Ku yi adalci, lallai Allah Na son ma su adalci.” (Hujuraat:9).
Ya kuma ce:
“Ku kyautata, lallai Allah Na son masu kyautatawa.” (Baqara:195).
Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai Allah Yana kyautatawa.

14. Manzon Allah (S.A.W.) ya yarda da duk ayyuka da zantuka na ibada da Shi Allah Ya shar’anta Yana kuma qin duk abubuwa da ya yi hani ga barin su. Ya ce:
“In kun kafirta, to lallai Allah Ya wadatu ga barin ku (Shi Allah) bai yardar wa bayinSa da kafirci ba. Kuma lallai in kun gode zai yardar muku da shi.” (Ma’ana zai yarda da bautar) (Zumar:7)
Ya kuma ce:
“Amma sai Allah Ya qi fitarsu (zuwa yaqi), sai Ya zaunar da su, aka ce musu ku zauna tare da masu zama.” (Tauba:46).

15. Muna kuma ba da gaskiya cewa: Lallai ne Allah Ta’ala Yana tabbatar da yardarSa a kan wadanda suka yi ban gaskiya da Allah suka kuma yi aiki na gari.
Ya ce:
“Allah Ya yarda da su kuma su ma sun yarda da abin da Allah ya ba su. Samun haka sai wanda ya ji tsoron Allah.” (Bayyinah:8).

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s