KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) WAJIBCIN TSAYUWA A KAN LITTAFIN ALLAH DA SUNNAR ANNABI (S.A.W.) *** 002(Sheikh Aliyu Said Gamawa)


Horon da Allah Ya Yi na bin dokokinSa da ke cikin Alqurani bai tsaya kawai ga ManzonSa ba, don kuwa ya hada da dukkan talikai. Allah (S.W.A.) ya ce: “Ku bi abin da aka saukar a gareku daga UbangijinKu, kuma kada ku bi wasu majibinta koma bayanSa. Kadan ne suke wa’azantuwa.” (A’raf:3). “Kuma wannan wani littafi ne wanda muka saukar da Shi mai cike da albarka, don haka ku bi Shi kuma ku ji tsoron (Allah) ko a yi muku rahama.” (An’am:155).

A cikin Alqurani mai girma Allah (S.W.T.) Ya Yi mana umarni da bin littafinsa tare da albishir ga wadanda suka amsa wannan kira: “Haske ya zo muku daga Allah, haka kuma littafi mabayyani (wanda) da shi Allah Yake shiryar da wanda Ya so ta hanyar yardarSa zuwa ga hanyoyin aminci, kuma yana fitar da su daga duhu zuwa ga haske da izininSa kuma yana shiryarwa zuwa hanya madaidaiciya.” (Ma’ida:15-16).

Duk wadannan ayoyi suna wajaba ga Muminai ne, kan jagorancin Manzon tsira Annabi Muhammad (S.A.W.), da su bi littafin Allah wanda Ya Yi wahayinSa ga amintacenSa kuma MaaikinSa don ya zama shiriya da rahama ga talikai baki daya. Babu wata hanya ko madogara ga Musulmi wadda ta yi daidai ko kusa da saqon Allah da ke dauke a littafinSa mai girma. Shi Alqurani ya qunshi umarni ne da hani na Ubangijin halitta, da ba da labarin abin da ya gabace mu da wanda zai zo bayanmu, da abin da ya boyu daga garemu na labarin tashin Alqiyama da Wuta da Aljanna da dai sauransu. Sai an bi Alqurani ne ake samun tsira da sakamako yardajje.

A cikin Alqurani ne ake yi mana bayanin abin da za mu karba mu bi da wanda za mu juya wa baya. Daga cikin abin da Alqurani ya wajabta mana akwai bin Manzon Allah (S.A.W.), da karbar umarninsa da haninsa da komawa gare shi don warware matsalolinmu da rikice-rikicenmu da suka shafi rayuwar duniya da ta lahira. Allah (S.W.T.) ne da kanSa ya umarci ManzonSa da ya isar da wannan muhimmin saqo “Ka ce ya ku mutane! Lallai ne ni Manzon Allah ne zuwa gareku baki daya. (Shi Allah) wanda yake da mulkin sammai da qassai babu abin bautawa face Shi, wanda Yake rayawa da kashewa. Sai ku yi imani da Allah da kuma ManzonSa Annabi Ummiyyi, wanda ya yi imani da Allah da kalmominSa, ku bi Shi ko kun shiryuwa.” (A’raf:158).

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s