KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih). *** 021 AQIDAR AHLUS SUNNAH (Daga Sheikh Muhammad Salih al-Uthaimin).(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


20. Kuma AhlusSunnah sun yi ijmai a kan cewa: Idanun Allah biyu ne. Kuma zancen nan na Maaikin Allah (S.A.W.) ya qarfafa wannan maganar. Ita ce fadarsa da ya yi game da Dujal. Sai ya ce: (Lalle mai ido daya ne, kuma lallai shi Ubangijin naku Allah ba mai ido daya ba ne).
Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai Allah Ta’ala.
“Idanu ba sa riske Shi, Shi ne yake riske idanu, Shi ne (Sarki) Masanin lamari (kuma) Masanin komai.” (An’am:103).

21. Muna kuma ba da gaskiya lallai mumunai za su ga Ubangijinsu ranar Qiyama.
“Wasu fuskoki a wannan rana za su yi kyau, suna masu dubi zuwa ga UbangijiSu.” (Alqiyama:22-23).

22. Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai Allah Ta’ala ba Shi da abin kamantawa, saboda cikkakun SiffofinSa.
“Babu wani abu da ya yi kama da Allah, Shi ne Mai ji kuma Mai gani.” (Shura:11).

23. Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai:
“Gyangyadi ba ya kama shi, ko kuma barci.” (Baqara:255).

24. Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai Allah ba ya zaluntar kowa saboda cikakken adalcinSa. Mun kuma yarda cewa lallai ba Ya rafkana da abin da bayinSa ke aikatawa, saboda cikakkiyar kulawarSa da kuma cewa IliminSa na kewaye da komai.

25. Muna kuma ba da gaskiya cewa: Lallai babu wani abu da yake gagarar Sa, cikin sama ne ko a qasa, saboda cikakken Iliminsa da ikonSa.
“Lallai yadda lamarinSa ya ke, in Ya so aikata wani abu sai Ya ce kasance sai ko ya kasance.” (Yasin:82).

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s