KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih). *** 022 AQIDAR AHLUS SUNNAH (Daga Sheikh Muhammad Salih al-Uthaimin).(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


26. Muna kuma ba da gaskiya cewa lallai gajiya ba ta samun Sa, haka kuma wahala saboda cikar qarfinSa. Yana cewa:
“Haqiqa Mun halicci sammai da qassai da abubuwan da ke tsakaninsu, cikin kwana shida. Kuma wata gajiya ba ta shafe Mu ba.” (Qaf:38)

27. Muna kuma ba da gaskiya da duk wasu sunaye ko kuma siffofi da Ubangiji Ya tabbatar wa kanSa, ko kuma ManzonSa (S.A.W.) ya tabbatar maSa sai dai kuma muna matuqar kubuta ga barin abubuwan nan masu girma biyu da aka yi mana kashedi da barin su. Su ne na farko, wato kamantawa da fadin harshe, cewa ita siffar Allah ta yi kama da siffar halitta. Na biyu wato shi ne mutum ya tabbatar a cikin zuciyarsa ko kuma ya fada da harshensa cewa: haqiqanin siffar Allah ga yadda ta ke. Na’uzu billah.

28. Muna kuma ba da gaskiya, kuma mun yarda da kore duk siffa da Allah Taala Ya kore ta daga barin zatinSa, ko kuma wannan Manzo (S.A.W.) ya kore ta ga barin Allah. Mun yi imani cewa, korewar wadannan siffofi (da Allah Ya kore), zai tabbatar da siffa cikakkiya ga Allah. Kuma duk wani abu da Allah da ManzonSa suka qyale ba su yi wani bayani a kansu ba. Mu ma ba za mu ce komai game da su ba.
Muna kuma ganin cewa wajibi ne mu bi wannan tafarki don kuwa Allah Taala dai Ya fi mu sanin kansa, saboda haka duk abin da ya tabbatar na siffofi da kanSa, ko kuma Ya kore shi, to wannan abu tabbatacce ne. Kuma Manzo (S.A.W.) shi ne ya fi kowa sanin Ubangiji don kuwa shi ya fi kowa gaskiya, shi ya fi kowa fasaha.
Duk abin da muke buqata na cikakken ilimi da gaskiya, za mu same su cikin Littafin nan na Allah da kuma Hadisan Annabin (S.A.W.).
Duk wani abu da muka ambata, na game da siffofi na Ubangiji Mai Girma da Daukaka, ko a dunqule, ko kuma dalla-dalla mun tabbatar da shi ne ko kuma mun kore shi ne, duk wani bayani da muka yi mun dogara ne da Alqurani da Hadisin Manzon Allah (S.A.W.) muna bin tafarkin shiryayyun magabatanmu ne.
Kuma muna ganin cewa, wajibi ne mu fassara nassin Alqurani da Hadisan Manzon Allah (S.A.W.) a kan zahirinsu. Muna fassara shi nassin ne a kan haqiqanin maanarsa yadda ya dace da Ubangiji Mai Girma da Daukaka.
Kuma ba mu yarda da fassarar nan ta mavarnata ba, wadanda ke fassara Alqurani da Hadisai ba ta yadda Maaikin Allah (S.A.W.) ya fassara su ba, ba mu kuma yarda da hanyar nan, ta masu tozartar da siffofin Allah ba wadanda ke tozartar da ma’anonin Alqurani ba ta yadda Allah da ManzonSa suka nuna ba. Muna kuma nuna kubutarmu daga tafarkin fassarar nan ta masu qetare iyaka, su ne wadanda ke kamanta Ubangiji da bayinSa, da masu kamanta yadda ya ke.

29. Mun kuma sakankance cewa lallai abin nan da ya zo a cikin Alqurani ko Hadisin Manzon Allah (S.A.W.) shi ne gaskiya. Kuma ba a samun wani sabani tsakaninsu a fuskar fasaha. Allah Mai Girma da Daukaka Ya ce:
“Shin ba za su yi la’akari da Alqur’ani ba, da ya fito daga gun wanin Allah ne, da an sami sabani da yawa a cikinsa.” (Nisa’i: 82).

Lallai samun tangarda a cikin zancen mutum, babu shakka yana tabbatar da qaryar wannan zance, kuma wannan sam ba mai yiwuwa ba ne a same shi a cikin littafin Allah, ko kuma a cikin zancen MaaikinSa (S.A.W.).
Duk wanda ya yi daawar cewa za a iya samun tangarda tsakanin ayoyin Alqurani ko kuma cikin Hadisan Manzon Allah (S.A.W.) to, ko shakka babu cewa zuciyarsa ta ratse, sai ya hanzarta tuba zuwa ga Allah, maza ya dawo daga wannan bata nasa.
Kuma babu wanda zai zaci cewa da akwai sassabawa cikin ayoyin Alqurani ko kuma cikin Hadisan Manzon Allah (S.A.W.) sai mai qarancin ilimi ko kuma raunin fahimta ko kuma shi ne ya kasa mayar da hankali sosai cikin zurfin tunani cikin Littafin Allah. Babu abin da ya kamace shi sai kawai ya zage damtse ya nemi ilimi don ya fihimci gaskiya. Idan kuwa bai sami fahimta ba, to sai ya koma ga masaninsa ya fawwala masa lamarin don ya yi masa bayani, don ya daina wanan mummunan zato, sai ya fadi irin kalmar nan da masu zurfin hankali suke fada. Sai Ya ce:
“Mun ba da gaskiya da shi, duka daga Ubangijinmu ne ya ke!” (Ali Imraan:07).
Ya iya ganewa cewa lallai littafin nan na Allah da Hadisan nan na Manzon Allah (S.A.W.) babu sabani a cikinsu.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s